Addu'ar kafin cin abinci (Bismillah)

Abin da ake faɗa kafin cin abinci, da dalilin ambaton sunan Allah a kan abinci.

1 Sau ɗaya

بِسْمِ اللَّهِ

Ma'ana da tushe

Daga Umar ɗan Abu Salama - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance yaro a kulawar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hannuna ya kasance yana yawo a faranti, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da ni: "Ya kai yaro, ka ambaci Allah, ka ci da damanka, ka ci abin da ke gabanka" hakan bai gushe ba shi ne irin cin abincina bayan nan.

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Umar Dan Abu Salama - Allah Ya yarda da su - ɗan matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Ummu salamah - Allah Ya yarda da ita - yana ba da labari - (cewa) ya kasance ƙarƙashin renonsa da kulawarsa -, cewa ya kasance a tsakiyar cin abinci yana yawo da hannunsa asasannin ƙwarya (kwanon abin ci) don ya ɗauki abincin, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanar da shi ladubba uku daga ladubban cin abinci.

Na farkonsu: Faɗin "Da sunan Allah" a farkon ci.

Na biyunsu: Cin abinci da dama.

Na ukunsu: Cin abinci daga ɓangaren da yake kusa daga gare shi na abincin.

Fa'idodi

  • Daga ladubban ci da sha (akwai) ambaton Allah a farkonsa.
  • Sanar da yara ladubba, musamman ma waɗanda ke ƙarƙashin kulawar mutum.
  • Tausayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da yalwar ƙirjinsa a koyar da yara da ladabtar da su.
  • Daga ladubban abinci akwai cin abin da ke gaban mutum, sai dai idan ya kasance nau'uka ne da yawa, to, yana da damar da zai ɗauki wanda ya so.
  • Lazimtar sahabbai da abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ladabtar da su da shi, hakan abin fahimta ne daga faɗin Umar: Hakan bai gushe (irin) cin abincina ba bayan nan.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Wahshi ɗan Harb - Allah Ya yarda da shi -: Cewa su sun ce: Ya Manzon Allah, lallai mu mun kasance muna ci ba ma ƙoshi, ya ce: «Wataƙila kuna ci ne a rarrabe?» Ya ce: Eh. Ya ce: «To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa».

Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad Daraja: Hasan ne

Sharhi

Wasu daga cikin sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai suka ce: Lallai mu mun kasance muna ci amma bama ƙoshi.

Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce musu: Wataƙila kuna rarrabuwa a lokacin ci; sai kowa ya ci shi kaɗai? Suka ce: Eh. Ya ce: To ku haɗu ku ci ba'a rarrabe ba, kuma ku ambaci sunan Allah a lokacin ci da faɗin: Bismillah (Da sunan Allah), za'a sanya muku albarka a cikinsa, kuma zaku ƙoshi.

Fa'idodi

  • Haɗuwa a abinci da kuma ambatan Allah a lokacin ci sababi ne na samun albarka a cikin abinci, da kuma ƙoshi daga cinsa.
  • Rabuwa dukkaninta sharri ce, haɗuwa kuwa dukkaninta alheri ce.
  • Kwaɗaitarwa akan haɗuwa da kuma ambatan Allah a lokacin abinci.
  • Sindi ya ce: Da haɗuwa ne albarkatu suke sauka a cikin abin ci, kuma da ambatan Allah ne Shaiɗan yake hanuwa daga kaiwa ga abinci.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance idan muka halarci abinci tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ma sanya hannuwanmu har sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara sanya hannunsa, kuma mu wani lokaci mun halarci abinci tare da shi, sai wata kunyanga ta zo kai ka ce ana turota ne, sai ta tafi dan ta sanya hannunta a cikin abincin, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannunta, sannan wani balaraben ƙauye ya zo, kai kace ana turo shi ne, sai ya riƙe hannunsa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai Shaiɗan yana halatta abin cin da ba'a ambaci sunan Allah a kansa ba, kuma shi (shaidan) ya zo da wannan kuyangar ne dan ya halatta shi da ita sai na riƙe hannunta, sai ya zo da wannan balaraben ƙauyen dan ya halatta shi da shi, sai na riƙe hannunsa, lallai hannunsa yana cikin hannuna tare da hannunta».

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su idan suka halarci abinci tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basa sanya hannayensu a cikin abin cin har sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara ya sanya hannunsa, cewa mu wani lokaci mun halarci abinci tare da shi, sai wata kuyanga (baiwa) ta zo saboda tsananin saurinta kai ka ce ana turota, sai ta tafi dan ta sanya hannunta a cikin abin cin, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannunta, sannan wani balaraben ƙauye ya zo kai ka ce ana turo shi ne, sai ya riƙe hannunsa kafin ya taɓa abin cin, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya ce: Lallai Shaiɗan yana samun dama a cikin abin ci idan ya fara cinsa ba tare da ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - ba, lallai ya zo da wannan kuyangar ne dan ya halatta cin abin cin da ita sai na riƙe hannunta, sai ya zo da wannan balaraben ƙauyen dan ya halatta abin cin da shi, sai na riƙe hannunsa, na rantse da wanda raina yake a hannunsa, lallai hannun Shaiɗan yana hannuna tare da hannunta, sannnan ya ambaci sunan Allah ya ci.

Fa'idodi

  • Girmamawar da sahabbai suke yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma ladabinsu tare da shi.
  • yana cikin ladabin cin abin ci shi ne yaro ya jira sai babba da mai daraja ya fara cin abin cin.
  • Shaiɗan yana tunkuɗo wasu daga cikin rafkanannu dan wasu ayyukan da shi ya yarda da su; dan ya samu damar kaiwa ga manufarsa, yana daga hakan abinda ke cikin wannan hadisin.
  • Nawawi ya ce: Malamai sun ce: An so ya bayyana Bismillah dan wani ma ya ji sai ya faɗakar da shi akanta.
  • Idan wani ya zo yana so ya ci abin ci baka ji shi ya ambaci sunan Allah ba to ka riƙe hannunsa har sai ya ambaci sunan Allah.
  • Wajabcin canza abin ƙi ga wanda yake masani, da kuma canza abin ƙi da hannu ga wanda yake da iko.
  • Wannan hadisin aya ce daga cikin ayoyin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, inda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanar da shi abinda ya faru a cikin wannan ƙissar.
  • Shaiɗan ba ya samun damar cin abin cin masu imani saidai idan ba'a ambaci sunan Allah a kansa ba.
  • An so koyawa mutane ladabin ci da sha a cikin Musulunci.
  • An so rantsuwa; dan ƙarfafa umarni ga mai ji.
  • Nawawi ya ce: Ambatan Allah a shan ruwa da nono da zuma da miya da magani da sauran abubuwan sha kamar ambatan Allah ne a abin ci.
  • Nawawi ya ce: Da a ce zai bar ambatan Allah a farkon abinci da gangan ko da mantuwa ko da jahilci ko tilasta masa aka yi ko ya kasa dan wani abu mai bijirowa sannan ya samu damar yi a tsakiyar cin abin cin nasa to an so ya ambaci Allah sai ya ce: “Bismillahi awwalahu wa ãkhirahu”. Ma’ana: (Da sunan Allah a farkonsa da ƙarshensa); saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Idan ɗayanku zai ci abin ci to ya ambaci sunan Allah, idan ya manta ambatan sunan Allah a farkonsa to ya ce: Da sunan Allah a farkonsa da ƙarshensa". Abu Dawud ne ya ruwaito shi.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

A kan Aisha, Allah ya yarda da ita, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cin sahabbansa shida, don haka wani Badawiyi ya zo, kuma ya ci shi da bakinku, don haka ya ce: "Allah ya albarkace ku da ɗan abinci biyu."

Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cin abinci tare da sahabbansa shida, sai wani Balarabe ya zo tare da su sai ya shiga tare da su sai ya ci sauran tare da mors biyu. Koyaya, idan mutum bai sami guba ba, ana cire albarkar daga cikin abincinsa.

Karanta a HadeethEnc.com

5 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare, idan zai shiga bai ambaci sunan Allah a yayin shigarsa ba, Shaidan zai ce: Kun sami makwanci, idan bai ambaci Allah a lokacin cin abincin sa ba, zai ce : Kun riski makwanci da abincin dare".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ambatan Allah a yayin shiga gida da kafin cin abinci, kuma cewa shi idan ya ambaci Allah da fadinsa: (Da sunan Allah) a lokacin shigarsa da kuma lokacin fara abincinsa, Shaidan zai cewa mataimakansa: Baku da rabo na makwanci ko abincin dare a wannan gidan da mai shi ya kare kansa daga ku da ambatan Allah - Madaukakin sarki -. Amma idan zai shiga gidansa bai ambaci Allah a lokacin shigarsa ba ko lokacin cin abincinsa, sai Shaidan ya sanar da mataimaknsa cewa sun sami makwanci, da abincin dare a wannan gidan.

Fa'idodi

  • An so ambatan Allah a lokacin shiga gida da lokacin cin abinci, domin Shaidan yana kwana a cikin gidaje, yana ci daga abincin mutanen gidan idan ba su ambaci sunan Allah - Madaukakin sarki ba -.
  • Shaidan yana lura da Dan Adam a cikin aikinsa da jujjuyawarsa acikin al'amauransa gaba dayansu, idan ya rafkana daga zikiri zai samu abin nufinsa daga gare shi .
  • Zikiri yana kore Shaidan.
  • Kowanne Shaidan yana da mabiya da masoya suna albishir da maganarsa kuma suna bin umarninsa.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'ar kafin cin abinci: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.