أَلَمۡ نَشۡرَحۡ لَكَ صَدۡرَكَ ١
Alam nashrah laka sadrak
Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
أَلَمۡ نَشۡرَحۡ لَكَ صَدۡرَكَ ١
Alam nashrah laka sadrak
Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
وَوَضَعۡنَا عَنكَ وِزۡرَكَ ٢
Wawada'nā 'anka wizrak
Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
ٱلَّذِيٓ أَنقَضَ ظَهۡرَكَ ٣
Alladhī anqada zahrak
Wanda ya nauyayi bãyanka?
وَرَفَعۡنَا لَكَ ذِكۡرَكَ ٤
Warafa'nā laka dhikrak
Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
فَإِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرًا ٥
Fa inna ma'al-'usri yusrā
To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
إِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرٗا ٦
Inna ma'al-'usri yusrā
Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
فَإِذَا فَرَغۡتَ فَٱنصَبۡ ٧
Fa idhā faraghta fansab
Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَٱرۡغَب ٨
Wa ilā rabbika farghab
Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.
Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.
Surat Ash-Sharh tana da ayoyi 8. Ita ce sura ta 94 a cikin Alƙur'ani.
Surat Ash-Sharh sura Makkiya ce.
Surat Ash-Sharh tana cikin juz'i 30.
Eh. Danna Kunna a saman wannan shafi, ko ka fara daga kowace aya. Manhajar Qabas kuma tana ba ka damar sauke ta don sauraro ba tare da intanet ba.