Yaushe ake amsa addu'a? Lokuta da dalilai

Lokuta da halayen da aka fi fatan a amsa addu'a a cikinsu.

1 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa ga Ubangijinsa shi ne idan yana mai sujjada, sai ku yawaita addu'a".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi kusancin lokacin da bawa yake kusanci ga Ubangijinsa shi ne alhalin yana mai sujjada; hakan ya kasance ne saboda mai sallah yana sanya mafi ɗaukakar abin da ke jikinsa a kan ƙasa cikin ƙanƙan da kai da ƙasƙantarwa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - alhali shi yana mai sujjada.

Haƙiƙa (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi umarni da yawaita addu'a a sujjada, sai ƙanƙar da kai ga Allah ya haɗu da faɗa da aikatawa.

Fa'idodi

  • Biyayya tana ƙarawa bawa kusanci ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.
  • An so yawaita addu'a a sujjada; domin cewa ita tana daga wuraren amsawa.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Umamah ya ce: Amr ɗan Abasa - Allah Ya yarda da shi - ya zantar da ni cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa kusa da Ubangiji a cikin (kason) dare na karshe, idan kana da ikon ka kasance daga wanda yake ambatan Allah a wannan lokacin to ka kasance".

Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Ubangiji - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne mafi kusa ga bawa a lokacin sulusin dare na karshe; idan an datar da kai kuma ka samu iko - ya kai mumini - da ka kasance daga jumlar masu bauta masu sallah masu ambatan Allah masu tuba a wannan lokacin to shi wani al'amari ne wanda yana kamata a ci ribarsa da kokari a cikinsa.

Fa'idodi

  • Kwaɗaitar da musulmi akan zikiri a karshen dare.
  • Fifikon lokuta a tsakaninsu ga zikiri da addu'a da sallah.
  • Mirik ya ce: A cikin banbanci tsakaknin faɗinsa: "Mafi kusancin lokacin da Ubangiji ya fi kusa da bawa", da tsakanin faɗinsa: " Mafi kusancin lokacin da bawa yake kusa da Ubangijinsa alhali shi yana mai sujjada': Abin nufi a nan bayanin lokacin kasancewar Ubangiji Shi ne mafi kusa ga bawa shi ne tsakiyar dare, abin nufi a can bayanin kusancin halayen bawa ga Ubangiji alhali shi yana halin sujjada.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama".

Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana falalar addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama, kuma cewa ba'a dawo da ita kuma ta cancanci amsawa, to ku roƙi Allah a cikinsa.

Fa'idodi

  • Falalar wannan lokacin dan yin addu'a.
  • Idan mai yin addu'a ya siffantu da ladubban addu'a, kuma ya nufi gurarenta da lokutanta masu falala, kuma ya nisanta daga saɓon Allah, Ya tsare kansa daga afkawa a cikin shubuhohi da kokwanto, kuma ya kyautatawa Allah zato: To shi ya cancanci a amsa masa da izinin Allah.
  • Al-Manawi ya ce game da amsa addu'a: Wato: Bayan tara sharuɗɗan addu'a da rukunanta da ladubbanta, idan wani abu ya saɓa daga garesu to kada ya zargi kowa sai kansa.
  • Amsa addu'a: Kodai a gaggauto masa da abinda ya roka, ko a kawar masa da sharri kwatankwacin sa, ko a ajiye masa ita a lahira; hakan gwargwadan hikimar Allah da rahamarSa.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Sahl bin Saad - yardar Allah ta tabbata a gare su - a cikin marfoo ': "Ba a juya mata biyu baya, ko kuma ba safai ake dawo da su ba: Addu'a a lokacin kira da karfin hali, idan aka hade ta."

Abu Daud Ya Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

A cikin wannan hadisin bayani ne a kan falalar jihadi saboda Allah ta yadda Allah - Madaukaki - ke amsa kiran mujahid yayin da yake cikin yaki, haka nan kuma ya bayyana falalar kiran salla yayin da Allah - Madaukaki - ke amsa addu'ar Musulmi a kiran salla da har sai an tsayar da salla.

Karanta a HadeethEnc.com

5 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Ummu al-Darda'i da Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbara agare shi - ya kasance yana cewa: «‌Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce, a daidai kansa akwai wani Mala'ika wanda aka wakilta a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce: Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin haka».

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa musulmi a bayan idon wanda aka yi wa addu'ar abar karɓa ce; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a cikin ikhlasi, kuma lallai cewa a wajen kan mai addu'ar akwai wani Mala'ikan da aka wakilta, a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce; Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin abinda ka roƙa.

Fa'idodi

  • Kwaɗaitarwa akan kyautatawa muminai sashinsu ga sashi ko da da addu'a ne.
  • Addu'a a ɓoye tana nuni a bayyane akan gaskiyar imani da kuma 'yan uwantaka.
  • Ƙayyade addu'a da cewa a ɓoye; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a ikhlasi (wato yi domin Allah) da kuma halartowar zuciya.
  • Daga cikin sabubban amsa addu'a akwai musulmi ya yi wa ɗan'uwansa musulmi addu'a a ɓoye.
  • Nawawi ya ce; Falalar addu'a ga ɗan'uwansa musulmi a ɓoye, da a ce zai yi wa jama'ar musulmai addu'a to wannan falalar zata tabbata, da kuma a ce zai yi addu'a ga jumlar musulmai to zance mabayyani shi ne samuwar (falalar), wani daga cikin magabata na gari ya kasance idan yana so ya yi wa kansa addu'a sai ya yi wa ɗan'uwansa addu'a da wannan addu'ar; domin cewa ita za'a amsata, kuma zai samu kwatankwacinta.
  • Bayanin wasu daga cikin ayyukan Mala'iku, kuma cewa daga cikinsu akwai wanda Allah Ya wakilta shi ga wannan aikin.

Karanta a HadeethEnc.com

6 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Addu'a ita ce ibada', sannan ya karanta; " {Ubangijinku Ya ce ku roƙeni zan amsa muku, lallai waɗanda suke girman kai game da bautata za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu} [Gafir: 60].

Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa addu'a ita ce ibada, to, wajibi ne ta zama dukkaninta abar tsarkakewa ga Allah, duka ɗaya ne, ta kasance addu'ar tambaya ce da nema, da ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - abin da zai amfaneshi, da tunkuɗe abin da zai cutar da shi a duniya da lahira, ko addu'ar ibada, ita kuma itace dukkanin abin da Allah Yake sonsa kuma Ya yarda da shi na maganganu da ayyuka na zahiri da baɗini, ibadu na zuciya ko na jiki ko na dukiya.

Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kafa dalili akan haka ta inda ya ce: Allah Ya ce: {Ku roƙeni zan amsa muku, lalle waɗanda suke girman kai game da bauta min, da sannu za su shiga jahannama suna ƙasƙantattu}.

Fa'idodi

  • Addu'a ita ce asalin ibada, ba ya halatta a juyar da ita ga wanin Allah.
  • Addu'a ta ƙunshi haƙiƙanin bauta da iƙirari bisa wadatar Ubangiji da ikonsa - Maɗaukakin sarki -, da buƙatuwar bawa gareshi.
  • Narko mai tsanani sakamakon girman kai game da bautar Allah da barin roƙonsa, kuma waɗanda suke girman kai game da roƙon Allah za su shiga jahannama suna ƙasƙantattu.

Karanta a HadeethEnc.com

7 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a".

Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi Daraja: Hasan ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa babu wani abu a ibadu mafifici a wurin Allah sama da addu'a; domin a cikinta akwai iƙirari da wadatar Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -, da kuma iƙirari da gajiyawar bawa da buƙatuwarsa gareshi.

Fa'idodi

  • Falalar addu'a kuma wanda ya roƙi Allah, to, shi mai girmamashi ne, kuma mai tabbatarwa ne da cewa Shi (Allah) Mawadaci ne - tsarki ya tabbatar masa - ba a roƙon mabuƙaci, kuma cewa Shi Mai yawan ji ne kurma ba a roƙonsa, kuma cewa shi mai kyauta ne, marowaci ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Mai jin ƙai ne mai bushewar zuciya ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Mai iko ne gajiyayye ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Makusanci ne manisanci ba ya ji, da wanin haka na siffofin ɗaukaka da kyau na Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.

Karanta a HadeethEnc.com

8 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karɓa sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Maɗaukakin sarki Ya ce:

{Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}.

Kuma Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama (yana cewa): Ya Ubangiji! ya Ubangiji! abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to ta yaya za'a amsa masa ga hakan?».

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah tsarkakakke ne, tsarkakakke abin tsarkakewa daga nakasa kowacce iri da aibuka, kuma Mai siffantuwa ne da cika, ba Ya karɓar ayyuka da maganganu da ƙudirce-ƙudirce sai abinda ya kasance mai tsarki, shi ne tsantsa saboda Allah, wanda ya dace da shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, baya kamata a nemi kusanci zuwa ga Allah sai da hakan, daga mafi girman abinda tsarkin ayyuka yake faruwa ga mumini tsarkin abin cinsa, kuma ya zama na halal ne, da hakan ne aikinsa zai tsarkaka, saboda haka ne Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci manzanni da shi, na cin halal da aiki na gari, sai Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa} kuma Ya ce: {Ya ku wadanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirtaku}.

Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga cin haram wanda yake ɓata aiki kuma yake hana karɓarsa duk irin kokarin da ya yi na sabubban karɓar na zahiri; daga cikinsu:

Na farko: Tsawaita tafiya ta fuskokin ayyukan ɗa'a kamar hajji da jihadi da sada zumunci da wanin hakan.

Na biyu: Cukurkuɗar gashi dan rashin taje shi, wanda launinsa ya canja da launin tufansa daga turɓaya, shi mabuƙaci ne.

Na uku: Yana ɗaga hannayensa sama da addu'a.

Na huɗu: Yana tawassuli zuwa ga Allah da sunayenSa kuma yana nacewa a cikin hakan (yana cewa): Ya Ubangiji ya Ubangiji!

A tare da waɗannan sabubban na amsar addu'a ba'a saurare shi ba; hakan saboda abin cinsa da abin shansa da abin ɗaurawarsa haramun ne, kuma an shayar da shi da haram, to ya nisanta a amsa wa wanda wannan ita ce siffarsa, to ta yaya za'a amsa masa?!

Fa'idodi

  • Cikar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a cikin zatinSa, da siffofinSa, da ayyukanSa, da hukunce-hukuncenSa.
  • Umarni da tsarkake aiki saboda Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Anfani da abinda yake ƙarfafa gwiwa akan aiki, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi", idan mumini ya san cewa wannan yana daga abubuwan da aka umarci Manzanni to cewa shi zai ƙarfafu zai ji ƙwarin gwiwa akan riko da shi.
  • Daga abubuwan da suke hana amsar addu'a (akwai) cin haram.
  • Daga cikin sabubban amsar addu'a (akwai) abubuwa biyar: Na farkonsu: Tsawaita tafiya dan abinda ke cikinta na karyewar zuciya wanda shi yana daga mafi girman sabubban amsa addu'a. Na biyu: Halin buƙatuwa. Na uku: Ɗaga hannaye zuwa sama. Na huɗu: Nacewa Allah da maimaita ambatan RububiyyarSa, kuma shi yana daga mafi girman abinda ake neman amsa addu'a da shi. Na biyar: Daddadan abin ci da abin sha.
  • Cin halal mai tsarki yana daga sabubba masu taimakawa ga aiki na gari.
  • Alƙali ya ce: Mai tsarki kishiyar mummuna ne, idan aka siffanta Allah Maɗaukakin sarki da shi to ana nufin cewa shi abin tsarkakewa ne daga dukkanin tawaya, abin tsarkakewa ne daga aibuka. Idan kuma aka siffanta bawa da shi kai tsaye ana nufi da shi cewa shi mai tsiraita ne daga munanan ɗabi'u da munanan ayyuka, kuma mai siffantuwa da kishiyoyin hakan ne, idan aka siffanta dukiya da shi ana nufin kasancewarta halal ce kuma taka daga cikin zaɓaɓɓun dukiyoyi.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Lokacin amsa addu'a: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.