Addu'ar neman gafara (istighfari)

Sayyidul Istighfar da sauran kalmomin neman gafara daga Sunna.

1 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ وَأَبُوءُ لَكَ بِذَنْبِي فَاغْفِرْ لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ

Ma'ana da tushe

Daga Shaddadu Dan Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Shugaban Istighfari shi ne ka ce: Ya Allah Kai ne Ubanjina babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai ka halicceni, kuma ni bawanKa ne, kuma ni ina kan alkawarinKa gwargwadon ikona, ina neman tsarinKa daga sharrin abinda na aikata, ina ikirari gareKa da ni'amarKa gareni, kuma ina ikirari da zunubina, to Ka gafarta mini domin cewa babu mai gafartawa sai Kai".

ya ce: "wanda ya fadeta da rana yana mai sakankancewa da ita, sai ya mutu a wannan rana kafin ya yi yammaci to yana cikin 'yan aljanna, wanda ya fadeta da daddare yana mai sakankancewa da ita sai ya mutu kafin ya wayi gari to yana cikin 'yan aljanna".

Bukhari ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa istigfri yana da lafuzza, kuma mafificinsu mafi girmansu bawa ya ce: "Ya Allah Kai ne Ubangiji na, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Ka halicceni, ni bawanKa ne, ni kuma ina kan al'kawarinKa gwargwadon iko, ina neman tsarinKa daga sharrin abinda na aikata, ina ikirari da ni'imarKa gareni, ina ikirari da zunubina, Ka gafarta mini, domin babu mai gafarta zunubai sai kai" Sai bawa ya tabbatarwa Allah da Tauhidi a farko, kuma cewa Allah ne Mahaliccinsa kuma abin bautarsa, cewa shi yana kan abinda ya yi wa Allah - tsarki ya tabbatar maSa - alkawari akansa na imani da Shi da biyayya gareShi, gwargwadan ikonsa; Domin bawa duk yadda ya tsaya akan ibada ba shi da ikon ya zo da dukkanin abinda Allah Ya umarce shi da shi da abinda yake wajaba na godiyar ni'ima, kuma cewa shi yana fakewa ne ga Allah, yana neman tsari daShi, cewa Shi abin neman tsari ne daShi daga sharrin da bawa ya aikata shi , Kuma cewa shi ya yi ikirari ya tabbatar gare shi ya yarda da ni'imarSa gare shi, kuma ya komawa kansa da ikirari da tabbatarwa da laifinsa da sabonsa. Bayan wannan kamun kafar zuwa ga Allah, ya roki Ubangijinsa Ya gafarta masa ta hanyar suturta zunubansa Ya kare shi laifukansu, da rangwamenSa da falalarSa da rahamarSa, cewa ba mai gafarta zunubai sai Shi - Mai girma da daukaka -. Sannan tsira da aminci ya bada labarin cewa su suna daga zikiran safiya da dare, wanda ya fadesu da sakankancewa da halarto ma'anoninsu da imani da su a farkon yininsa, tsakanin bullowar rana zuwa karkacewarta, shi ne lokacin rana, sai ya mutu, zai shiga aljanna, wanda ya karantata da daddare, shi ne daga faduwar rana zuwa bullowar alfijir, sai ya mutu kafin ya wayi gari, zai shiga aljanna.

Fa'idodi

  • Sigogin istigafri sun saba, sashinsu sun fi sashi.
  • Cewa yana kamata ga bawa ya yi kwadayi akan rokon Allah da wannan addu'ar; Domin ita ce shugaban istigafari.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

رَبِّ اغْفِرْ لِي خَطِيئَتِي وَجَهْلِي، وَإِسْرَافِي فِي أَمْرِي كُلِّهِ، وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ مِنِّي، اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي خَطَايَايَ، وَعَمْدِي وَجَهْلِي وَهَزْلِي، وَكُلُّ ذَلِكَ عِنْدِي، اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي مَا قَدَّمْتُ وَمَا أَخَّرْتُ، وَمَا أَسْرَرْتُ وَمَا أَعْلَنْتُ، أَنْتَ المُقَدِّمُ وَأَنْتَ المُؤَخِّرُ، وَأَنْتَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana addu'a da wannan addu'ar. "Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena da wautata, da wuce gona da irina a cikin dukkan al'amarina, da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni, ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina, da gangancina da jahilcina da kakacina, dukkan hakan daga garenin ne, ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar da abinda na jinkirtar, da abinda na ɓoye da abinda na bayyana, kaine Mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa, kuma kaine Mai iko akan dukkan komai".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Ya kasance daga addu'o'in Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai tattarowa faɗinsa:

"Ya Ubangiji Ka gafarta mini kurakuraina" da zunubina, "da jahilcina' da abinda ya afku daga gareni ba tare da sani ba.

"Da wuce gona da iri na a dukkan al'amarina" da kasawata da wuce gona da iri na.

"Da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni" Ka san shi Allah ni kuma na manta shi.

"Ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina da gangancina" da abinda ya bijiro na ganganci daga gareni da ilimi daga gareni da zunubai.

"Da (aiki) da gaske daga gareni da kakaci na" da abinda ya bijiro daga kakaci, da abinda ya afku daga gareni a hali biyun.

"Dukkanin wannan daga gareni ne" inda na tattara abinda aka ambata daga zunubai da aibuka.

"Ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar" da abinda ya shuɗe, "da abinda na jinkirtar" a abinda zai zo .

"Da abinda na ɓoye" na ɓoye, "da abinda na bayyana" na bayyanar.

"Kai ne mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa" Kana gabatar da wanda kake so daga halittarKa zuwa rahamarKa da dacewarKa da abinda Ka yarda da shi, kuma Kaine Mai jninkirtarwa Kana jinkirtar da wanda Kake so daga hakan da taɓarwarKa gare shi , bamai gabatar da abinda Ka jinkirtar, kuma ba mai jinkirtar da abinda Ka gabatar daga al'amura.

"Kai ne Mai iko akan dukkan komai" Mai cikakken iko Mai cikakken nufi, Mai aikata abinda Ka so.

Fa'idodi

  • Falalar wannan addu'ar da kwaɗayi akanta dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Hani daga wuce gona da iri kuma cewa mai wuce gona da iri abin bijirowa ne ga uƙuba.
  • Allah - Maɗaukakin sarki - Shi ne Mafi sanin mutum daga kansa, to ya wajaba akansa ya fawwala al'amarinsa zuwa ga Allah; domin cewa shi zai iya yin kuskure alhali shi bai sani ba.
  • Mutum za'a iya kama shi akan kakacinsa (barkwanci) kamar yadda ake kama shi akan gaskiyar maganarsa, to yana wajaba akan mutum ya kiyaye a cikin kakacinsa.
  • Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Banga bigiren addu'a da hakan a wani abu daga hanyoyinsa ba, haƙiƙa mafi yawan ƙarshensa ya afku... ya kasance yana faɗinsa a cikin sallar dare, kuma ya afku cewa shi ya kasance yana faɗinsa a ƙarshen sallarsa, riwaya ta saɓa shin ya kasance yana faɗin sa kafin sallama ne ko bayanta? ya zo a duka biyun .
  • Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin kuskurene dan ya nemi gafara? Wasu malaman suka ce; Shi ya faɗeta ne dan ƙanƙar da kai da kwantar da kansa (ga Allah), ko ƙirga cika da barin abinda ya fi na zunubai. Ko ya yi nufin abinda ya kasance daga rafkanuwa, ko abinda ya kasance kafin Annabci, an ce: Istigfari ibada ce da yinta yake wajaba, ba dan gafara ba, kai dan bauta ne (kawai), an ce: Hakan faɗakarwa ne da sanarwa ga al'ummarsa; dan kada su aminta su bar yin istigafri.

Karanta a HadeethEnc.com

3 sau 3

أَسْتَغْفِرُ الله الذي لا إله إلا هو الحَيَّ القيَّومَ وأتوب إليه

Ma'ana da tushe

Daga Zaid, malamin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya ce: Ina neman gafara daga Allah, wanda ba shi da wani abin bauta sai Shi wanda yake Madawwami, kuma na tuba zuwa gare Shi, za a gafarta masa zunubansa, koda kuwa ya tsere daga rarrafe."

Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Duk wanda ya ce: Ina neman gafara daga Allah, wanda ba shi da wani abin bauta face Shi rayayye ne, Madawwami, kuma na tuba zuwa gare Shi, za a gafarta masa zunubinsa, koda kuwa ya gudu daga yakar kafirai. ), Kuma ma'anar madaidaiciya ce: idan abin da ake nufi shi ne cewa ya tuba daga dukkan zunubai, gami da: guduwa daga rarrafe, in ba haka ba, kawai neman gafara yayin da mutum ya kasance a kan zunubin ba zai amfane shi ba, amma hakan yana da fa'ida tare da tuba daga zunubin.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -, a cikin abin da yake hakaitowa daga Ubanngijinsa - mai girma da ɗaukaka -, ya ce: "Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, sai (allah) Mai girma da ɗaukaka ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma yana yin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo ya sake yin zunubi, sai yace: Ya Ubangiji Ka gafarta min, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma Yanayin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo sai yayi zunubin, sai ya ce: Ya Ubangiji ka gafarta min laifina, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta zunubi, kuma yanayin uƙuba a kan zunubi, ka aikata abin da ka so haƙiƙa na gafarta maka".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbat a gareshi - yana ruwaitowa daga Ubangijinsa cewa idan bawa ya aikata zunubi sannan ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, Allah - Maɗaukakin sarki - Zai ce: Bawana ya aikata zunubi, kuma ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, Ya suturtashi ya yafe masa, ko yayi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafarta masa. Sannan bawan ya dawo sai ya yi zunubi, sai ya ce: Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubina, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Bawana ya aikata zunubi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubi, sai ya suturta shi ya yafe masa, ko Ya yi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafartawa bawana. Sannan bawan ya dawo sai ya yi zunubi, sai ya ce: Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubina, sai Allah Ya ce: Bawana ya aikata zunubi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubi, sai ya suturta shi ya yafe masa, ko Yayi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafartawa bawana, sai ya aikata abin da ya so muddin dai cewa shi a duk lokacin da ya yi zunubi zai bar zunubin ya yi nadama, ya yi niyyar barin komawa a cikinsa, sai dai zuciyarsa tana rinjayarsa, sai ya afka a cikin zunubi karo na gaba, muddin dai yana aikata haka yana zunubi yana tuba, to, zan gafarta masa; domin cewa tuba yana rushe abin da ke kafinsa.

Fa'idodi

  • Yalwar rahamar Allah ga bayinsa, kuma cewa mutum a duk lokacin da ya yi zunubi, kuma a duk lokacin da ya aikata idan ya tuba daga shi ya koma zuwa ga Allah Zai yi karɓi tubansa.
  • Mai imani ga Allah - Maɗaukakin sarki - yana burin afuwar Ubangijinsa, sai ya yi gaggawa zuwa tuba, ba zai zarce a kan saɓo ba.
  • Sharuɗɗan ingantacciyar tuba: Cirata daga zunubi, da nadama a kansa, da niyya a kan rashin komawa zuwa zunubin, idan tuban ya kasance daga zaluncin bawa ne a dukiya ko mutunci ko rai, sai ka kara sharaɗi na hudu, shine: Warwara daga mai haƙƙin, ko bashi haƙƙinsa.
  • Muhimmancin sanin Allah wanda ya ke sanya bawa ya zama masani da al'amuran addininsa, sai ya tuba a duk lokacin da ya yi kuskure, ba zai yanke ƙauna ba ba zai zarce ba.

Karanta a HadeethEnc.com

5 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - ya ce:Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abinda ya kasance gareka babu ruwaNa.

Ya kai ɗan Adam da zunubanka sun kai ƙololuwar sama, sannan ka nemi gafarata zan gafarta maka, babu ruwaNa.

Ya kai ɗan Adam lallai cewa kai da ka zo min da kurakurai cikin ƙasa sannan ka gamu dani ba yi min tarayya da wani abu ba, da na zo maka da gafara cikinta".

Tirmizi ne ya ruwaito shi Daraja: Hasan ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari cewa Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya faɗa a cikin hadisi Kudisi:

Ya kai ɗan Adam muddin dai kana roƙoNa kana kwaɗayin rahamata, ba ka yanke ƙauna ba; zan suturta zunubanka zan shafesu batare da kulawa ba a cikinsu; koda wannan zunubin da sabon sun kasance daga manyan zunubai ne. Ya kai ɗan Adam ! Da zunubanka sun yawaita yawan da zasu cika abinda ke tsakanin sama da ƙasa ta inda suka kai sasanninta kuma suka game gefanta, sannan ka nemi gafarata; zan shafe zan gafarta maka dukkaninsu ba tare da kulawa da yawansu ba.

Ya kai ɗan Adam: Lallai kai da zaka zo min bayan mutuwa da zunubai da sabo cikin ƙasa, kuma ka zama mai tauhidi baka taranya wani abu daNi ba; dana fuskanci waɗannan zunuban da sabon da gafara cikin ƙasa; domin cewa Ni Mai yalwar gafar ne, kuma ina gafarta dukkan zunubai in banda shirka.

Fa'idodi

  • Yalwar rahamar Allah - Maɗaukakin sarki - da gafararSa da falalarSa.
  • Falalar Tauhidi, kuma cewa Allah Yana gafarta zunubai da sabo ga masu Tauhidi.
  • Haɗarin shirka kuma cewa Allah ba Ya gafara ga masu shirka.
  • Ibnu Rajab ya ce: Haƙiƙa wannan Hadisin ya ƙunshi sabubba uku waɗanda gafarta zunubai suke samuwa da su: Na farko: Addu'a tare da ƙauna. Na biyu: Istgfari da neman tuba. Na uku: Mutuwa akan Tauhidi.
  • Wannan Hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai shi babu keɓance-keɓancen Alƙur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin alwala sabo da taba shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, (Mu’ujiza) da sauransu.
  • Zunubai nau'i uku ne: Na farko: Shirka da Allah; wannan Allah ba Ya gafarta shi, Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: {Lallai cewa shi wanda ya yi shirka da Allah to haƙiƙa Allah Ya haramta masa aljanna}. Na biyu: Zalintar bawa ga kansa a cikin abinda ke tsakaninsa da tsakanin Ubangijinsa na zunubai da sabo; domin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - zai gafarta hakan, kuma zai ƙetare in Ya so. Na uku: Zunuban da Allah baYa barin komai daga garesu; su ne zalintar bayi sashinsu da sashi, babu makawa daga sakayya.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'ar neman gafara: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Yaya na'urar ƙirga take aiki?

Taɓa na'urar ƙirga da ke ƙarƙashin zikiri, za ta ƙirga baya har zuwa sifili. Tana wannan shafi ne kawai kuma ba a adana komai.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.