Addu'ar kwanciya barci da zikirin barci

Abin da Annabi ﷺ yake faɗa da karantawa idan zai kwanta.

1 Sau ɗaya

قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ ﴿١﴾ اللَّهُ الصَّمَدُ ﴿٢﴾ لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ ﴿٣﴾ وَلَمْ يَكُن لَّهُ كُفُوًا أَحَدٌ ﴿٤﴾
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ ﴿١﴾ مِن شَرِّ مَا خَلَقَ ﴿٢﴾ وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ ﴿٣﴾ وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ ﴿٤﴾ وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ ﴿٥﴾
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ ﴿١﴾ مَلِكِ النَّاسِ ﴿٢﴾ إِلَهِ النَّاسِ ﴿٣﴾ مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ ﴿٤﴾ الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ ﴿٥﴾ مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ ﴿٦﴾

Ma'ana da tushe

Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wa shinfidarsa kowanne dare yana taro tafikansa, sannan ya yi tofi a cikin su, sai ya karanta a cikinsu: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadi }, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane} (Kul huwa da Falaki da kuma Nasi), Sannan ya shafi abinda ya yi wu daga jikinsa, yana farawa ne da su daga kansa da fuskarsa da abinda ya yi gaba na jikinsa, yanayin haka sau uku.

Bukhari ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Ya kasance daga shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya zo wa shinfidarsa dan ya yi bacci yana tara tafikansa biyu sai ya daga su - kamar yadda mai addu'a yake yi - sai ya yi tofi a cikinsu daga bakinsa sassaukan tofi tare da yawu sassauka sai ya karanta surori uku: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya} da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane}, sannan ya shafi abinda zai yi wu daga jikinsa; yana mai farawa da kansa da fuskarsa da bangare na gaba daga jikinsa, yana maimaita wannan aikin sau uku.

Fa'idodi

  • An so karanta suratul Ikhlas da Mu'awwizataini kafin bacci da tofi da su, da shafar abinda zai yi wu daga jikinsa.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْهِ مِنْ رَبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللَّهِ وَمَلَائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِنْ رُسُلِهِ وَقَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ ﴿٢٨٥﴾ لَا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَا إِنْ نَسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلَا تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلْنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا أَنْتَ مَوْلَانَا فَانْصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ ﴿٢٨٦﴾

Ma'ana da tushe

Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin duk wanda ya karanta ayoyi biyun ƙarshe na Suratul Baƙara cikin dare, to, Allah zai tsare shi daga sharri da abin ƙi, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi nafilar dare, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi addu’oin dare. An ce kuma: su ne mafi ƙarancin abin da zai isa na karatun Alkur’ani a nafilar dare, an ma faɗi wanin haka, kuma muna fatan duk abin da aka faɗa ɗin daidai ne, domin zai ƙunshe su duka

Fa'idodi

  • Bayanin falalar [ayoyin] ƙarshen Baƙara, su ne daga faɗin Allah: (( Manzon ya yi imani….. har zuwa ƙarshen Surah.
  • Ƙarshen Suratul Baƙara yana tunkuɗewa wanda ya karanta mugun abu da sharri da shaiɗanu, idan ya karanta su da daddare.
  • Dare yana farawa ne daga faɗuwar rana, yana kuma ƙarewa ne da hudowar alfijir.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

اللهم ربَّ السماواتِ وربَّ الأرض وربَّ العرش العظيم، ربَّنا وربِّ كلِّ شيء، فالقَ الحَبِّ والنَّوى، ومُنْزِلَ التوراة والإنجيل والفُرقان، أعوذ بك من شرِّ كل شيء أنت آخذٌ بناصيتِه، اللهم أنت الأولُ فليس قبلك شيء، وأنت الآخرُ فليس بعدك شيء، وأنت الظاهرُ فليس فوقك شيء، وأنت الباطن فليس دونك شيء، اقضِ عنَّا الدِّينَ، وأغنِنا من الفقر

Ma'ana da tushe

An rawaito daga Suhail, ya ce: Abu Saleh Ya kasance yana Umartarmu idan dayan mu zai bacci ya kwanta akan bangaren sa na dama, sannan ya ce: "ya Allah Ubangijin Sammai da Kasa kuma Ubangijin Al-arshi Mai girma, Ubangijin kowa ne abu, wanda ya Kawayar iri da kuma kwallon Dabino, Kuma wanda ya saukar da Attausa da Linjila da Kuma Qur'ani, ina neman tsarinka daga Sharrin kowane abu da kai riko da makwankwadarsa, Ya Allah kaine na farko wanda babu wani kafinka, kuma kai ne na Karshen da babu wani a bayanka, kaine Sama da kowa wanda babu wani Sama da kai, Kaine boyayye wanda babu abu ba kai ba, Ka biya mana bashi, kuma ka wadata mu daga Talauci" kuma ya kasance ya rawaito wannan ne daga Abu Huraira, daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

4 Sau ɗaya

اللهم فاطِرَ السماوات والأرض عالم الغيبِ والشهادة، ربَّ كُلِّ شَيءٍ ومَلِيكَه، أَشْهد أن لا إله إلا أنت، أعوذ بك من شرِّ نفسي وشرِّ الشيطان وشِرْكِهِ وأن أقترف على نفسي سوءًا أو أجرُّه إلى مسلم

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - cewa Abu Bakr Al-Siddiq, Allah ya yarda da shi, ya ce: Ya Manzon Allah, don Allah ka fada min kalmomin da nake fada lokacin da na zama, kuma idan na kasance, sai ya ce: "Ka ce: Ya Allah, kai ne Mahaliccin sama da ƙasa, da abunda ke fake da na fili, Ubangijin komai da Mallakarsa, na shaida hakan Babu wani abin bauta sai kai, ina neman tsarinka daga sharrin raina da sharrin Shaidan da shirkarsa, da cewa na aikata sharri ko jawo shi ga Musulmi.Ya ce: "kakatanta idan ka wayi gari ko kayi yammaci ko idan ka tafi kwanciya."

Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

5 sau 3

اللَّهُمَّ قِنِي عَذَابَكَ يَوْمَ تَبْعَثُ عِبَادَكَ

Ma'ana da tushe

Huzaifa Ibnul Yaman -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin yin bacci yana sanya hannunsa ƙarƙashin kansa, sannan ya ce: «‌Ya Allah Ka kareni azabarKa ranar da zaKa tara ko zaka tashi bayinKa».

Tirmizi ne ya ruwaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya kwanta dan yayi barci, sai ya shimfiɗa hannunsa na dama kuma ya sanya kundukukinsa (kumatunsa)na dama akansa, sai ya ce: «‌Ya Allah» Ubangijina «‌Ka kareni» Ka kiyayeni daga «‌azabarKa» da uƙubarKa «‌ranar da zaKa tara ko zaKa tashi bayinKa» a ranar hisabi, ranar alƙiyama.

Fa'idodi

  • Falalar wannan addu'ar mai albarka, kuma an so kiyayewa a kanta dan yin koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • An so kwanciya akan ɓarin jiki na dama.
  • Sindi ya ce: Faɗinsa (Ya Allah Ka kareni azabarKa), a cikinsa cewa yana kamata ga mai hankali ya maida baccinsa tsani dan tina mutuwa da kuma tashi a bayanta.
  • Kariya daga azabar Allah a ranar alƙiyama tana kasancewa ne da falalar Allah da kuma rahamarSa, ta hanyar dacewar bawa ga aiki na gari da kuma gafarar Allah ga bayinSa.
  • Tawali'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa kuma Majiɓincin al'amuransa - Allah Maɗaukakin sarki -.
  • Tabbatar da taruwa da kuma makoma, kuma cewa mutane masu komawa ne zuwa ga Ubangijinsu dan ya yi musu hisabi akan ayyukansu, wanda ya samu alheri to ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki -, wanda ya samu koma bayan haka to kada ya zargi kowa sai kansa, kawai su ne ayyukan bayi Allah Yana kiyaye musu su.
  • Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan bayanin halayen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agagre shi - a baccinsa.
  • Faɗinsa: "Sai ya sanya hannunsa na dama ƙarƙashin kundukukinsa" ya kasance daga al'adunsa - tsra da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne damantawa a cikin kowane abu, sai dai abinda dalili ya zo akan saɓaninsa.
  • Bacci akan ɓarin jiki na dama ya fi saurin farkawa saboda rashin tabbatar zuciya a cikin wannan halin, kuma ya fi sauƙi ga zuciya; domin ita zuciya a ɓangaren hagu take, da a ce bawa ya yi bacci akan ɓarin hagu zai cutar da zuciya dan nauyin gaɓɓai a kanta.

Karanta a HadeethEnc.com

6 Sau ɗaya

الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَطْعَمَنَا وَسَقَانَا، وَكَفَانَا، وَآوَانَا، فَكَمْ مِمَّنْ لَا كَافِيَ لَهُ وَلَا مُؤْوِيَ

Ma'ana da tushe

An rawaito daga Anas -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah ya Kasance idan zai tafi zuwa Makwancinsa yana cewa: "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da mu kuma ya Shayar da mu, kuma ya isar mana kuma ya bamu Makwanci, Saboda da yawa wanda babu mai isar masa ko mai bashi makwanci"

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

7 Sau ɗaya

سُبْحَانَ اللَّهِ (٣٣)، الْحَمْدُ لِلَّهِ (٣٣)، اللَّهُ أَكْبَرُ (٣٤)

Ma'ana da tushe

Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Faɗima - Allah Ya yarda da ita - ta zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tana kawo ƙarar abinda take gamuwa da shi a hannunta na daka, kuma labari ya isar mata cewa wani bawa ya zo masa, bata same shi ba, sai ta ambaci hakan ga A'isha, lokacin da ya dawo sai A'isha ta ba shi labari, (Aliyu) ya ce: Sai ya zo mana alhali mun kwanta, sai muka tafi muka tashi, sai ya ce: "Ku zauna a wurinku" sai ya zo sai ya zauna tsakani na da ita, sai naji sanyin diga-digansa akan cikina, sai ya ce: "Shin bana shiryar daku ga mafi alheri daga abinda kuka tambaya ba? idan kun kwanta - ko kunzo shinfiɗarku - to ku yi tasbihi sau talatin da uku, ku yi hamdala sau talatin da uku, ku yi kabbara sau talatin da da hudu, to shi ne mafi alheri gareku daga dan aiki".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Faɗima - Allah Ya yarda da ita - 'yar manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - takai koken abinda take fama dashi na gurbin kayan niƙan da take niƙawa, lokacin da ribatattu suka zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ta tafi zuwa gare shi zata tambaye shi ɗan aiki daga waɗannan ribatattun; dan ya tsaya a matsayinta akan ayyukan gida, sai dai cewa bata sameshi a gidansa ba, sai ta samu A'isha - Allah Ya yarda da ita -, sai ta bata labarin hakan, Lokacin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi dawo sai Nana A'isha ta ba shi labarin zuwan Faɗima wurin shi dan ta tambaye shi ɗan aiki ne, sai Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo wurin Nana Faɗima da Aliyu - Allah Ya yarda da su - a gidansu alhali su suna kan shinfiɗa suna shirin barci, sai ya zauna tskaninsu har Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ji sanyin diga-digan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan cikinsa, sai ya ce: Shin bana sanar daku mafi alheri daga abinda kuka tanbayeni ba akan na baku ɗan aiki? Suka ce: Eh, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan kun kwanta dan yin bacci da daddare, to ku yi kabbara sau talatin da huɗu, da faɗin: Allahu Akbar, ku yi tasbihi sau talatin da uku, da faɗin: Subhanallahi, ku yi hamdala sau talatin da uku, da faɗin: Alhamdulillah; to wannan zikirin shi ne mafi alheri gareku daga ɗan aiki.

Fa'idodi

  • An so dawwama akan wannan zikirin mai albarka, an ruwaito cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - bai bar wanna wasiyyar ta Annabi ba, mai ƙunsar (abubuwan alheri) har daren da aka yi Siffin.
  • Wannan zikirin ba'a faɗarsa sai a baccin dare kawai, kuma lafazinsa a wurin Muslim daga riwayar Mu'azu daga Shu'uba "Idan kuka kwanta da daddare".
  • Idan musulmi ya manta wannan zikirin a farkon dare sannan ya tina shi a ƙarshensa to babu laifi; domin cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - maruwaicin hadisin yana cewa shi ya manta faɗarsa a daren Siffin a farkon daren sai ya tina sai ya faɗeshi kafin Asuba.
  • Mihlab ya ce; A cikinsa akwai cewa mutum ya ɗora iyalansa kan abinda ya ɗora kansa aikai na fifita lahira akan duniya idan sun kasance suna da iko akan hakan.
  • Ibnu Hajar al’Asƙalani ya ce: Wanda ya lazimce shi ba zai cutu da yawan aiki ba kuma ba zai wahalar da shi ba koda gajiya ta faru gare shi.
  • Al’Aini ya ce: Ta fuskar alherin kodai ana nufin shi yana rataye da lahira ne shi kuma ɗan aiki da duniya, lahira kuwa ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa, ko kuma ana nufin dangane da abinda ta nema da cewa ikon da zata samu ya zama shi ne mafi karfi akan aikin da dan aiki zai yi mata.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'ar kwanciya barci: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Yaya na'urar ƙirga take aiki?

Taɓa na'urar ƙirga da ke ƙarƙashin zikiri, za ta ƙirga baya har zuwa sifili. Tana wannan shafi ne kawai kuma ba a adana komai.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.