Addu'o'in neman tsarin Allah

Abubuwan da Annabi ﷺ ya nemi tsarin Allah daga gare su.

1 Sau ɗaya

اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ زَوَالِ نِعْمَتِكَ، وَتَحَوُّلِ عَافِيَتِكَ، وَفُجَاءَةِ نِقْمَتِكَ، وَجَمِيعِ سَخَطِكَ

Ma'ana da tushe

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ya kasance daga addu'ar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga abubuwa huɗu:

Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa) ta Addini da duniya kuma in tabbata akan Musulunci, in nisanci faɗawa cikin saɓon da yake gusar da ni'imomi.

Na biyu: (Da juyawar lafiyarKa) da canjata zuwa bala'i; to ina roƙonKa dawwamar lafiya, da kuɓuta daga radaɗi da cututtuka.

Na uku: (Da shammatar azabarKa) daga bala'i ko saɓo, azaba da uƙuba idan suka zo fuj'a bagtatan, to babu wani lokaci a wannan dan tuba da riska, wanda aka shafa da su zai zama mafi girma kuma mafi tsanani.

Na huɗu: (Da dukkan fushinKa) da sabubban da suke wajabta fushinKa; domin wanda Ka yi fushi da shi to haƙiƙa ya taɓe kuma ya yi asara.

Haƙiƙa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zo da lafazin jam'i; dan ya ƙunshi sabubban fushinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - daga maganganu da ayyuka da ƙudirce-ƙudierce.

Fa'idodi

  • Buƙatuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
  • Waɗannan neman tsarin masu albarka sun ƙunshi: Dacewa ga godewar ni'imomi, da kiyayewa daga afkawa cikin saɓo; domin cewa su suna gusar da ni'imomi.
  • Kwaɗayi daga barin nisanta daga guraren fushin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  • (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga shammatar azabar Allah - Maɗaukakin sarki -; domin cewa Shi idan Ya yi wa bawa azaba to haƙiƙa Ya saukar masa da bala'in da ba zai iya tunkuɗeshi ba, kuma ba zai nemi kariyar ragowar halittu ba, koda sun taru gaba ɗaya.
  • (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nemi tsari daga juyawar lafiyarSa - tsarki ya tabbatar maSa -; domin cewa shi idan Allah ya kasance ya keɓance shi da lafiyarSa to haƙiƙa ya rabauta da alherin duniya da lahira, idan ta juya daga gare shi to haƙiƙa an taɓa shi da sharrin duniya da lahira, domin cewa lafiya da ita ce gyaruwar Addini da duniya (suke).

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَالْجُبْنِ وَالْبُخْلِ وَالْهَرَمِ وَعَذَابِ الْقَبْرِ، اللهُمَّ آتِ نَفْسِي تَقْوَاهَا، وَزَكِّهَا أَنْتَ خَيْرُ مَنْ زَكَّاهَا، أَنْتَ وَلِيُّهَا وَمَوْلَاهَا، اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عِلْمٍ لَا يَنْفَعُ، وَمِنْ قَلْبٍ لَا يَخْشَعُ، وَمِنْ نَفْسٍ لَا تَشْبَعُ، وَمِنْ دَعْوَةٍ لَا يُسْتَجَابُ لَهَا

Ma'ana da tushe

Daga Zaid Dan Arƙam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ba zan faɗa muku (komai ba) sai kamar yadda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana faɗa: Ya kasance yana cewa: «‌Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala, da tsoro da rowa, da tsufa, da azabar ƙabari, ya Allah Ka baiwa raina tsoranta, Ka tsarkaketa, Kai ne mafificin Mai tsarkaketa, Kai ne majiɓincin lamarinta kuma shugabanta, Ya Allah ina neman tsarinKa daga ilimin da ba shi da amfani, da zuciyar da bata risina, da zuciyar da ba ta ƙoshi, da addu'ar da ba'a amsarta ».

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Ya kasance daga cikin addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - «‌Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa» da fakewa gareKa, «‌Daga gajiyawa» rashin iko akan dabara mai amfani, «‌Da kasala» rashin samuwar niyyar yin aiki, gajiyayye ba ya iya yin wata dabara, mai kasala kuwa ba ta ma nufinta.

«‌Da tsoro» ta hanyar hanuwa daga gabatowa akan abinda aikata shi yake kamata, «‌Da rowa» da hana abinda bada shi yake wajaba, «‌Da tsufa» yawan shekarun da zai kai zuwa ga raunin jiki, «‌Da azabar ƙabari» Da sabubban da suke kaiwa zuwa ga hakan. «‌Ya Allah Ka bawa raina» Ka bata kuma Ka datar da ita ga «‌Tsron Allahnta» da aikata ɗa'a da barin saɓo, «‌Ka tsarkaketa» Ka tsarkaketa daga ƙasƙanci da munanan ɗabi'u, «‌Kaine mafi alherin wanda Ya tsarkaketa» babu wani mai tsarkaketa inbaKai ba, «‌Kaine majiɓincinta» Mai taimakonta kuma mai tsaya mata, «‌Kuma shugabanta» Mai jiɓintar al'amuranta, kuma Ubangijinta Mamallakinta kuma Mai ni'imtar da ita. «‌Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa daga ilimin da ba shi da amfani», kamar ilimin taurari da bokanci da tsafi, ko wanda ba zai yi amfani a lahira ba, ko ilimin da ba za’a yi aiki da shi ba, «‌Da zuciyar da bata risinawa» gareKa, kuma bata ƙanƙar da kai, kuma bata nutsuwa, bata nutsuwa saboda ambatanKa, «‌Da ran da baya ƙoshi» ba ya wadatuwa da abinda Allah Ya ba shi kuma Ya azurta shi daga halal mai tsarki, «‌Da addu'a» abar juyarwa «‌wacce ba'a amsa mata».

Fa'idodi

  • An so neman tsari daga waɗannan al'amuran, waɗanda aka ambata a cikin hadisin.
  • Kwaɗaitarwa akan tsoron Allah da yaɗa ilimi da kuma aiki da shi.
  • Ilimi mai amfani shi ne wanda yake tsarkake zuciya kuma yake haifar mata da tsoron Ubangiji - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -, sai ya yi naso daga gareta zuwa saurin gaɓoɓi.
  • Zuciya mai tsoron Allah ita ce wacce take jin tsoro, kuma take raurawa a lokacin ambatan Allah sannan ta tausasa ta kuma natsu.
  • Zargin kwaɗayin duniya da rashin ƙoshi daga sha'awowinta da abubuwan jin daɗinta, saboda haka zuciya mai zari mai kwaɗayi akan jin daɗin duniya ita ce mafi ƙiyayyar mutum, saboda haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga gareta.
  • Yana kamata ga mutum ya rabu da sabubban kin karbar add'a da kuma rashin karɓuwarta.
  • Nawawi ya ce: Wannan hadisin da waninsa na addu'o'in da aka yi wa saja'i dalili ne akan abinda malamai suka faɗa; cewa saja'in da aka zarga a cikin addu'a shi ne wanda ake ɗorawa kai, domin cewa shi yana tafiyar da khushu'i da ƙanƙar da kai da kuma ikhlasi, kuma yana shagaltarwa daga tawali'u da buƙatuwa da kuma kakkaɓar zuciya, amma abinda ya samu ba tare da matsawa kaiba, ba kuma tare da aiwatar da tinani dan cikar fasaha ba da kuma makamancin haka, ko wanda aka haddace to babu laifi da shi, kai yana ma da kyau.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

اللهم إني أعوذ بك من فتنة النار، وعذاب النار، ومن شر الغنى والفقر

Ma'ana da tushe

An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- cewa Annabi yana yin Addu'a da wadan nan kalmomi:"Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga fitinar Wuta, da Azabar Wuta, da kuma Sharrin Wadata da talauci"

Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

4 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ مُنْكَرَاتِ الأَخْلاَقِ وَالأَعْمَالِ وَالأَهْوَاءِ

Ma'ana da tushe

Daga Ƙuɗbah ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa: «Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa, daga munanan ɗabi'u da ayyuka da soye-soyen rayuka».

Tirmizi ne ya ruwaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Ya kasance daga cikin addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Ya Allah lallai ni ina neman tsari) ina fakewa (da Kai) banda waninKa, (daga munanan) abubuwan da Allah da ManzonSa suka hana su, (ɗabi'u) kamar ƙullata da hassada da girman kai, (da kuma) munanan (ayyuka) kamar zagi, (da) dukkanin (soye-soyen zuciya), waɗanda zuciya take son su alhali sun saɓawa shari'a.

Fa'idodi

  • Falalar wannan addu'ar kuma an so a yi ta.
  • Mumini yana kwaɗayi akan nisantar ɗabi'u ababen zargi da kuma munanan ayyuka, kuma yana kiyayewa daga bin son rai da kuma afkawa cikin sha'awowi.
  • Rarrabuwar ɗabi'u da soye-soyen zuciya zuwa munana da kuma kyawawa.

Karanta a HadeethEnc.com

5 Sau ɗaya

اللهم إني أعوذ بك من الجوع، فإنه بِئْسَ الضَّجِيعُ،وأعوذُ بِكَ منَ الخِيَانَةِ، فَإنَّهَا بِئْسَتِ البِطَانَةُ

Ma'ana da tushe

An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi: "Ya Ubangiji ina neman tsari da kai daga yinwa, saboda cewa ita ce mafi muni daga..., kuma ina neman daga kai daga Ha'inci"

Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi Daraja: Hasan ne

6 Sau ɗaya

اللهم إني أعوذ بك من شر سمعي، ومن شر بصري، ومن شر لساني، ومن شر قلبي، ومن شر مَنِيِّي

Ma'ana da tushe

An rawaito daga Shakl Bn Humaid -Allah ya yarda da shi- Na ce: Ya Manzon Allah ka koyamun wata Addu'a ya ce kace: "Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga sharrin jina, da kuma sharrin Ganina, da kuma Sharrin Harshena, da kuma Sharrin Zuciyata, da kuma Sharrin farjina"

Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

7 Sau ɗaya

اللهم إني أعوذ بك من البَرَصِ، والجُنُونِ، والجُذَامِ، وَسَيِّئِ الأسْقَامِ

Ma'ana da tushe

An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya ce"Ka nemi tsari da Allah daga Wahalar Bala'i, da Fadawa tabewa, da Mummunan Rabo, da Kuma Dariyar Makiya"

Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'o'in neman tsari: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.