Darasi 2 cikin 4
Me Musulunci ke cewa game da iyaye?
Daga Alƙur'ani
۞ وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّآ إِيَّاهُ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنًاۚ إِمَّا يَبۡلُغَنَّ عِندَكَ ٱلۡكِبَرَ أَحَدُهُمَآ أَوۡ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَآ أُفّٖ وَلَا تَنۡهَرۡهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوۡلٗا كَرِيمٗا ﴿٢٣﴾ وَٱخۡفِضۡ لَهُمَا جَنَاحَ ٱلذُّلِّ مِنَ ٱلرَّحۡمَةِ وَقُل رَّبِّ ٱرۡحَمۡهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرٗا ﴿٢٤﴾
Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci. Kuma ka sassauta musu fikãfikan tausasãwa na rahama. Kuma ka ce: "Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami."
وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ وَهۡنًا عَلَىٰ وَهۡنٖ وَفِصَٰلُهُۥ فِي عَامَيۡنِ أَنِ ٱشۡكُرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيۡكَ إِلَيَّ ٱلۡمَصِيرُ ﴿١٤﴾
Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu (Muka ce masa) "Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take."
Daga Sunna
Daga Bahzu ɗan Hakim daga babansa daga kakansa ya ce: Na ce ya Manzon Allah: Waye wanda zan fi yi wa biyayya? Ya ce: «Mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan babanka, sannan mafi kusa sai mafi kusa».
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mafi cancantar mutane da yi wa biyayya, da kyautata masa, da kyakkyawar mu'amala, da tsaftatacciyar mu'amala, da abokantakarsa da sadar da zumuncinsa: Ita ce uwa, kuma ya ƙarfafa haƙƙin uwa akan waninta da maimaitawarsa sau uku; dan bayanin falalarta akan ragowar mutane ba tare da togancewa ba. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce yana mai bayyana wanda yake biye mata a biyayya: Sannan uba, sannan mafi kusanci sai mafi kusanci daga 'yan dangi, kuma a duk lokacin da ya zama ya fi kusanci to ya zama mafi cancanta da sadar da zumunci daga mafi nesa.