Mafi kyawun zikiri: SubhanAllah, Alhamdulillah, La ilaha illallah

Gajerun kalmomin zikiri masu lada mai yawa, don kowane lokaci na yini.

1 Sau ɗaya

لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ

Ma'ana da tushe

Daga Jabir -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Mafificin zikiri: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma mafificiyar addu'a: Godiya ta tabbata ga Allah".

Tirmizi da Nasa'i a cikin Al-kubra da Ibnu Majah ne Suka rawaito shi Daraja: Hasan ne

Sharhi

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa mafificin zikiri: "La ilaha illal lahu" Ma'anarta babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa mafificiyar addu'a godiya ta tabbata ga Allah; shi ne ikirari da cewa mai ni'imtarwa Shi ne Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, wanda ya cancanci cikakkiyar siffa mai kyau.

Fa'idodi

  • Kwadaitarwa ga yawaita ambaton Allah da kalmar Tauhidi, da addu'a da godiya.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

سُبْحَانَ اللَّهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَاللَّهُ أَكْبَرُ

Ma'ana da tushe

Daga Samura ɗan Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gagreshi - ya ce: "Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, da kowanne ka fara daga cikinsu ba ya cutar da kai".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi soyuwar zance a wurin Allah huɗu ne:

Tsarki ya tabbata ga Allah; Tana nufin tsarkake Allah - Maɗaukakin sarki - daga kowace tawaya.

Godiya ta tabbata ga Allah: Siffanta Allah ne da cikakkiyar cika tare da soyayyarSa da girmamashi.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah: Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.

Allah ne mafi girma: Wato; Mafi girma kuma Mafi buwaya daga dukkan komai.

Kuma cewa falalarta da samun ladanta ba ya nufin sai lallai an jeranta su a yayin furuci da su.

Fa'idodi

  • Sauƙin shari'a, ta inda ba ya cutarwa da kowaccen waɗannan kalmomin ka fara.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ، سُبْحَانَ اللَّهِ الْعَظِيمِ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba da labari game da kalmomi biyu da mutum zai furta su ba tare da wahala ba, kuma akowane hali, kuma ladansu mai girma ne a ma'auni, kuma Ubangijimmu Al-Rahman - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - Yana sonsu:

Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi; saboda abin da suka ƙunsa na siffanta Allah da girma da cika, da tsarkakeshi daga tawaya - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.

Fa'idodi

  • Mafi girman zikiri shi ne a haɗa tsakanin tsarkakeshi da yabo gareshi a cikinsa.
  • Bayanin yalwar rahamar Allah ga bayinsa, Yana sakayya da gwaggwaɓan lada a kan aiki kaɗan.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

سُبْحَانَ اللَّهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَاللَّهُ أَكْبَرُ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: In ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah, Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah ne mafi girma.

Fadin haka ya fi min duk abin da rana ta fito a kansa.

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labari cewa anbaton Allah (Zikiri) da waɗannan kalmomi masu girma, shi ya fi duniya da abin da yake cikinta, su ne:

"Tsarki ya tabbata ga Allah": Tsarke Allah ne daga dukkan tawaya.

"Godiya ta tabbata ga Allah": Yabon Allah ne da siffofinSa na Kamala tare da sonSa da kuma girmamaShi.

"Babu abin bautawa sai Allah": Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah.

Allah ne mafi girma; Mafi girma da ɗaukaka a kan komai.

Fa'idodi

  • Kwaɗaitarwa a kan anbaton Allah. Kuma Shi ne mafi soyuwa sama da duk wani abu da rana ta fito a kansa.
  • Zaburarwa a kan yawaita anbaton Allah, saboda ladan da yake da shi da kuma falala.
  • Jin daɗin duniya kaɗan ne, kuma sha’awar da ke cikinta mai gushewa ce

Karanta a HadeethEnc.com

5 sau 100

سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Hurairah Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi.

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Ma’aikin tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin cewa duk wanda a rana ya faɗa sau ɗari: Tsarki ya tabbata ga Allah haɗi da gode masa. an share kurakuransa an kuma gafarta su, ko da suna da yawa misalin farar kunfar nan ce da take saman teku lokacin kaɗawar igiya da ambaliya.

Fa'idodi

  • Wannan ladan yana samuwa ne ga wanda ya faɗeta a rana a jere ko a rarrabe.
  • Tasbihi: Tsarkake Allah daga tawaya. Godiya: Siffanta Allah da cika tare da so da kuma girmamawa.
  • Abin nufi da Hadisin kankare ƙananan zunubai, amma manyan dole sai da an tuba.

Karanta a HadeethEnc.com

6 Sau ɗaya

سُبْحَانَ اللَّهِ الْعَظِيمِ وَبِحَمْدِهِ

Ma'ana da tushe

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Tsarki ya tabbata ga Allah da yabonSa, za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna».

Tirmizi ne ya ruwaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Tsarki ya tabbata ga Allah) Ya tsarkakeShi (Mai girma) da zatinSa da siffofinSa da kuma ayyukanSa (da yabonSa) abin haɗawa da raɓa siffofin cika gareShi - tsarki ya tabbatar maSa -; za'a kafa kuma za'a dasa masa wani dabino a cikin ƙasar aljanna a duk lokacin da ya faɗeta.

Fa'idodi

  • Kwaɗaitarwa akan yawaita ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, daga hakan (akwai): Tasbihi tare da Tahmidi.
  • Aljanna mai yalwa ce, kuma dashenta shi ne Tasbihi da Tahmidi, wannan falala ce daga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma ni'imominSa.
  • An keɓanci bishiyar dabino a cikin hadisin banda waninta cikin bishoyoyi; saboda yawan anfaninta da kuma daɗin 'ya'yanta; sbaoda haka ne Allah Ya buga misalin mumini da kuma imaninsa da ita a cikin Alƙur'ani.

Karanta a HadeethEnc.com

7 Sau ɗaya

لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، اللهُ أَكْبَرُ كَبِيرًا، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ كَثِيرًا، سُبْحَانَ اللهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ

Ma'ana da tushe

Daga Sa'ad - Allah Ya yarda da su - ya ce: Wani balaraben kauye ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ka sanar maganar da zan fada, ya ce: "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya, Allah ne Mafi girma Mai girma, godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, babu dabara babu karfi sai ga Allah Mabuwayi Gwani" sai ya ce: Wadannan na Ubangijina ne, to ni me gareni? ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka gafarta mini Ka ji kaina Ka shiryar dani Ka azurtani".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Wani mutum daga mazauna kauye ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da shi wani zikirin da zai fade shi, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai yake ba da abokin tarayya" ya fara da shahada ta tauhidi, ma'anarta babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, "Allah ne Mafi girma Mai girma" Wato: Allah ne Mafi girma daga kowanne abu kuma Mafi girma, "Godiya ta tabbata ga Allah mai yawa" Wato: Godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, ga siffofinSa da ayyukanSa da ni'imominSa wadanda ba'a iya lissafe su, "Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai" Wato: Ya tsarkaka Ya tsarkaka daga tawaya, "Babu dabara babu karfi sai ga Allah Ubangiji Mabuwayi Gwani" Wato: Babu dabara ta canza wa daga wani hali zuwa wani halin sai ga Allah da taimakonSa da gamkatar dinSa, sai mutumin ya ce: Wadannan kalmomin sun tabbata ga Ubanigijina dan ambatonSa da girmamaShi, to ni meye gareni na addu'a ga kaina? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: "Ya Allah Ka gafarta mini" Da shafe munanan ayyuka da suturta su, "Ka jikaina" Ta hanyar sadar da abubuwan amfani da maslahohi na Addini da duniya gareni, "Ka shiryr da ni" ga mafi kyawun halaye kuma zuwa ga hanya mikakkiya, "Ka azirtani" Dukiya ta halal da lafiya da dukkanin alheri da lafiya.

Fa'idodi

  • Kwadaitarwa akan anbaton Allah da hailala da kabbara da tahmidi da tasbihi.
  • An so anbaton Allah da yabo gareShi kafin fara addu'a.
  • Anso addu'ar mutum da mafi tsarkakan addu'o'i, da kuma abinda aka ciro wanda a cikinsa akwai tattaro alherin duniya da lahira. Kuma yana da damar addu'a da abinda ya so.
  • Yana kamata ga bawa ya yi kwadayi akan neman ilimin abinda zai amfanar da shi a duniya da lahira.
  • Kwadaitarwa akan neman gafara da rahama da arziki, su ne matattarar alheri.
  • Tausayinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi akan ilmantar da al'ummarsa abinda zai amfanar da su.
  • An ambaci rahama bayan gafara dan tsarkakewa ta cika, gafara ita ce suturta zunubai da shafesu da nisanta daga wuta, rahama kuwa ita ce sadar da alherai da shiga aljanna, wannan shi ne rabo mai girma.

Karanta a HadeethEnc.com

8 Sau ɗaya

رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبَّاً، وَبِالْإِسْلَامِ دِيناً، وَبِمُحَمَّدٍ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَبِيّاً

Ma'ana da tushe

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muhammad a matsayin Manzo, Aljanna ta wajaba a gare shi».

Abu Dawud ne Ya Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji) kuma abin bautawa da gaskiya mai reno kuma mamallaki shugaba kuma mai gyarawa.

(Da Musulunci) da dukkanin hukunce-hukuncensa na umarni da hani (Addini) kuma tafarki da shari'a da miƙa wuya.

(Da Annabi Muhammad a matsayin manzo) da Annabi; da dukkanin abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi garemu, sai aljanna ta wajaba gare shi.

Fa'idodi

  • Kwaɗaitarwa a kan faɗar wannan addu'ar, da bayanin ladan da ya jerantu a kanta.
  • Yarda da Allah a matsayin Ubangiji ta ƙunshi kada mutum ya bautawa waninSa - tsarki ya tabbatar maSa -.
  • Yarda da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da Manzo ya ƙunshi yi masa biyayya - aminci ya tabbata agare shi - da jawuwa ga sunnarsa.
  • Yarda da Musulunci a matsayin Addini shi ne yarda da abinda Allah Ya zaɓe shi ga bayinSa.
  • An so faɗin wannan addu'ar a yayin shahada biyu daga jin kiran sallah kamar yanda yake a cikin wasu riwayoyin daban.
  • Kuma ya zo a cikin wani hadisin daban cewa an so wannan addu'ar a safiya da maraice.

Karanta a HadeethEnc.com

9 Sau ɗaya

يَا ذَا الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِ

Ma'ana da tushe

Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Ku kama kafa da fadin Ya Ma'abocin Girma da Daukaka"r"

Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

10 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Sa`id al-Khudri, yardar Allah ta tabbata a gare shi, wanda ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Ragowar na kirki ne, babu wani Allah sai Allah, tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Allah ya fi girma, kuma Allah ya fi girma”

Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi - Al-Hakim Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne a baki dayan Riwayoyin sa

Sharhi

A cikin wannan hadisin akwai shaidar cancantar wannan ambaton a cikin wannan sigar, domin kuwa ya qunshi ma’anonin yabo, tsarkakewa da tasbihi ga Allah mai girma da daukaka, kuma saboda yabon Allah ga ayyukansa. Samun alheri, sai dai tare da Allah Madaukaki. Waɗannan kalmomi tare da waɗannan ma'anoni masu girma sune abin da ya rage na mumini da fa'idar shi bayan mutuwarsa.

Karanta a HadeethEnc.com

11 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Cewa tsarki na zahiri yana kasancewa ne da alwala da wanka, kuma sharadi ne a sallah. Kuma cewa fadin: Alhamdulillah, (wato) "Godiya ta tabbata ga Allah yana cika ma'auni", shi ne godiya gare shi - tsarki ya tabbatar maSa - da kuma siffantaShi da siffofin cika, za'a auna su ranar alkiyama sai su cika ma'aunin ayyuka. Kuma fadin: Subhanallah, "Tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah", Shi ne tsarkake Shi daga kowacce tawaya da kuma siffantaShi da cikakken cika wanda yake dacewa da girmanSa, tare da sonSa da girmamaShi suna cika abinda ke tsakanin sammai da kasa. Kuma: "Sallah haske ce’’ ga bawa a cikin zuciyarsa, da fuskarsa, da cikin kabarinsa, da a tashinsa a taron Alkiyama. Kuma: "Sadaka garkuwace" kuma dalili ce akan gaskiyar imanin mumini, da kuma banbancinsa da munafikin da yake hanuwa daga yin ta (ita sadakar) dan kasancewarsa ba ya yin sadaka a lokacin ta. Kuma: "Hakuri haske ne" - Shi ne tsare rai daga firgici da fushi - wani haskene wanda yake da zafi da kuna, kamar hasken rana; domin shi mai wahalane, kuma yana bukatuwa ga dakewar zuciya da tsareta daga abinda take so; mai shi ba zai gushe ba yana mai haskaka , mai shiriya mai zarcewa akan daidai. Shi ne hakuri akan biyayya ga Allah, da kuma barin sabonSa, da kuma hakuri akan masifu da nau'o'in abubuwan ki a duniya. Kuma: 'Alkur’ani hujjane a gareka" ta hanyar Karanta shi da kuma aiki da shi, ko kuma "Hujjane akanka", ta hanyar barinsa ba tare da wani aiki ba, ko karantawa ba. Sannan - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkanin mutane suna tafiya suna fita suna tashi daga barcinsu suna fita daga gidajensu dan ayyukansu mabanbanta, Daga cikinsu akwai mai tabbata akan biyayya ga Allah, sai ya 'yanto kansa daga wuta, daga cikinsu akwai wanda yake kaucewa daga hakan kuma yake afkawa a cikin sabo sai ya halakar da ita ta hanyar shigarta wuta.

Fa'idodi

  • Tsaki iri biyu ne; Tsarki na zahiri, yana kasancewa ne da yin alwala da wanka, da kuma tsarkin badini yana kasancewa ne da kadaita Allah da imani da aiki na gari.
  • Muhimmanicin kiyaye sallah, ita ce haske ga bawa a duniya da kuma ranar alkiyama.
  • Sadaka dalili ce akan gaskiyar imani.
  • Muhimmancin aiki da Alkur’ani da gasgata shi, dan ya zama hujja a gareka ba akanka ba.
  • Rai idan ba ka shagaltar da ita da da'a ba, za ta shagaltar da kai da sabo.
  • Kowanne mutum ba makawa sai ya yi aiki; kodai ya 'yanto ransa da biyayya (ga Allah) ko ya halakar da ita da sabo.
  • Hakuri yana bukatar juriya da neman lada, kuma acikinsa akwai wahala.

Karanta a HadeethEnc.com

12 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi wa al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka basu labarin cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce mai daɗin ruwa ce, kuma ita faƙo ce kuma dashenta (shi ne): Subhanallah, (tsarki ya tabbata ga Allah), Alhamdulillah (godiya ta tabbata ga Allah), Lailaha Illallahu, (babu abin bautawa da gaskiya sai Allah), Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)".

Tirmizi ne ya ruwaito shi Daraja: Hasan ne a baki dayan Riwayoyin sa

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa ya haɗu da (Annabi) Ibrahim badaɗayi - aminci ya tabbata agare shi - a daren Isra'i da Mi'iraji, sai ya ce masa Ya Muhammad; Ka isarwa da al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka sanar dasu cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce, mai daɗin ruwa ce babu zartsi a acikinsa, kuma aljanna mai faɗi ce madaidaiciya ce babu itatuwa a cikinta, dashenta (shi ne) kalmomi masu tsarki, sune wanzajju na gari: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, duk lokacin da musulmi ya faɗesu kuma ya maimaita su za'a yi masa dashe a cikin aljanna.

Fa'idodi

  • Kwaɗaitarwa akan dawwama akan zikiri dan yawaita dashen aljanna.
  • Falalar al'ummar musulmi; inda (Annabi) Ibrahim - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya isar mata da sallama.
  • Kwaɗaitarwa (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - ga al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cikin yawaitawa daga ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -.
  • Malam al-Ɗaibi ya ce: Aljanna ...?, sannan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya samar mata da bishiyoyi da katangu da falalarsa gwargwdan ayyukan masu aiki; kowane mai aiki akwai abinda ya keɓanta da shi saboda aikinsa, sannan cewa Shi - Allah Maɗaukakin sarki - yayin da Ya sawwaƙa masa dan abinda Ya halicce shi saboda shi na aiki dan ya samu lada da hakan sai Ya sanya shi kamar mai dasa waɗancan bishiyoyin.

Karanta a HadeethEnc.com

13 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya so Ya azabtar da su idan kuma Ya so Ya gafarta musu".

Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi a cikin Alkubra Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga rafkana daga ambatan Allah, kuma cewa wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba kuma basu ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa ba, kuma ba su yi salati ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sai wannan mazaunin ya zama hasara a kansu da nadama da taɓewa da tawaya a ranar alƙiyama, idan Ya so Ya azabtar da su saboda zunubinsu da ya gabata da kuma kasawarsu mai zuwa, idan kuma Ya so Ya gafarta musu dan falala da rahama daga gare shi.

Fa'idodi

  • Kwaɗaitarwa akan zikiri da kuma falalarsa.
  • Falalar wuraran zama da a cikinsu akwai ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, da ambatan ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma cewa majalisan da a cikinsu babu hakan to sune majalisan zargi ga ma'abotansu a ranar alƙiyama.
  • Abinda aka ambata na gargaɗi daga rafkana daga ambatan Allah ba mai taƙaituwa ba ne akan wuraren zama kawai ba, kai yana game wasunsu, alNawawi ya ce: An karhanta ga wanda ya zauna a wani wuri ya bar wurin ba tare da ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa.
  • Hasara mai faruwa ce garesu a ranar Alkiyama: Ko dai da kufcewar lada da sakamako saboda rashin fa'idantuwa daga lokaci a cikin biyayya ga Allah, kodai da zunubi da uƙuba saboda shagaltuwar lokacin a saɓon Allah.
  • Wannan gargaɗin idan wannan rafkanar da abubuwan da aka halatta ne, to ta yaya da wuraren zaman da aka haramta waɗanda a cikinsu akwai giba da annamimanci da wasunsu?!

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Mafi kyawun zikiri: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Yaya na'urar ƙirga take aiki?

Taɓa na'urar ƙirga da ke ƙarƙashin zikiri, za ta ƙirga baya har zuwa sifili. Tana wannan shafi ne kawai kuma ba a adana komai.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.