Addu'o'i masu tattare alherin duniya da lahira

Gajerun addu'o'i masu roƙon dukkan alheri, a duniya da lahira.

1 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً، وَفِي الآخِرَةِ حَسَنَةً، وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ

Ma'ana da tushe

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita addu'a da addu'a gamammiya, daga cikinsu: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma Ka tsaremu azabar wuta", Ita ta tattaro kyau a duniya na arziki mai dadi, mayalwaci na halal, da mace ta gari, da da wanda ido zai yi farin ciki da shi, da hutu, da ilimi mai amfani, da makamancin hakan na abububuwan da ake so na halal, kyakkyawa a lahira na kubuta daga ukubobin kabari da tsayuwa da wuta, da samuwar yardar Allah, da rabauta da ni'ima madawwamiya, da kusanci ga Ubangiji Mai jin kai a lahira.

Fa'idodi

  • An so addu'a da addu'o'i masu tattarowa, dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Mafi cika mutum ya hada tsakanin alherin duniya da lahira a addu'arsa.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ الْخَيْرِ كُلِّهِ، عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ، مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ أَعْلَمْ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ الشَّرِّ كُلِّهِ، عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ، مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ أَعْلَمْ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ مَا سَأَلَكَ عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا عَاذَ بِهِ عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْجَنَّةَ، وَمَا قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ النَّارِ، وَمَا قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ، وَأَسْأَلُكَ أَنْ تَجْعَلَ كُلَّ قَضَاءٍ قَضَيْتَهُ لِي خَيْرًا

Ma'ana da tushe

Daga (Nana) A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koya mata wannan addu'ar: "Ya Allah ina roƙon Ka dukkan alheri, magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba, kuma ina neman tsarinKa daga dukkan sharri magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba. Ya Allah ina roƙonKa mafi alherin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya roƙeKa, kuma ina neman tsarinKa daga sharrin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya nemi tsarin Ka da shi, ya Allah ina roƙonKa aljanna da abin da yake kusantota na magana ko aiki, kuma ina neman tsarinKa daga wuta, da abin da yake kusantota na magana ko aiki, ina rokonKa Ka sanya dukkan hukuncin da Ka hukunta gare ni ya zama alheri".

Ibnu Majah da Ahmad ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koyawa Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - dunkulallun addu'o'i su ne addu'o'i huɗu:

Na farko: Addu'a mai game kowane alheri: (Ya Allah ina roƙonKa dukkan alheri) dukkansa, (magaggaucinsa) makusanci a lokacinsa, (da majinkircinsa) na nesa, (abinda na sani daga gare shi) daga abinda Ka sanar da ni, (da abinda ban sani ba), daga abinda yake kasancewa a cikin saninKa - tsarki ya tabbatar maKa -. A cikinsa akwai fawwala al'amari zuwa ga Allah Masani Mai bada labari Mai sawwaƙawa; sai tsarki ya tabbatar maSa Ya zaɓawa musulmi maffificinsa kuma mafi kyansa, (Ina neman tsarinKa) ina neman tsarinKa ina kiyayewa (da Kai daga sharri dukkansa magaggaucinsa da majinkircinsa, abinda na sani da abinda ban sani ba).

Addu'a ta biyu: Ita ce kiyayewar musulmi daga ya yi shisshigi a cikin addu'a (Ya Allah lallai ni ina roƙonKa) ina nemanKa (daga mafificin abinda bawanKa kuma AnnabinKa ya roƙeKa) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, (ina neman tsarin Ka) ina fakewa ina nenam tsari (da Kai daga sharrin abinda bawanKa kuma AnnabinKa ya nemi tsarin Ka) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi , wannan addu'a ce da nema daga Allah Ya bawa mai addu'ar daga abinda Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya roƙe shi kuma ya neme shi ga kansa, ba tare da ƙididdiga nau'ikan abinda tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi ya roka ba.

Addu'a ta uku: Neman shiga aljanna da nisantar wuta, shi abin neman kowane musulmi ne kuma matuƙar aikinsa:

(Ya Allah ina roƙon Ka aljanna) da rabauta da ita (da abinda ya kusantota na magana ko aiki) na gari wanda zai yardar da kai, (ina neman tsarinKa daga wuta) inda babu tsari daga munanan ayyuka sai da luɗufinKa, (da abinda ya kusanto zuwa gareta na magana ko aiki) daga saɓon da zai sa fushinKa.

Addu'a ta huɗu: Addu'a da yarda da hukuncin Allah (ina roƙonKa Ka sanya kowane hukuncin da Ka hukunta mini ya zama alheri) dukkan al'amarin da Allah Ya hukunta shi gareni Ya sanya shi mafi alheri gare ni, wannan yana daga addu'a da yarda da hukuncin Allah.

Fa'idodi

  • Koyarwar mutum ga iyalansa abinda zai anfanar da su daga al'amuran Addini da duniya, kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga (Nana) A'isha.
  • Abinda ya fi ga musulmi ya haddace addu'o'in da suka zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa su suna daga addu'o'i dunkulallu.
  • Malamai sun faɗa game da wannan hadisin: Shi ne mafi tattarowar hadisai a roƙon alheri da neman tsari daga sharri, shi yana daga kalmomi masu tattarowa (kalmomi kaɗan masu ɗaukar ma'anoni masu yawa) waɗanda aka bawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - su.
  • Daga sabubban shiga aljanna bayan rahamar Allah: Ayyuka da kalamai na gari.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَافِيَةَ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ فِي دِينِي وَدُنْيَايَ وَأَهْلِي وَمَالِي، اللَّهُمَّ اسْتُرْ عَوْرَتِي -أَو: عَوْرَاتِي- وَآمِنْ رَوْعَاتِي، اللَّهُمَّ احْفَظْنِي مِنْ بَيْنِ يَدَيَّ، وَمِنْ خَلْفِي، وَعَنْ يَمِينِي، وَعَنْ شِمَالِي، وَمِنْ فَوْقِي، وَأَعُوذُ بِعَظَمَتِكَ أَنْ أُغْتَالَ مِنْ تَحْتِي

Ma'ana da tushe

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana barin waɗannan addu'o'i ba lokacin da ya yi yammaci ko ya wayi gari: "Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira, ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwami da lafiya a Addini na da duniya ta da iyalaina da dukiyata, ya Allah Ka suturta al'aurata - ko: al'aurorina Ka amintar da tsorona, ya Allah Ka kiyayeni ta gabana, da bayana, da damana, da haguna, da samana, ina nemn tsarinKa kada a yaudareni da kisa ta ƙarƙashina".

Abu Daud da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne suka Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance ba yana barin waɗannan addu'o'in ba lokacin da Ya yi yammaci da lokacin da ya wayi gari:

(Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya), da kuɓuta daga masassara da masifu da tsanance-tsanance na duniya, da sha'awowi da fitintinu cikin Addini (a duniya da lahira) magaggauciya da majinkirciya.

(Ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwame) da shafe zunubai da ƙetare su.

(da lafiya) da kuɓuta daga aibuka, (a Addini na) daga shirka da bidi'o'i da saɓo, (da duniya ta) daga masifu da cuta da sharruka, (da iyalaina) matana da 'ya'ya na da 'yan uwana, (da dukiya ta) dukiyoyi na da aiki na.

(Ya Allah Ka suturta al'aurori na) da abinda ke cikina na aibuka da ɓaci da taƙaitawa Ka shafe zunubai na, (Ka amintar da tsorace -tsorace na) razani na da tsoro na.

(Ya Allah Ka kiyaye ni) Ka tunkuɗe bala'i daga gare ni daga abubuwa masu cutarwa da masifu, (ta gaba na da baya na, da dama na, da hagu na, da sama na) inda ya roƙi Allah Ya kiyaye shi ta kowane bangare: domin cewa masifu da aibuka kaɗai suna samun mutum ne kuma suna fuskantar sa daga ɗaya daga waɗannan ɓangarorin.

(Ina neman tsarinKa kada a kashe shi ni) shi ne a kamani bagtatan, in mutu ba tare da na sani ba (ta ƙarƙa shi na) sh ne in halaka ta kisfewa.

Fa'idodi

  • Kiyayewa akan waɗannan kalmomin dan koyi da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Mutum kamar yadda shi abin umarta ne da roƙon Allah lafiya a cikin Addini kamar haka shi abin umarta ne da roƙonta a duniya.
  • Al-Ɗaibi ya ce: Ya game ɓangarori shida ne; domin cewa aibuka daga garesu ne, kuma yakai matuƙa a ɓangaren ƙasa dan munin aibukan daga gareta ne.
  • Abin da yafi a karanta zikirai, a safiya: Daga ɓollowar alfijir zuwa ɓullowar rana a farkon yini, haka kuma daga bayan la'asar zuwa kafin faɗuwar rana, idan ya faɗesu bayan hakan yana nufin: Ya faɗesu a safiya bayan ɗagawar walaha ya isar masa, idan ya faɗesu bayan azahar ya isar masa, idan ya faɗesu bayan Magariba ya isar masa, to wannan lokaci ne na zikiri.
  • Dalili bai yi nuni ba akan kasancewar zikiri yana da lokaci ayyananne ba a cikin dare kamar karanta ƙarshen ayoyi biyu daga Suratul Baƙarah cewa ita tana kasancewa ne da daddare bayan faɗuwar rana.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abbas ɗan AbdulMuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, ka sanar dani wani abu in roƙi Allah, Allah - Mai girma da ɗaukaka -shi. Ya ce: "Ka roƙi Allah lafiya", sai na zauna wasu kwanuka sannan na zo sai na ce: Ya Manzon Allah, ka sanar dani wani abu in roƙi Allah shi. Sai ya ce dani: "Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya a duniya da lahira".

Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi Daraja: Ingantacce ne ta wani bangaren

Sharhi

Baffan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya nema daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da shi addu'ar da zai roƙi Allah ita, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sanar da shi cewa ya roƙi Allah lafiya da kuɓuta daga illoli da aibuka a addini da duniya da lahira, Abbas ya ce: Bayan wasu kwanuka sai na dawo zuwa gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - karo na gaba ina tambayarsa ya sanar dani addu'ar da zan nemeta daga Allah, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa yana mai nuna masa kauna: Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roki Allah lafiya dan tunkude kowace cuta da jawo kowane alheri da anfani a duniya da lahira.

Fa'idodi

  • Maimaitawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ita kanta addu'ar ga Abbas lokacin da ya tambaye shi karo na biyu yana nuni akan cewa lafiya ita ce mafi alherin abinda bawa zai roƙi UbangijinSa.
  • Bayanin falalar lafiya, kuma a cikinta akwai tattarowar alherin duniya da lahira.
  • Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan neman ƙari na ilimi da alheri.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'o'i masu tattare alheri: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.