Zikiri bayan sallah (bayan kowace sallah)

Ambaton Allah da ake yi bayan sallolin farilla, bayan an yi sallama.

1 Sau ɗaya

أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ (٣)، اللَّهُمَّ أَنْتَ السَّلَامُ وَمِنْكَ السَّلَامُ، تَبَارَكْتَ يَا ذَا الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِ

Ma'ana da tushe

Daga Sauban, Allah Ya yarda da shi: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya sallame daga sallah yana neman gafara sau uku, ya kuma ce: Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareka yake, Ka ɗaukaka ya ma’abocin girma da karamci . Walid ya ce: Na cewa Awza’i: Ya neman gafarar yake? Ya ce: Za ka ce ne:

Ina neman gafarar Allah, ina neman gafarar Allah,

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa idan ya kammala sallarsa; Ina neman gafar Allah, Ina neman gafarar Allah, Ina neman gafarar Allah.

Sannan sai ya girmama Ubangijinsa, ya ce: "Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareKa yake, Ka girmama ya ma’abocin girma da karamci".

Shi Allah tsarkakke ne, kuma cikakke ne a siffofinsa, kuma Ya tsarkaka daga barin kowanne aibu da tawaya, kuma ka nemi waraka daga dukkan sharri duniya da lahira daga wajenSa ba daga wani ba, Shi Allah alheranSa sun yawaita a duniya da lahira, Ma’abocin girma da kyautatawa ne.

Fa'idodi

  • Ana son neman gafara bayan kammala sallah, da kuma dawwama a kan hakan.
  • Ana son neman gafara domin cike tawaya a ibada, da ɗori na kasawa a ibadar.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ

Ma'ana da tushe

Daga Warrad magatakardar Mugira ɗan Shu'uba ya ce: Mugira ɗan Shu'uba ya yi min shifta ( yana fada ina rubutawa) ta wata wasiƙa zuwa ga Mu'awiyya: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne godiya tasa ce, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, ba mai bayar da abin da Ka hana, mai wadata wadatarsa bata amfanar da shi (komai) a wajenKa".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, godiya ta tabbata a gareShi, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, kuma ba mai bayar da abin da Ka hana, kuma mai wadata wadatarsa ba ta amfanar da shi (komai) a wajenKa".

Wato: Ina tabbatar da kalmar tauhidi babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ibada ta gaskiya ina tabbatar da ita ga Allah, kuma ina koreta daga waninSa, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina tabbatar da cewa mulki na haƙiƙa cikakke na Allah ne, dukkanin godiyar wadanda ke sammai da ƙasa abar cancanta ce ga Allah - Maɗaukakin sarki -, yayin da yake Shi mai iko ne a kan dukkan komai, kuma abin da Allah Ya kaddara shi na bayarwa ko hanawa ba mai juyar da shi, kuma a wajenSa wadata ba ta amfanar da ma'abocinta, kaɗai aikinsa nagari ne zai amfanar da shi.

Fa'idodi

  • An so yin wannan zikirin a bayan salloli saboda abin da ke ƙunshe a cikinsa na lafazan tauhidi da godiya.
  • Gaggawa zuwa ga ruko da sunnoni, da kuma yaɗasu.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، ‌وَلَا ‌نَعْبُدُ ‌إِلَّا إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ وَلَهُ الْفَضْلُ وَلَهُ الثَّنَاءُ الْحَسَنُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ

Ma'ana da tushe

Daga baban Zubair ya ce: Dan Zubair ya kasance yana cewa a bayan kowacce Sallah idan ya yi sallama: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki na Sa ne, kuma godiya ta Sa ce, kuma Shi mai iko ne a kan komai. Ba dabara ba ƙarfi sai da Allah, babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi, Shi Ya ke da ni’ima da falala, Shi ke da kyawawan yabo, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsarkake addini gare shi, ko da kafirai sun ƙi. Ya kuma ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗinsu bayan kowacce sallah.

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana HAILALA bayan ya sallame daga kowacce sallah ta farilla da wannan zikirin mai girma,

Ma’anarsa ita ce:

"Babu abin bautawa sai Allah"; Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah.

"Shi kaɗai yake ba shi da abokin tarayya": Wato babu wanda yake tarayya da Shi a Allantaka [ cancantar bauta ] ko a rububiyya [ kasancewarSa Mahalicci, Mai azurtawa, Mai rayawa, Mai matarwa ] ko kuma a sunaye da siffofinSa.

"Mulki na sa ne": Wato; Shi Ya ke da cikakken mulki wanda ya game komai, mulkin sammai da ƙassai da abin da ke tsakaninsu.

"Godiya ta sa ce": Wato shi ne wanda ya siffantu da cikakkiyar cika, wanda ake yabonSa da cika saboda so da girmawa a kowanne lokaci, na farin ciki da na damuwa.

"Shi mai iko ne a kan komai": IkonSa cikakken iko ne ta kowacce fuska, babu abin da yake gagararsa, babu wani al’amari da zai gagare shi.

"Ba dabara ba ƙarfi sai da yin Allah": Wato babu canji daga wani hali zuwa wani halin, ko daga saɓon Allah zuwa ga baiyayyarSa, haka babu ƙarfi, sai da Allah wanda Shi ne Mai taimako, kuma Wanda ake dogara da Shi.

"Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi": karfafawa ce a kan ma’anar Allantaka da kuma kore shirka, da cewa babu wanda ya cancanci bauta in ba Shi ba.

"Ni’ima ta Sa ce da falala": Shi ne wanda ya halicci ni’imomi kuma yake mallakarsu, yake kuma ba da su ga wanda Ya so cikin bayinSa.

"Kyakkyawan yabo nasa ne": A bisa zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa da Ni’imominSa a kowanne lokaci.

"Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsantsanta addini a gareShi": Wato, muna masu Tauhidi, babu riya, kuma babu jiyarwa a kan biyayya ga Allah.

"Koda kafirai sun ƙi": Wato muna masu tabbatuwa a kan Tauhidi da bauta masa ko da kafirai sun ƙi.

Fa'idodi

  • An so kulawada da wannan zikirin bayan kowacce sallah ta farilla.
  • Musulmi yana ji da addininsa, kuma yana bayyana ayyukan addininsa, ko da kafirai sun ƙi.
  • Idan a cikin Hadisi aka ce: "bayan sallah", to, idan abin da a ka ce a Hadisin zikiri ne, to, asali ana nufin bayan sallama, idan kuma addu’a ce, to, ana nufin kafin sallama.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

سُبْحَانَ اللَّهِ (٣٣)، الْحَمْدُ لِلَّهِ (٣٣)، اللَّهُ أَكْبَرُ (٣٣)، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, ya yi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan (lissafin) shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki ya tabbata gareShi, godiya ta tabbata gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai), za'a gafarta masa kurakuran sa, ko da sun kasance tamkar kumfar kogi".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce bayan ƙare sallar farilla:

Sau talatin da uku: "Tsarki ya tabbata ga Allah" (Subhanallah) shi ne tsarkake Allah daga tawaya.

Da kuma talatin da uku: "Godiya ta tabbata ga Allah" (Alhamdulillah) shi ne yabo gareShi da siffofin cika tare da sonSa da girmamaShi.

Da talatin da uku: "Allah ne Mafi girma" (Allahu Akbar) shi ne cewa Allah ne Mafi girma kuma Mafi ɗaukaka daga dukkan komai.

Da cike adadin ɗarin da faɗin: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai. Ma’anarsa: Babu abin bauta da cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi Maɗaukakin Ya keɓanta da cikakken mulki, wanda ya cancanta da Yabo da kambamawa tare da so da girmamawa banda wanda ba shi ba, kuma Shi mai iko ne babu abin da yake gagarar sa.

Wanda ya faɗi hakan an shafe masa kurakuransa kuma an gafarta masa su, ko da sun kasance kwatankwacin farar kunfa ce wacce take saman kogi lokacin da ya kwaranyo.

Fa'idodi

  • An so yin wannan zikirin bayan sallolin farilla.
  • Wannan zikirin sababi ne na gafarar zunubai.
  • Girman falalar Allah - Maɗaukakin sarki - da rahamarSa da gafararSa.
  • Wannan zikirin sababi ne na gafarar zunubai, abin nufi: Kankare ƙananan zunubai, amma manyan zunuban babu abinda yake kankaresu sai tuba.

Karanta a HadeethEnc.com

5 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Ka'ab dan Ujrah - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da wasu zikiran da mai fadainsu ba ya asara kuma ba ya tabewa, kai yana da ladan wadannan kalmomin, kuma sashinsu yana zuwa bayan sashi, ana fadarsu a bayan sallolin farilla, su ne:

"Tsarki ya tabbata ga Allah" sau talatin da uku, wato tsarkakeshi - Madaukakin sarki - daga dukkanin tawaya.

"Godiya ta tabbata ga Allah" sau talatin da uku, ita ce siffanta Allah da cikakkiyar cika tare da soyayyarSa da girmamaShi.

"Allah ne Mafi girma" sau talatin da hudu, Allah ne Mafi girmamawa Mafi buwaya daga dukkan komai.

Fa'idodi

  • Falalar tasbihi da tahmidi da kabbara, su ne wanzajju nagartattu.

Karanta a HadeethEnc.com

6 Sau ɗaya

اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Umamah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallar farilla to babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa".

Nasa'i ne ya rawaito shi a cikin Al-Kubra Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya karanta Ayatul Kursi bayan ƙare sallar farilla babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa; ita tana cikin Suratul Baƙara, faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Wanda komai ya tsayu da Shi, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wanene wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya gajiyar da Shi, Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma} [al-Baƙara: 255].

Fa'idodi

  • Falalar wannan ayar mai girma; dan abinda ta ƙunsa na kyawawan sunaye, da siffofi Maɗaukaka.
  • An so karanta wannan ayar mai girma bayan kowacce sallar farilla.
  • Ayyuka na gari sababi ne na shiga aljanna.

Karanta a HadeethEnc.com

7 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ أَعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ، وَشُكْرِكَ، وَحُسْنِ عِبَادَتِكَ

Ma'ana da tushe

Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannuna, sai ya ce: "Ya Mu'az, wallahi lallai ni ina sonka", sai ya ce: "Ina yi maka wasicci ya Mu'az bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa".

Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannun Mu'aza - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ce masa: Wallahi lallai ni ina sonka, kuma ina yi maka wasicci ya Mu'az a ƙarshen kowace sallah kada kabar faɗin: (Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa) a kowace magana da aikin da zai kusanto da ni zuwa biyayya, (da godiyarKa) ta hanyar samun ni'imomi da tunkuɗe masifu, (da kyakkyawar bautarKa) ta hanyar yin ikhlasi ga Allah da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Fa'idodi

  • Halaccin baiwa mutum labari da sonsa a lamarin Allah.
  • An so yin wannan addu'ar a bayan kowace sallar farilla da nafila.
  • A cikin yin addu'a da waɗannan lafuzan 'yan kaɗan (akwai) abbuwan nema a duniya da lahira.
  • Daga fa'idojin soyayya a lamarin Allah yin wasicci da gaskiya da yi wa juna nasiha da taimakekeniya akan aikin alheri da tsoron Allah.
  • Malam al-Ɗaibi ya ce: Ambatan Allah shi ne kan gaba a buɗewar ƙirji, godiyarSa kuma tsani ce na ni'imomi ababen amsawa, kyakkyawar ibada kuwa abar nema daga gare shi, shi ne nisantar abinda zai shagaltar da shi daga Allah - Maɗaukakin sarki -.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Zikiri bayan sallah: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.