Addu'a bayan kiran sallah (adhan)

Abin da ake faɗa yayin kiran sallah da addu'ar bayan an gama.

1 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwadaitarwa akan amsa wa ladani a lokacin jinsa, hakan da mu fadi irin abinda yake fada, jumla da jumla, A yayin da ya yi kabbara sai mu yi kabbara a bayansa, a yayin da ya zo da shaida biyu, sai mu zo da su a bayansa. An togance lafazin: (Ku yi gaggawa zuwa sallah, ku yi gaggawa zuwa tsira) cewa za'a fada a bayansu: Babu dabara babu karfi sai ga Allah.

Fa'idodi

  • Zai bi ladani na biyu bayan karewar na farko, koda ladanan suna da yawa; dan gamewar hadisin.
  • Ya amsawa ladani a kowanne hali, indai ba ya kasance ne a bayan gida ko yana kan biyan bukatarsa ba.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Ina shaida wa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce; Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan ya ce; Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa sallah, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa tsira, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sai ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah daga zuciyarsa zai shiga aljanna".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Kiran sallah shi ne sanar da mutane shigowar lokacin sallah, kuma kalmomin kiran sallah kalmomi ne masu tattaro aƙidar imani.

A wannan Hadisin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana abin da aka shara'anta a yayin jin kiran sallah, shi ne mai ji ya faɗi irin abin da ladanin yake faɗa, idan ladani ya ce: "Allah ne mafi girma", mai ji ya ce: "Allah ne mafi girma", haka nan; sai dai a lokacin fadin ladani: "Ku yi gaggawa zuwa sallah", "Ku yi gaggawa zuwa tsira" sai mai ji ya ce: "Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah".

Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana cewa wanda ya maimaita tare da ladani yana mai tsarkake (niyya) daga zuciyarsa zai shiga aljanna.

Ma'anonin kalmar kiran sallah: "Allah ne mafi girma": Wato cewa Shi (Allah) - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne mafi girma mafi ɗaukaka mafi girma daga dukkan komai.

"Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.

"Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne": Wato ina tabbatarwa kuma ina shaidawa da harshena da zuciyata cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, Allah - Mai girma da ɗaukaka -Ya aiko shi , kuma yana wajaba a yi masa biyayya .

"Ku yi gaggawa zuwa sallah", wato ku zo zuwa sallah, da faɗin mai ji: "Babu dabara kuma babu karfi sai ga Allah", wato babu dabara a kuɓuta daga abubuwan da suke hana biyayya, babu ƙarfi a kan aikatasu, kuma babu iko a kan kowanne abu daga abubuwa sai dace daga Allah - Maɗaukakin sarki -.

"Ku yi gaggawa zuwa tsira", wato ku zo zuwa sababin tsira, shi ne rabauta da aljanna da tsira daga wuta.

Fa'idodi

  • Falalar amsawa ladani da irin abin da yake faɗa sai dai a Hai'ala biyu kawai, sai ya ce: "Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah".

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، رَضِيتُ بِاللهِ رَبًّا وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولًا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا

Ma'ana da tushe

Daga sa'ad Dan Abu Wakkas - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "Wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, baShi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, na yadda da Allah Shi ne Ubangiji kuma (Annabi) Muhammad Manzo ne, kuma Musulunci shi ne Addini.

Za’a gafarta masa zunubinsa".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah "Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya" wato: Ina tabbatarwa ina bada labarin cewa babu wani abin bautawa da agskiya sai Allah, kuma dukkan wani abin bauta wanda ba shi ba to shi karya ne, "Kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne" wato: shi bawa ne ba'a bauta masa, kuma Manzone ba ya karya, "Na yarda da Allah Shi ne Ubangiji" wato: Da RububiyyarSa da UluuhiyyarSa da sunayenSa da siffofinsa, "Da (Annabi) Muhammad shi ne Manzo" wato: Da dukkanin abinda aka aiko shi da shi, kuma ya isar da shi garemu, "Da Musulunci" wato: Da dukkanin hukunce-hukuncen Musulunci na umarni da hani, "Addini" wato: A kudircewa da aikatawa, "Za'a gafarta masa zunubinsa" wato: kananunsu.

Fa'idodi

  • Maimaita wannan addu'ar a lokacin jin kiran sallah yana daga masu kankare zunubai.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ رَبَّ هَذِهِ الدَّعْوَةِ التَّامَّةِ، وَالصَّلاَةِ القَائِمَةِ، آتِ مُحَمَّدًا الوَسِيلَةَ وَالفَضِيلَةَ، وَابْعَثْهُ مَقَامًا مَحْمُودًا الَّذِي وَعَدْتَهُ

Ma'ana da tushe

Daga Jbir ɗan Abbdullahi - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Duk wanda ya ce a yayin da ya ji kiran sallah: (Ya Allah, Ma’abocin wannan cikakken kira da sallah da za'a tayar, Ka bai wa [Annabi] Muhammad al-Wasila da al-Fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alƙawarin sa), ceto na zai halatta a gare shi ranar alƙiyama".

Bukhari ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah bayan ya gama:

(Ya Allah Ma’abocin wannan kiran) sune lafuzan kiran sallah waɗanda ake kira zuwa bautar Allah da kuma sallah da su, (cikakkiya) cikakkiya, kira zuwa ga Tauhidi da saƙo, (da sallar da za'a tayar) dawwamammiya wacce za'a tayar, (Ka bawa) Ka bawa, ((Annabi) Muhammad al-Wasila) matsayi maɗaukaki a cikin aljanna wanda ba ya kamata sai gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, (da Fadila) daraja ce mai ƙaruwa akan darajoji kan halittu, (Ka tashe shi) Ka ba shi (matsayi abin yabo) wanda ake yabon mai tsayawa a cikinsa; shi ne babban ceto a ranar alƙiyama, (wanda Ka yi masa alƙawari) da faɗinKa: {Ana kaunar Ubangijinka ya tasheka a wani matsayi abin yabo} da ya kasance gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Wanda ya yi wannan addu'ar ya cancanci kuma ceton Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajaba a gare shi ranar alƙiyama.

Fa'idodi

  • Halaccin wannan addu'ar bayan gama maimaita (kiran sallah) a bayan ladan, wanda bai ji kiran sallah ba; to shi ba zai faɗeta ba.
  • Matsayin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda aka ba shi Wasila da Fadila da matsayi abin yabo da babban veto a kan rabewa tsakanin halittu.
  • Tabbatar da ceto ga Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; saboda faɗinsa: "Cetona ya halatta gare shi ranar alƙiyama".
  • Cetonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kasancewa ne ga ma'abota manyan zunubai daga al'ummarsa a cikin rashin shiga wuta ko kuma a fitar da wanda ya shigeta, ko kuma a shiga aljanna ba tare da hisabi ba, ko ɗaukaka darajojin wanda ya shigeta.
  • AlƊaibi ya ce: Daga farkonsa zuwa faɗinsa: "(Annabi) Muhammad Manzon Allah ne" ita ce cikakkiyar kira, Hai'ala kuma ita ce sallar da za'a tayar a cikin faɗinsa suna tsaida sallah, za'a iya ɗaukar cewa ya zama abin nufi da sallar addu'a da kuma za'a tayar madawwamiya daga ya tsaya akan abu idan ya dawwama a kansa, akan haka ne to faɗinsa: "Da sallah dawwamammiya" bayani ne ga kira cikakke, kuma zai iya ɗaukar cewa ya zama abin nufi da sallar wacce a za’a yi ake kira zuwa gareta a wannan lokacin ita ce mafi bayyana.
  • AlMuhallab ya ce: A cikin hadisin akwai kwaɗaitarwa akan yin addu'a a lokutan salloli; domin loakaci ne na fatar amsar Addu’a .

Karanta a HadeethEnc.com

5 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba ya kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, ina ƙaunar in zama ni ne shi, duk wanda ya roƙi Allah Wasila gareni, to, cetona zai tabbata gare shi".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nuna wa wanda ya ji mai kiran sallah da ya maimaita a bayansa, sai ya faɗi irin abinda ya fada, ban da Hai'ala biyu, cewa ya ce a bayansu: Babu dabara ba ƙarfi sai ga Allah.

Sannan ya yi salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan gama kiran sallah, domin cewa wanda ya yi salati ɗaya a gare shi to Allah zai yi masa salati goma da shi, ma'anar salatin Allah ga bawanSa: shi ne YabonSa ga bawa a wurin Mala'iku.

Sannan ya yi umarni da a roƙa masa Allah Wasila - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ita ɗin wani matsayi ne a aljanna, shi ne mafi ƙololuwa, ba ta dace ba, kuma wannan matsayin ba zai samu ba sai ga wani bawa ɗaya daga dukkanin bayin Allah - Maɗaukakin sarki -, ina ƙaunar in zama ni ne shi, kaɗai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya faɗa ne, don Tawalu’u; domin cewa idan shi wannan matsayin da yake babba ba zai kasance ba sai ga mutum ɗaya, to, ai wannan mutum ɗayan ba zai zama ba sai shi (Annabin) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; domin shi ne mafificin halitta.

Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa wanda ya roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila; to, cetonsa zai same shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Fa'idodi

  • Kwaɗaitarwa a kan amsawa mai kiran sallah.
  • Falalar salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan amsawa mai kiran sallah
  • Kwaɗaitarwa a kan roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila bayan salati a gareshi .
  • Bayanin ma'anar Wasila, da ɗaukakar darajarta ta inda ba ta tabbata sai ga wani bawa ɗaya.
  • Bayanin falalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da aka keɓanceshi da wancan babban matsayin.
  • Wanda ya roƙi Allah Wasila ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - to, cetonsa zai ya halatta gare Shi.
  • Bayanin ƙanƙar da kansa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da ya nemi addu'a daga al'ummarsa na wannan matsayin, tare da cewa zai kasance gare shi.
  • Yalwar falalar Allah da rahamarSa, aikin lada ɗaya (za a yi sakamako) da goma tamkarta.

Karanta a HadeethEnc.com

6 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama".

Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana falalar addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama, kuma cewa ba'a dawo da ita kuma ta cancanci amsawa, to ku roƙi Allah a cikinsa.

Fa'idodi

  • Falalar wannan lokacin dan yin addu'a.
  • Idan mai yin addu'a ya siffantu da ladubban addu'a, kuma ya nufi gurarenta da lokutanta masu falala, kuma ya nisanta daga saɓon Allah, Ya tsare kansa daga afkawa a cikin shubuhohi da kokwanto, kuma ya kyautatawa Allah zato: To shi ya cancanci a amsa masa da izinin Allah.
  • Al-Manawi ya ce game da amsa addu'a: Wato: Bayan tara sharuɗɗan addu'a da rukunanta da ladubbanta, idan wani abu ya saɓa daga garesu to kada ya zargi kowa sai kansa.
  • Amsa addu'a: Kodai a gaggauto masa da abinda ya roka, ko a kawar masa da sharri kwatankwacin sa, ko a ajiye masa ita a lahira; hakan gwargwadan hikimar Allah da rahamarSa.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'a bayan kiran sallah: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.