Addu'ar shiga da fita daga masallaci

Kalmomin da ake faɗa a ƙofar masallaci, lokacin shiga da lokacin fita.

1 Sau ɗaya

أعوذ بالله العظيم، وبوجهه الكريم، وسلطانه القديم، من الشيطان الرَّجِيم

Ma'ana da tushe

Daga Abdullahi ɗan Amru ɗan Ass - Allah Ya yarda da su -: Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina neman tsarin Allah Mai girma, da fuskarSa Mai girma, da sarautarSa daɗaɗɗiya, daga Shaiɗan abin jefewa", Ya ce: Wannan kawai? na ce: Eh, ya ce: Idan ya ce haka Shaiɗan zai ce : an kiyaye shi daga gareni ragowar yinin.

Abu Dawud ne Ya Rawaito shi Daraja: Hasan ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga masallaci zai ce: (Ina neman tsarin Allah Mai girma) Ina neman tsari ina fakewa ga Allah da kuma siffofinSa (Da fuskarSa mai kyauta) Mai kyauta Mai bayarwa, (Da sarautarSa) RinjayenSa da ikonSa da rinjayenSa akan wanda ya yi nufi daga halittarSa (Madawwami) na tun fi azal na har abada (Daga Shaiɗan abin jefewa) Abin nisantarwa abin korewa daga rahamar Allah, Wato; Ya Allah Ka kiyayeni daga wasiwasinsa da halakarwarsa da tsarinsa da haɗarinsa da ƙawacensa da ɓatarwarsa, domin shi ne sababi a ɓatarwa mai sa halakarwa da jahilci, Aka cewa Abdullahi ɗan Amr "Shin shike nan?" Wato: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi wannan kadai? Ya ce: Eh.

Idan mai shiga masallaci ya faɗi wannan addu'ar; Shaiɗan zai ce : Haƙiƙa an kiyaye ran wannan mai shigowar daga gareni dukkanin lokaci, yininsa da darensa.

Fa'idodi

  • Falalar yin addu'a da wannan zikirin a lokacin shiga masallaci, kuma cewa shi ana kiyaye mai faɗarta daga Shaiɗan a ragowar yininsa.
  • Gargaɗarwa daga Shaiɗan, kuma cewa shi yana jiran musulmi; dan ɓatar da shi da kuma halaka shi.
  • Mutum yana samun kiyayewa daga halakarwar Shaiɗan da karkatarwarsa gwargwadon abinda yake tsayuwa a zuciyarsa na imani da Allah da halarto wannan addu'ar da gasgatawarsa ga alƙawarin Allah abin wanda ta tabbata akansa.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Humaid ko daga Abu Usaid ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da al'ummarsa addu'ar da ake faɗa a yayin shiga masallaci: (Ya Allah ka buɗe min ƙofofin rahamarKa), sai ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sawwaka masa hanyoyin rahamarSa, idan ya yi nufin fita, to, ya ce: (Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa), sai ya roƙi Allah daga falalarSa da ƙarin kyautatawarSa daga arziki na halal.

Fa'idodi

  • An so wannan adddu'ar a yayin shiga masallaci da fita daga cikinsa.
  • Keɓance ambaton rahama a shiga, da falala a fita: saboda mai shiga ya shagalta da abin da zai kusanto da shi zuwa ga Allah da kuma aljannarSa, sai ya dace da ya ambaci rahama, idan ya fita zai tafi a ban ƙasa don neman falalar Allah da arziki, sai ya dace da ambaton falala.
  • Waɗannan zikiran ana faɗinsu ne yayin nufin shiga masallaci, da yayin nufin fita daga cikinsa.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'ar masallaci: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.