Darasi 1 cikin 2
Me Musulmi suka yi imani da shi?
Daga Alƙur'ani
ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِۦۚ وَقَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ غُفۡرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ ﴿٢٨٥﴾
Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take "
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ ءَامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِي نَزَّلَ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِن قَبۡلُۚ وَمَن يَكۡفُرۡ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا ﴿١٣٦﴾
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ĩmãni da Allah da Manzonsa, da Littãfin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littãfin nan wanda Ya saukar daga gabãni. To, wanda ya kãfirta da Allah da malã'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Rãnar Lãhira, to, lalle ne yã ɓace, ɓata mai nĩsa.
۞ لَّيۡسَ ٱلۡبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ قِبَلَ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ وَٱلۡكِتَٰبِ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ وَءَاتَى ٱلۡمَالَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ ذَوِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِ وَٱلسَّآئِلِينَ وَفِي ٱلرِّقَابِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلۡمُوفُونَ بِعَهۡدِهِمۡ إِذَا عَٰهَدُواْۖ وَٱلصَّٰبِرِينَ فِي ٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَحِينَ ٱلۡبَأۡسِۗ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُتَّقُونَ ﴿١٧٧﴾
Bai zama addini ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan sama da Annabãwa, kuma ya bãyar da dũkiya, akan yana son ta, ga mai zumunta da marãyu da matalauta da ɗan hanya da mãsu rõƙo, kuma a cikin fansar wuya, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bãyar da zakka, da mãsu cika alkawari idan sun ƙulla alkawarin da mãsu haƙuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãƙi. Waɗannan su ne suka yi gaskiya. Kuma waɗannan su ne mãsu taƙawa.
Daga Sunna
Daga Umar ɗan khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da wani mutum ya ɓullo mana mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba’a ganin sawunsa, kuma wani daga cikinmu bai sanshi ba, har ya zauna zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya jingina gwiwoyinsa zuwa gwiwoyinsa, ya ɗora tafukansa a kan cinyoyinsa, sai ya ce: Ya Muhammad, ba ni labari game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Muslulunci: shi ne ka shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, ka tsai da sallah, ka ba da zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci ɗakin (Allah) idan kana da ikon tafiya zuwa gareshi" ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: Sai muka yi mamakinsa, yana tambayarsa yana gasgatashi, ya ce: Ka ba ni labari game da imani, sai ya ce: "Ka ba da gaskiya da Allah, da mala'ikunsa, da littattafansa, da manzanninsa, da ranar lahira, ka ba da gaskiya da kaddara alherinta da sharrinta". Sai ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: Ka ba ni labari game da kyautayi, ya ce: "Ka bautawa Allah kamar kai kana ganinsa, idan ka kasance ba ka ganinsa, to, shi yana ganinka" Ya ce: ka ba ni labari game da al-ƙiyama, ya ce: Wanda ake tambayar bai fi wanda yake tambayar sani ba". Ya ce: Ka ba ni labarin alamominta, ya ce: "Kuyanga za ta haifi uwargijiyarta, kuma za ka ga marasa takalma talakawa masu kiwon dabbobi suna gasar tsawaita gidaje", Ya ce: Sannan ya tafi, sai na zauna ɗan wani lokaci sannan ya ce da ni: "Ya Umar, shin ka san waye mai tambayar?" Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "To, lallai Jibrilu ne ya zo muku don ya sanar da ku addininku".
Bayani
Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - yana ba da labari cewa Jibril - aminci ya tabbata a gare shi - ya fito wurin sahabbai - Allah Ya yarda da su - a surar wani mutum namiji ba a sanshi ba, daga siffofinsa, cewa tufafinsa masu tsananin fari ne, gashin kansa kuma mai tsananin baƙi ne, ba a ganin gurbin tafiya a gareshi na bayyanar gajiya, da ƙura, da rarrabewar gashi, da dattin tufafi, kuma wani ɗaya daga mahalartan bai sanshi ba, alhali su suna zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - irin zaman mai neman sani, sai ya tambayeshi game da musulunci, sai ya ba shi amsa da waɗannan rukunan, waɗanda suka ƙunshi iƙirari da shaida biyu, da kiyayewa a kan salloli biyar, da ba da zakka ga waɗanda suka cancanta, da azimin watan Ramadan, da ba da farillar Hajji a kan mai iko.
Sai mai tambayar ya ce: Ka yi gaskiya, sai sahabbai suka yi mamaki daga tambayarsa mai nuni a kan rashin saninsa a cikin abin da yake bayyana da kuma gasgatashi.
Sannan ya tambaye shi gami da imani, sai ya amsa masa da waɗannan rukunan guda shida masu ƙunshe da imani da samuwar Allah - Maɗaukakin sarki - da siffofinsa, da kaɗaitashi da ayyukansa kamar halitta, da kaɗaita shi da ibada, kuma cewa mala'iku waɗanda Allah Ya haliccesu daga haske bayi ne ababen girmamawa ba sa saɓawa Allah - Maɗaukakin sarki - kuma suna aiki da umarninsa, da yin imani da littattafan da aka saukar ga manzanni daga Allah - maɗaukakin sarki -, kamar Alƙur'ani da At-Taura da Linjila da wasunsu, da kuma (imani) da manzanni masu isar da Addinin Allah, daga cikinsu akwai (annabi) Nuhu, da Ibrahim, da Musa, da Isa, da na ƙarshensu (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su -, da wasunsu daga cikin Annabawa da manzanni, da imani da ranar lahira, abin da ke bayan mutuwa yana shiga cikinsu na kabari da rayuwar barzahu, kuma cewa mutum za a tasheshi bayan mutuwa kuma za a yi masa hisabi, kuma makomarsa za ta zama ko dai zuwa aljanna ko zuwa wuta, da imani da cewa Allah Ya ƙaddara abubuwa gwargwadon yadda iliminsa ya rigaya da shi, kuma hikimarsa ta hukuntashi da rubutunsa ga hakan, da mashi'arsa gareshi, da afkuwarsu gwargwadon yadda ya ƙaddarasu, ya kuma haliccesu don haka. Sannan ya tambaye shi game da kyautatawa, sai ya ba shi labari da cewa kyautatawa ita ce ya bautawa Allah kamar shi yana ganinsa, idan bai samu damar kaiwa zuwa wannan matsayin ba, to, ya bautawa Allah - Maɗaukakin sarki - kamar Allah Yana ganinisa, na farko shi ne matsayin Mushahada, ita ce mafi ɗaukaka, na biyu shi ne matsayin Muraƙabah.
Sannan ya tambaye shi yaushe ne alƙiyama? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana cewa sanin al-ƙiyama yana daga abin da Allah Ya keɓanta da saninsa, babu wani daga halitta da ya sanshi, wanda ake tambayar da mai tambayar.
Sannan ya tambaye shi gami da alamomin alƙiyama? Sai ya bayyana masa cewa daga cikin alamominta akwai yawan kuyangi (sa-ɗaka) da 'ya'yansu, ko yawan saɓawar 'ya'ya ga iyayensu, mata za su dinga yi musu mu'amala irirn mu'amalar bayi, kuma cewa makiyaya dabbobi da talakawa za a shinfiɗa musu duniya a ƙarshen zamani, sai su dinga alfahari a ƙawata gine-gine da ɗaukakasu.
Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labari da cewa mai tambayar shi ne Jibrilu ya zo don sanar da sahabbai wannan addinin miƙaƙƙe.