Addu'ar bayan cin abinci

Godiya ga Allah da ake faɗa idan an gama cin abinci.

1 Sau ɗaya

الحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَطْعَمَنِي هَذَا وَرَزَقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلاَ قُوَّةٍ

Ma'ana da tushe

Daga Sahlu ɗan Mu'azu ɗan Anas daga babansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa".

Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi Daraja: Hasan ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da wanda ya ci wani abinci da ya godewa Allah, babu wani iko gareni a samun abinci, ko a cinsa sai ga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma taimakonSa, Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi wa wanda ya faɗi hakan bushara da cewa shi ya cancanci gafarar Allah gare shi a abinda ya shuɗe daga zunubansa ƙananu.

Fa'idodi

  • An so godewa Allah - Maɗaukakin sarki - a ƙarshen cin abin ci.
  • Bayanin girman falalar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bayinSa, inda Ya azirtasu kuma Ya sawwaƙa musu sabubban arziƙi , kuma Ya sanya kankare munanan ayyuka a cikin hakan.
  • Al'amuran bayi gabaɗayansu daga Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, ba da dabararsu ko ƙarfinsu ba, kuma bawa abin umarta ne da aikata sabubba.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

الحمد لله الذي أطعمنا وسقانا، وكفانا وآوانَا، فَكَمْ مِمَّنْ لا كَافِيَ له وَلاَ مُؤْوِيَ

Ma'ana da tushe

An rawaito daga Anas -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah ya Kasance idan zai tafi zuwa Makwancinsa yana cewa: "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da mu kuma ya Shayar da mu, kuma ya isar mana kuma ya bamu Makwanci, Saboda da yawa wanda babu mai isar masa ko mai bashi makwanci"

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

3 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Anas Ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan.

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana godiyar da bawa ya ke yi wa Ubangijinsa a kan falalarSa da ni’imarSa suna cikin al’amuran da ake samun yardar Allah da su, idan ya ci abin ci sai ya ce: Na gode wa Allah. Idan ya sha abin sha sai ya ce: Alhamdulillah.

Fa'idodi

  • Karamcin Allah Mabuwayi, haƙiƙa shi ne ya ba da arziƙi, kuma yake yarda da a gode masa.
  • Yardar Allah ana samunta da abu mafi sauƙi, kamar godiya ga Allah bayan ci da sha.
  • Yana daga cikin ladubban ci da sha: Godiya ga Allah maɗaukaki bayan ci da sha.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'ar bayan cin abinci: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.