Musulunci a rayuwar yau da kullum

Darasi 3 cikin 4

Yaya Musulmi zai yi magana kuma ya kyautata wa maƙwabta?

Daga Alƙur'ani

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَسۡخَرۡ قَوۡمٞ مِّن قَوۡمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُواْ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا نِسَآءٞ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيۡرٗا مِّنۡهُنَّۖ وَلَا تَلۡمِزُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَلَا تَنَابَزُواْ بِٱلۡأَلۡقَٰبِۖ بِئۡسَ ٱلِٱسۡمُ ٱلۡفُسُوقُ بَعۡدَ ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن لَّمۡ يَتُبۡ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ ﴿١١﴾ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱجۡتَنِبُواْ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلظَّنِّ إِنَّ بَعۡضَ ٱلظَّنِّ إِثۡمٞۖ وَلَا تَجَسَّسُواْ وَلَا يَغۡتَب بَّعۡضُكُم بَعۡضًاۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمۡ أَن يَأۡكُلَ لَحۡمَ أَخِيهِ مَيۡتٗا فَكَرِهۡتُمُوهُۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ تَوَّابٞ رَّحِيمٞ ﴿١٢﴾

"Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai." Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai.

Al-Hujurat 49:11-12Karanta a cikin Alƙur'ani

Daga Sunna

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce : "Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya faɗi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama maƙocinsa, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama baƙonsa".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Ingantacce ne HadeethEnc.com
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa bawan da ya yi imani da Allah da ranar lahira wadda makomarsa take a cikinta, kuma a cikinta sakayyar aikinsa take, to, imaninsa zai kwaɗaitar da shi a kan aikata waɗannan ɗabi'un.

Na farko: Magana mai kyau: Ta tasbihi da hailala, da horo da aikin alheri, da hani daga abin ƙi, da gyara a tsakaknin mutane, idan bai aikata ba, to, ya lazimci shiru, ya kame daga cutarwa, ya kiyaye harshensa.

Na biyu: Girmama maƙoci: Da kyautata masa da rashin cutar da shi.

Na uku: Girmama baƙo mai gabatowa don ziyararka: Ta hanyar daddaɗan zance da ciyar da abinci da makamancin hakan.

Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi ".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Ingantacce ne HadeethEnc.com
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi mai cikakken Musulunci shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa ba ya zaginsu kuma ba ya la'antarsu, ba ya gulmarsu, kuma ba ya tafiya tsakaninsu da kowanne nau'i na nau'ukan cutarwa da harshensa, kuma suka kubuta daga hannunsa ba ya yi musu ta'addanci, ba ya ƙwatar dukiyoyinsu ba tare da wani haƙƙi ba, da makamantan hakan, mai hijira shi ne wanda ya bar abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Ingantacce ne HadeethEnc.com
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa Jibrilu bai gushe ba yana maimaita masa kuma yana umartarsa da kulawa da maƙoci, wanda shi ne makusancin gida, musulmi ne ko kafiri, ɗan uwa ne ko ba ɗan uwa ba ne, da kiyaye haƙƙinsa da rashin cutar da shi, da kyautatawa gareshi da haƙuri a kan cutarsa, har (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi zaton cewa daga girmama haƙƙin makoci da maimaitawar Jibrilu hakan cewa wahayi zai sauka da a ba shi (wani abu )daga dukiyar maƙocinsa wacce zai barta bayan mutuwarsa.

Duk darussa