Surat Ad-Duha الضحى

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلضُّحَىٰ ١

Wad-duhā

Inã rantsuwa da hantsi.

وَٱلَّيۡلِ إِذَا سَجَىٰ ٢

Wallayli idhā sajā

Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).

مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ ٣

Mā wadda'aka rabbuka wamā qalā

Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.

وَلَلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لَّكَ مِنَ ٱلۡأُولَىٰ ٤

Walal'ākhiratu khayrul laka minal-ūlā

Kuma lalle ta ƙarshe1 ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.

وَلَسَوۡفَ يُعۡطِيكَ رَبُّكَ فَتَرۡضَىٰٓ ٥

Walasawfa yu'tīka rabbuka fatardā

Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.

أَلَمۡ يَجِدۡكَ يَتِيمٗا فَـَٔاوَىٰ ٦

Alam yajidka yatīman fa'āwā

Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?

وَوَجَدَكَ ضَآلّٗا فَهَدَىٰ ٧

Wawajadaka dāllan fahadā

Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?

وَوَجَدَكَ عَآئِلٗا فَأَغۡنَىٰ ٨

Wawajadaka 'ā'ilan fa aghnā

Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?

فَأَمَّا ٱلۡيَتِيمَ فَلَا تَقۡهَرۡ ٩

Fa ammal-yatīma falā taqhar

Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.

وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنۡهَرۡ ١٠

Wa ammas-sā'ila falā tanhar

Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.

وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ ١١

Wa ammā bini'mati rabbika fahaddith

Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).

Lambobin bayanan ƙasa suna kai wa shafin aya, inda ake nuna bayanan mai fassara.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Tambayoyi

Ayoyi nawa ne a Surat Ad-Duha?

Surat Ad-Duha tana da ayoyi 11. Ita ce sura ta 93 a cikin Alƙur'ani.

Shin Surat Ad-Duha Makkiya ce ko Madaniya?

Surat Ad-Duha sura Makkiya ce.

A wane juz'i Surat Ad-Duha take?

Surat Ad-Duha tana cikin juz'i 30.

Zan iya sauraron Surat Ad-Duha?

Eh. Danna Kunna a saman wannan shafi, ko ka fara daga kowace aya. Manhajar Qabas kuma tana ba ka damar sauke ta don sauraro ba tare da intanet ba.