Addu'o'i cikin sallah: buɗe sallah, ruku'u, sujada da tahiya

Addu'o'in da Annabi ﷺ yake yi cikin sallah, daga kabbarar harama zuwa sallama.

1 Sau ɗaya

اللهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ، اللهُمَّ نَقِّنِي مِنْ خَطَايَايَ كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، اللهُمَّ اغْسِلْنِي مِنْ خَطَايَايَ بِالثَّلْجِ وَالْمَاءِ وَالْبَرَدِ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai ya yi shiru ɗan wani lokaci gabanin fara karatu, sai na ce: Ya manzon Allah, fansarka baba na da Baba ta, kana ganin shirun da kake yi tsakanin kabbara da karatu, me kake cewa? ya ce: Ina cewa: Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwan ƙanƙara kuma mai tsananin sanyi".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi kabbarar sallah yana yin shiru kaɗan kafin ya karanta fatiha, yana buɗe sallarsa da wasu daga addu'o'i a cikinta, daga abinda ya zo daga waɗannan addu'o'in faɗinsa: "Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga kurakuraina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti, ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwa da ƙanƙara da ruwa mai tsananin sanyi". Shi yana roƙon Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya nisantar da tsakaninsa da kurakurai da kada ya faɗa cikinsu, nisantarwa ta inda gamuwa ba zata ƙara faruwa tare da shi ba, kamar yadda babu haɗuwa tsakanin mahudar rana da mafaɗarta har abada, idan kuma ya faɗa cikinsu to Ya tsaftace su Ya kawar da su kamar yadda ake kawar da datti daga farin tufa, kuma Ya wanke shi daga kurakuransa Ya sanyaya horuwarsu da zafinsu, da waɗannan masu tsaftacewar masu sanyi: Ruwa, da kankara, da sanyi.

Fa'idodi

  • Boye addu'ar buɗe sallah koda sallar ta kasance ta karatun bayyana ne.
  • Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan sanin halayen Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a motsinsa da shirunsa.
  • Wasu sigogin daban sun zo na addu'ar buɗe sallah, abinda ya fi shi ne mutum ya bibiyi addu'o'in buɗe sallah da suka zo, kuma tabbatattu daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya zo da wannan wani lokaci, wani lokacin kuma ya zo da wannan.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، اللَّهُمَّ رَبَّنَا لَكَ الْحَمْدُ، مِلْءَ السَّمَاوَاتِ وَمِلْءَ الْأَرْضِ وَمِلْءَ مَا شِئْتَ مِنْ شَيْءٍ بَعْدُ

Ma'ana da tushe

Daga Ibnu Abi Aufa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Allah Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa, cikar sammai da cikar ƙasa da cikar abin da ka so daga wani abu bayan nan"

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u a sallah yana cewa: Allah Ya ji wanda ya gode maSa", wato: Cewa wanda ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - Allah - Maɗaukakin - sarki Ya amsa masa, Ya karɓi godiyarsa kuma Ya saka masa, sannan ya godewa Allah da faɗinsa; "Ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata a greKa, cikon sammai da cikon ƙasa da cikon abin da Ka so daga wani abu bayan nan", godiyar da za ta cika sammai da ƙassai da abin da ke tsakaninsu, kuma ya cika abin da Allah Ya so daga wani abu.

Fa'idodi

  • Bayanin abin da ake so masallaci ya faɗe shi idan ya ɗago kansa daga ruku'u.
  • Halaccin daidaituwa da nutsuwa bayan ɗagowa daga ruku'u; domin cewa ba zai yiwu ba ya faɗi wannan zikirin sai dai idan ya daidaita kuma ya nutsu.
  • Wannan zikirin abin shara'antawa ne a dukkanin salloli, duk ɗaya ne ta kasance farilla ce ko nafila.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

اللَّهمَّ اغْفِرْ لي، وارْحَمْنِي، وعافِني، واهْدِني، وارزقْنِي

Ma'ana da tushe

Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.

Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi Daraja: Hasan ne a baki dayan Riwayoyin sa

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana yin Addu’a tsakanin sujjada biyu a Sallarsa, da waɗannan addu’o’in biyar, wacce Musulmi yake da matuƙar buƙatar su, kuma sun ƙunshi alheran duniya da lahira, kamar neman gafara, da ɓoye zunubi, da kuma yafe su, da malalo rahama da waraka daga shubuhohi da abubuwan sha’awe-sha’awe da rashin lafiya da cututtuka , da kuma roƙon Allah samun shiriya a kan gaskiya da kuma tabbata a kanta, da arziki na imani da ilimi da aiki na ƙwarai da kuma dukiya ta halal mai daɗi.

Fa'idodi

  • Shar’antuwar wannan Addu’ar a zaman dake tsakanin sujjada biyu.
  • Falalar wannan Addu’ar saboda abin da ta ƙunsa na alheran duniya da lahira.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

اللهُمَّ اغْفِرْ لِي ذَنْبِي كُلَّهُ دِقَّهُ، وَجِلَّهُ، وَأَوَّلَهُ وَآخِرَهُ وَعَلَانِيَتَهُ وَسِرَّهُ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana addu'a a cikin sujjadarsa sai ya ce: (Ya Allah Ka gafarta mini zunubina) da suturta shi, kuma Ka kareni nauyinsu; sai Ka yi rangwami Ka ƙetare ka kauda kai, (dukkansa), ka taimake ni: (ƙanƙaninsa) ƙaraminsa da ƙanƙaninsa, (da babbansa) babbansa da mai yawansa, (da na farkonsa) farkon zunubi, (da na ƙarshensa), da abinda ke tsakaninsu, (na zahirinsa da na baɗininsa) daga abinda babu wani wanda ya sanshi sai Kai - tsarki ya tabbatar maKa -.

Fa'idodi

  • Ibnul-Kayyim ya ce: Neman gafarar zunubai ƙanana da manya, ƙanƙani da mai girma, na farko da na ƙarshe, na ɓoye da na bayyane, wannan gamewar kuma wannan ƙunshin dan tuba ya zo akan abinda bawa ya san shi daga zunubansa, da abinda ma bai sanshi ba.
  • An ce: Kawai ya gabatar da (ƙanƙani) akan (mai girma) ne; domin cewa mai tambaya yana kara matsawa ne a cikin tambayarsa wato yana hauhawa, domin cewa manyan zunubai suna faruwa a galibi ne daga nacewa akan ƙananu da kuma rashin kulawa da su, kamar cewa su hanyoyi ne zuwa manyan zunubai, kuma daga haƙƙin hanya shine a gabatar da ita a tabbatarwa da kuma ɗaukakawa.
  • Kanƙan da kai zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da nemanSa gafara daga dukkan zunubai, ƙanana da manya.
  • Nawawi ya ce: A cikinsa akwai ƙarfafa addu'a da yawaita lafazzukanta duk da sashinsu ya wadatar da sashi.

Karanta a HadeethEnc.com

5 Sau ɗaya

اللهُمَّ أَعُوذُ بِرِضَاكَ مِنْ سَخَطِكَ، وَبِمُعَافَاتِكَ مِنْ عُقُوبَتِكَ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْكَ لَا أُحْصِي ثَنَاءً عَلَيْكَ أَنْتَ كَمَا أَثْنَيْتَ عَلَى نَفْسِكَ

Ma'ana da tushe

Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na rasa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare a shinfiɗa sai na lalube shi sai hannuna ya faɗa akan cikin diga-digansa alhali shi yana cikin masallaci alhali su suna a kafe, alhali shi yana cewa: "Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na kasance ina barci a gefen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na rasashi da daddare, sai na laluba da hannayena gurin da ya kasance yake sallah a cikinsa a cikin ɗaki; sai gashi yana sujjada alhali diga-digansa suna a tsaye, sai gashi shi yana cewa:

(Ina neman tsari) ina kamun ƙafa (da yardarKa daga fushinKa) akaina ko akan al'ummata, (kuma) ina neman tsari (da rangwaminKa) afuwarKa mai yawa (daga uƙubarKa), (Ina neman tsari daga gareKa) da siffofin kyawunKa daga siffofin ɗaukakarKa, inda ba mai fakewa daga gare Ka sai Kai, babu matserata kuma babu mafaka daga Allah sai dai zuwa gareShi, (Ba zan iya ƙididdige yabo a gareKa ba) ba zan iya kuma bazan kai ƙololuwa a lissafewa ba da kuma ƙirgawa ba saboda gajiyawata ba, ƙididdige ni'imarKa da kyautatawarKa kamar yadda Kake cancantarsa ba koda na yi ƙoƙari a hakan. (Kai kamar yadda Ka yabi kanKa) Kaine wanda Ka yi yabo akan zatinKa yabon da ya dace da Kai, waye yake da iko akan bada haƙƙin yabonKa?!

Fa'idodi

  • An so waɗannan addu'o'in a cikin sujjada.
  • Mirak ya ce: A cikin ɗaya daga riwayoyi al-Nasa'i: Ya kasance yana faɗin wannan addu'ar idan ya gama sallarsa ya koma makwancinsa.
  • An so yabo ga Allah da siffofinSa da kuma roƙonSa da sunayenSa tabbatattu a cikin Littafi da Sunnah.
  • A cikinsa akwai girmama Mahalicci a cikin ruku'u da sujjada.
  • Halaccin neman tsari da siffofin Allah, kamar yadda neman tsari da zatinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - yake halatta.
  • AlKhaɗɗabi ya ce: A cikin wannan maganar akwai ma’ana mai kyau, ita ce: Cewa shi haƙiƙa ya nemi tsarin Allah Ya tsare shi da yardarSa daga fushinSa, da kuma rangwaminSa daga uƙubarSa, yarda da fushi kishiyoyi ne masu fuskantar juna, haka nan rangwami da kamu da uƙuba, lokacin da ya zama zuwa anbatan abinda bask shi da kishiya Shi ne Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ya nemi tsari da Shi daga gareShi bada waninSa ba, ma'anar haka: Istigfari domin kasawa wurin cika wajibi daga haƙƙin bayinSa, da yabo a gareShi. da faɗinSa: ba zan iya ƙididdige yabo a gareka ba: Wato ba zan iya shi ba, kuma ba zan iya kai matuka a cikinsa ba.

Karanta a HadeethEnc.com

6 Sau ɗaya

التحيَّات المباركات، الصَّلَوَاتُ الطَّيِّبَاتُ لله، السلام عليك أيها النبي ورحمة الله وَبَرَكَاتُهُ، السلام علينا وعلى عباد الله الصالحين، أشهد أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وأشهد أنَّ محمَّدا رسول الله

Ma'ana da tushe

Daga Ibn Abbas -Allah ya yarda da su- cewa shi ya ce: cewa shi ya ce: Manzo tsira da amincin Alla su tabbata a gare shi ya koyar da ni tahiya.hannu na na cikin hannayensa, kamar yadda yake koyar da ni Surar daga Alqur'ani, sai ya ce: "Gaisuwoyi Masu Albarka, Salatai maisu tsarki ga Allah, Amincin a gareka Manzon Allah da rahamatullah da Albarkatansa, Amincin Allah a garemu da sauran bayin Allah Salihai, na Shaida babu wani abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma na Shaida cewa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne" a wata riwayar ta Ibn Rumh kamar yadda yake koyar da mu Al-qura'ani

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Wannan Hadisin yana bayanin Sigar Tahiya, kuma cewa Annabi SAW ya Kasance yana kwaxayin koyar da su kamar yadda yake koya Musu Al-qurani, kuma sigar ita ce: "Gaisuwoyi Masu Albarka, Salatai maisu tsarki ga Allah, Amincin a gareka Manzon Allah da rahamatullah da Albarkatansa, Amincin Allah a garemu da sauran bayin Allah Salihai, na Shaida babu wani abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma na Shaida cewa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne" kuma tayi kama da sigar Tahiyar nan Mashahuriya da ta zo daga Ibn Mas'ud -Allah ya yarda da shi- kuma cewa Banbancin Qarin Albarkatun, kuma shafe waw din a cikin kalmomi biyu bayanta, kuma ya halarta banbantawa tsakanin Sigogin da suka zo a Tahiya

Karanta a HadeethEnc.com

7 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ

Ma'ana da tushe

Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da siffar salati gare shi? bayan sun san siffar sallama gare shi a Tahiya: "Aminci ya tabbata agareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa..."? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da su siffar salati gare shi, ma'anarsa: "Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad" Wato: Ka yi yabo gare shi da ambato mai kyau a cikin jama'a madaukaka, da mabiyansa a cikin AddininSa, da muminai daga makusantansa. "kamar yadda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim" Kamar yadda ka yi baiwa ga iyalan (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - su ne (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Isma'il, da (Annabi) Ishak, da zuriyarsu da mabiyansu muminai, to ka riskar da falalararKa ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -. "Lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma" Wato: Abin yabo a zatinKa da siffofinKa da ayyukanKa, Mayalwaci a girmanKa da sarautarKa da baiwarKa. "Ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad kamar yanda ka yi albarka ga Ibrahim" Wato: Ka ba shi alheri da girmamawa mafi girmasa Ka kara masa Ka tabbatar masa.

Fa'idodi

  • Magabata sun kasance suna musayar kyautar mas'alolin ilimi.
  • Wajabcin salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Tahiyar karshe a sallah.
  • Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koyawa sahabbansa sallama da salati gare shi.
  • Wannan sigar ita ce mafi cikar sigogi a salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Karanta a HadeethEnc.com

8 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ القَبْرِ، وَمِنْ عَذَابِ النَّارِ، وَمِنْ فِتْنَةِ المَحْيَا وَالمَمَاتِ، وَمِنْ فِتْنَةِ المَسِيحِ الدَّجَّالِ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yin addu'a yana cewa: "Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)". A cikin wani lafazin na Muslim:

"Idan dayanku ya gama tahiyar karshe, to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da sharrin Mai yawan yawo makaryaci (Jujal).

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana neman tsarin Allah daga abubuwa hudu bayan tahiyar karshe kuma kafin sallama a sallah, ya kuma umarcemu mu nemi tsarin Allah daga garesu,

Na farko: Daga azabar kabari.

Na biyu: Daga azabar wuta hakan a ranar Alkiyama .

Na uku: Daga fitinar rayuwa na sha'awowin duniya haramtattu da kuma shubuhohi masu batarwa, da kuma fitinar mutuwa, wato lokacin fitar rai, na karkacewa daga musulunci ko sunna, ko fitinar kabari kamar tambayar Mala'iku biyu.

Na hudu: Fitinar mai yawan yawo makaryaci (Dajjal) wanda zai fito a karshen zamani, Allah zai jarrabi bayinSa da shi, ya kebance shi da ambato dan girman fitinarsa da batarwarsa.

Fa'idodi

  • Wanan neman tsarin yana daga muhimman addu'o'i kuma gamammu, dan abinda suka kunsa na neman tsari daga sharrukan duniya da lahira.
  • Tabbatar da azabar kabari kuma cewa ita gaskiya ce.
  • Hadarin fitintinu da muhimmancin neman taimakon Allah da addu'a dan tsira daga garesu.
  • Tabbatar da fitowar Dujal da girman fitinarsa.
  • An so yin wannan addu'ar bayan tahiyar karshe.
  • An so yin addu'a bayan aiki na gari.

Karanta a HadeethEnc.com

9 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa ga Ubangijinsa shi ne idan yana mai sujjada, sai ku yawaita addu'a".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi kusancin lokacin da bawa yake kusanci ga Ubangijinsa shi ne alhalin yana mai sujjada; hakan ya kasance ne saboda mai sallah yana sanya mafi ɗaukakar abin da ke jikinsa a kan ƙasa cikin ƙanƙan da kai da ƙasƙantarwa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - alhali shi yana mai sujjada.

Haƙiƙa (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi umarni da yawaita addu'a a sujjada, sai ƙanƙar da kai ga Allah ya haɗu da faɗa da aikatawa.

Fa'idodi

  • Biyayya tana ƙarawa bawa kusanci ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.
  • An so yawaita addu'a a sujjada; domin cewa ita tana daga wuraren amsawa.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'o'i cikin sallah: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.