Darasi 4 cikin 5
Me ya sa Musulmi ke azumin Ramadan?
Daga Alƙur'ani
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ ﴿١٨٣﴾ أَيَّامٗا مَّعۡدُودَٰتٖۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٖ فَعِدَّةٞ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَۚ وَعَلَى ٱلَّذِينَ يُطِيقُونَهُۥ فِدۡيَةٞ طَعَامُ مِسۡكِينٖۖ فَمَن تَطَوَّعَ خَيۡرٗا فَهُوَ خَيۡرٞ لَّهُۥۚ وَأَن تَصُومُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ ﴿١٨٤﴾ شَهۡرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلۡقُرۡءَانُ هُدٗى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَٰتٖ مِّنَ ٱلۡهُدَىٰ وَٱلۡفُرۡقَانِۚ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهۡرَ فَلۡيَصُمۡهُۖ وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٖ فَعِدَّةٞ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَۗ يُرِيدُ ٱللَّهُ بِكُمُ ٱلۡيُسۡرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ ٱلۡعُسۡرَ وَلِتُكۡمِلُواْ ٱلۡعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُواْ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمۡ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ ﴿١٨٥﴾
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa, Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhẽri to, shi ne mafi alhẽri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna sani. Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabẽwa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauƙi gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde.
Daga Sunna
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari cewa wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da Allah, yana mai gasgatawa da wajabcin azumin da abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi tanadi na gwaggwaɓan ladaddaki da sakamako, yana mai nufin zatin Allah - Maɗauakakin sarki - da shi ba don riya ko jiyarwa ba, za'a gafarta masa zunubansa da suka shuɗe.