Darasi 5 cikin 5
Menene Hajji?
Daga Alƙur'ani
إِنَّ أَوَّلَ بَيۡتٖ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكٗا وَهُدٗى لِّلۡعَٰلَمِينَ ﴿٩٦﴾ فِيهِ ءَايَٰتُۢ بَيِّنَٰتٞ مَّقَامُ إِبۡرَٰهِيمَۖ وَمَن دَخَلَهُۥ كَانَ ءَامِنٗاۗ وَلِلَّهِ عَلَى ٱلنَّاسِ حِجُّ ٱلۡبَيۡتِ مَنِ ٱسۡتَطَاعَ إِلَيۡهِ سَبِيلٗاۚ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ عَنِ ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴿٩٧﴾
Kuma lalle ne, ¦aki na farko da aka aza dõmin mutãne, haƙĩƙa, shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga tãlikai. A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; (ga misãli) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦ãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai.
وَأَذِّن فِي ٱلنَّاسِ بِٱلۡحَجِّ يَأۡتُوكَ رِجَالٗا وَعَلَىٰ كُلِّ ضَامِرٖ يَأۡتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٖ ﴿٢٧﴾
"Kuma ka yi yẽkuwa ga mutãne da wajabcin Hajji su je maka suna mãsu tafiya da ƙafãfu da kuma a kan kõwane maɗankwarin rãƙumi mãsu zuwa daga kõwane rango mai zurfi."
Daga Sunna
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi".
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya ziyarci Dakin Allah - Madaukakin sarki - da Hajji kuma bai yi kwarkwasaba, kwarkwasa ita ce jima'i da abubuwan dake da alaka da shi na sumbata da runguma, kuma ana ambatansa da mummunanan zance, kuma bai yi fasikanciba, ta hanayar aikata sabo da munanan ayyuka ba, Daga fasikanci akwai aikata abubuwan da ka haramta in an yi harama, zai dawo daga hajjinsa wanda aka gafartawa, kamar yadda ake haifar yaro kubutacce daga zunubai.
An kammala tafiya
Madalla!
Rukunan Musulunci biyar
An kammala tafiya 1 cikin 6
Fara tafiya ta gabaAbin da Musulmi suka yi imani da shi