Abin da za a yi bayan mafarki mai kyau ko mummuna

Abin da za a yi da faɗa bayan mafarki mai kyau, da bayan mafarki mai firgitarwa.

1 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Katadah- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafarki na gari daga Allah ne, mummunan mafarki kuwa daga Shaiɗan ne, idan ɗayanku ya yi mummunan mafarkin da yake jin tsoronsa to ya yi tofi a hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, to cewa shi ba zai cutar da shi ba".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa kyakkyawan mafarki mai faranta rai a cikin mafarki to daga Allah ne, mummunan mafarki shi ne mafarkin da yake ƙi kuma yake baƙanta rai to daga Shaiɗan ne.

Wanda ya ga abinda yake ƙinsa (a mafarki) to ya yi tofi a ɓangaren hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsu; to cewa shi ba zai cutar da shi ba, inda Allah Ya sanya abinda aka ambata (na Addu’a) sababi ne na kuɓuta daga abin ƙi na abinda jeranta akan mafarki.

Fa'idodi

  • Kyakkyawan mafarki da mummuna wani abu ne daga abinda mai barci yake ganinsa a cikin barcinsa na abubuwa, sai dai (Kalmar: Ru'uya) ta fi rinjaye akan abinda yake ganinsa na alheri da abu mai kyau, kuma (Kalmar: Hulum) ta fi rinjaye akan abinda yake ganinsa na sharri da mummuna, kuma ana anfani da kowane ɗayan daga cikinsu a bigiren ɗayan.
  • Rabe-raben mafarki: 1- Kyakkyawan mafarki, shi ne mafarki na gaskiya kuma bushara daga Allah da (mutum) yake ganinsa ko agane masa. 2- Zancen zuci shi ne abinda mutum yake zantar da kansa a farke. 3- Baƙantawa da tsoratarwar Shaiɗan da razanarwa daga gare shi dan ya baƙanta ran ɗan Adam.
  • Abinda aka ambata a taƙaice daga Babin kyakkyawan mafarki abubuwa ne uku: Shi ne ya godewa Allah akansa, kuma ya yi albushir da shi, kuma ya faɗawa wanda yake so shi banda wanda yake ƙinsa.
  • Abinda aka ambata a taƙaice daga laduban mummunan mafarki abubuwa ne guda biyar: Ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, da kuma sharrin Shaiɗan, kuma ya yi tofi a hagunsa sau uku lokacin da ya farka daga baccinsa, kuma kada ya faɗawa kowa shi, idan ya yi nufin komawa baccinsa to ya juya daga ɓangaren da yake akansa; to cewa shi ba zai cutar da shi ba.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Sa'id Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba".

Bukhari ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa kyakkyawan mafarki mai faranta rai a cikin mafarki to daga Allah ne, kuma ya nunar da cewa ya godewa Allah akansa, ya kuma bada labarinsa, idan kuma ya ga abinda yake ƙinsa yake baƙanta masa rai to shi kawai daga Shaiɗan ne; to ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, kada ya faɗawa kowa; (to mafarkin) ba zai cutar da shi ba , inda Allah Ya sanya abinda aka ambata sababi na kuɓuta daga abinda yake na mugun mafarkin .

Fa'idodi

  • Rabe-raben mafarki: 1- Kyakkyawan mafarki, shi ne mafarki na gaskiya kuma bushara daga Allah da (mutum) yake ganinsa ko agane masa, 2- Zancen zuci shi ne abinda mutum yake zantar da kansa a farke, 3- Baƙantawa da tsoratarwar Shaiɗan da razanarwa daga gare shi dan ya baƙanta ran ɗan Adam ne.
  • Abinda aka ambata a taƙaice a Babin kyakkyawan mafarki abubuwa ne uku: Shi ne ya godewa Allah akansa, kuma ya yi albushir da shi, kuma ya faɗawa wanda yake so shi banda wanda yake ƙinsa.
  • Abinda aka ambata a taƙaice daga ladabin mummunan mafarki abubuwa ne guda biyar: Ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, da kuma sharrin Shaiɗan, kuma ya yi tofi a hagunsa sau uku lokacin da ya farka daga baccinsa, kuma kada ya faɗawa kowa mafarkin, idan ya yi nufin komawa baccinsa to ya juya daga ɓangaren da yake akansa; to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba.
  • Ibnu Hajar ya ce: Hikima a cikinsa cewa shi idan ya fadawa wanda ba ya ƙauna kyakkyawan mafarki zai iya fassara masa da abinda ba ya so kodai dan ƙiyayya ko dan hassada, kuma zai iya faruwa akan waccan siffar ko ya gaggautowa kansa baƙin ciki da takaici daga hakan, to sai aka umarce shi da barin fadawa wanda ba ya so saboda hakan.
  • Godiya a yayin faruwar ni'imomi, da sabuntuwar abubuwan buri, to hakan sababi ne na dawwamar su.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'a bayan mummunan mafarki: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.