Salati: yin salati ga Annabi ﷺ

Yadda ake yin salati ga Annabi ﷺ, da ladansa.

1 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ

Ma'ana da tushe

Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da siffar salati gare shi? bayan sun san siffar sallama gare shi a Tahiya: "Aminci ya tabbata agareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa..."? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da su siffar salati gare shi, ma'anarsa: "Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad" Wato: Ka yi yabo gare shi da ambato mai kyau a cikin jama'a madaukaka, da mabiyansa a cikin AddininSa, da muminai daga makusantansa. "kamar yadda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim" Kamar yadda ka yi baiwa ga iyalan (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - su ne (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Isma'il, da (Annabi) Ishak, da zuriyarsu da mabiyansu muminai, to ka riskar da falalararKa ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -. "Lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma" Wato: Abin yabo a zatinKa da siffofinKa da ayyukanKa, Mayalwaci a girmanKa da sarautarKa da baiwarKa. "Ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad kamar yanda ka yi albarka ga Ibrahim" Wato: Ka ba shi alheri da girmamawa mafi girmasa Ka kara masa Ka tabbatar masa.

Fa'idodi

  • Magabata sun kasance suna musayar kyautar mas'alolin ilimi.
  • Wajabcin salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Tahiyar karshe a sallah.
  • Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koyawa sahabbansa sallama da salati gare shi.
  • Wannan sigar ita ce mafi cikar sigogi a salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Husaini ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da su (Husain da Ali) - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mini salati ba".

Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar akan barin salati gare shi a halin jin sunansa ko alkunyarsa ko siffarsa, ya ce: Marowaci mai cikakkiyar rowa (shi ne) wanda aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba; hakan saboda wasu al'amura:

Na farko: Cewa hakan rowa ce, da wani abun da ba ya asara saboda shi kaɗan ne ko mai yawa, kuma ba ya bada wata dukiya, kuma ba ya yin wani ƙoƙari.

Na biyu: Cewa shi ya yi wa kansa rowa kuma ya haramta mata ladan salati ga Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi haƙiƙa ya yi rowa saboda hanuwarsa daga salati gare shi, kuma ya hanu daga bada haƙƙin da bada shi ya wajaba akansa dan ruko da umarni kuma ake samun lada da shi.

Na uku: Cewa salati gare shi a cikinsa akwai bada haƙƙin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, shi ne wanda ya sanar damu, kuma shi ne wanda ya shiryar damu, shi ne wanda ya kiramu zuwa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - kuma ya zo mana da wannan wahayin, da kuma wannan shari'ar, shi ne sababin shiriyarmu - bayan Allah - alhrerinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - wanda bai yi masa salati ba zai zama haƙiƙa ya yi wa kansa rowa, kuma ya yi rowa ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani haƙƙin da yana daga mafi ƙasan haƙƙoƙinsa.

Fa'idodi

  • Barin salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - take ne na rowa.
  • Salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana daga mafificin ayyukan kusanci da kuma ɗa'a a dukkanin lokuta, kuma yana ƙarfafuwa a halin ambatansa.
  • Al-Nawawi ya ce: Idan zai yi salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - to ya haɗa tsakanin salati da sallama, kada ya taƙaita akan ɗayansu; kada ya ce: (Allah Ya yi salati gare shi) kadai, ko: (Amnici ya tabbata agare shi) kadai.
  • Abul Aliya ya faɗa a cikin faɗinSa: {Lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga wannan Annabi} ya ce: Salatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga AnnabinSa: YabonSa gare shi, salati daga mala'iku da mutane: Addu'a.
  • AlHulaimi ya ce: Ma'anar: "Ya Allah Ka yi salati ga (Annabi) Muhammad": Ya Allah ka girmama shi a duniya da ɗaukaka ambatansa, da bayyanar da Addininsa, da wanzar da shari'arsa, a lahira kuma: Da neman cetansa a sha'anin al'ummarsa, da gwaggwaɓa ladansa da sakamakonsa, da bayyanar da falalarsa ga na farko da na karshe da matsayi abin yabo, da gabatar da shi akan dukkan makusanta masu halartowa.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba, an turbuɗe hancin mutumin da Ramadan ya shiga sannan ya fita ba’a gafarta masa ba, kuma an turbuɗe hancin mutumin da mahaifansa suka tsufa a wurinsa amma basu shigar da shi aljanna ba".

Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Mummunar addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan nau'i uku da turbuɗe hancinansu da turɓaya daga ƙasƙanci da wulaƙanci da kuma taɓewa. Nau'i na farko: Wanda aka ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wurinsa bai yi masa salati ba da faɗinsa: tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ko makamancinsa. Na biyu: Wanda ya riski watan Ramadan sannan watan ya ƙare ba’a gafarta masa ba saboda gazawarsa a aikata aikin ɗa'a. Na uku: Mutumin da tsufa ya riski iyayensa a wurinsa amma ba su zama sababi a cikin shigarsa aljanna ba dan saɓawarsa da kuma gazawarsa a kan haƙƙinsu.

Fa'idodi

  • Sindi ya ce: A taƙaice cewa kowane mutum daga waɗannan haƙiƙa ya samu abinda da badan kasawa daga gare shi ba da ya sami wani rabo mai yawa na alheri, yayin da ya kasa har hakan ya wuce shi to haƙiƙa ya taɓe kuma yayi hasara.
  • Kwaɗaitarwa akan salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a duk lokacin da aka ambaci sunansa.
  • Kwaɗaitarwa akan ƙoƙari da zage damtse ga ibada a cikin watan Ramadan.
  • Kwaɗaitarwa akan ƙoƙari a cikin biyayya ga mahaifa da kuma girmamasu, musamman ma a lokacin tsufa.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Salati ga Annabi ﷺ: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.