Addu'ar damuwa, tashin hankali da baƙin ciki

Addu'o'in da Annabi ﷺ ya yi a cikin wahala, kuma ya koyar don damuwa da baƙin ciki.

1 Sau ɗaya

لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ الْعَظِيمُ الْحَلِيمُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَرَبُّ الْأَرْضِ وَرَبُّ الْعَرْشِ الْكَرِيمِ

Ma'ana da tushe

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - Cewa Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin baƙin ciki: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Mai girma kuma Mai haƙuri, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin al'arshi mai girma, babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, Ubangijin sammai, Ubangijin ƙasa, kuma Ubangijin al'arshi mai girma».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin tsananin baƙin ciki da takaici gareshi: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, "Mai girman" daraja, mai girman sha'ani, a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, "Mai haƙuri" wanda ba Ya gaggauto da uƙuba ga mai saɓo kai Yana jinkirtata, kuma Zai iya yi masa afuwa tare da iko akansa, Shi ne Mai iko - tsarki ya tabbatar maSa akan kowane abu. "Babu abin bautawa da gaskiya sai Ubangijin al'arshi mai girma" Mahaliccin al'arshi Mai girma.

"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai da ƙasa" kuma Mahaliccin sammai da ƙasa, kuma Mahaliccin kowane abu a cikinsu kuma Mamallakinsa kuma Mai gyara shi , kuma Mai tasarrufi a cikinsa yanda ya so, "Ubangijin al'arshi mai girma" Mahaliccin al'arshi mai girma.

Fa'idodi

  • Wajabcin gaggawar komawa zuwa ga Allah da addu'a a lokacin saukar musibu da baƙƙan ciki.
  • Anso addu'a da wannan zikirin a lokacin baƙin ciki.
  • Al'arshin al-Rahman wanda Ya daidaita akansa - Maɗaukaki - shi ne mafi ɗaukakar ababen halitta kuma mafi girmansu, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta shi da cewa shi mai girma ne.
  • An keɓanci sammai da ƙasa da ambato; domin cewa sune mafi girman ababen halitta waɗanda ake gani.
  • AlƊaibi ya ce: Ya fara da wannan yabon ne da ambato dan ya dace da yaye baƙin ciki; domin cewa shi ne mahukuntar tarbiyya, kuma acikinsa akwai Hailala wacce ta ƙunshi tauhidi wanda shi ne asalin tsarkake-tsarkake masu girma, da girman da yake nuni akan cikar iko, da haƙuri wanda yake nuni akan ilimi, dan jahili ba'a tinanin haƙuri ko kyauta daga gare shi , kuma sune asalin siffofin girmamawa.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

اللهم إني أعوذ بك من العَجْزِ، والكَسَلِ، وَالجُبْنِ، والهَرَمِ، والبخل، وأعوذ بك من عذاب القبر، وأعوذ بك من فتنة المحيا والممات

Ma'ana da tushe

An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya Manzon Allah yana cewa: "Ya Ubangiji ni ina neman tsarinka daga gajiyawa, da Kasala, da Tsoro, da Tsufa, da Rowa, kuma ina neman tsarinka daga Azabar Kabari, Kuma ina neman tsarinka daga fitinar Rayuwa da ta Mutuwa" a kuma cikin wata riwayar kuma: "Kuma ..............Bashi da Galabar Mutane"

Buhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

3 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ غَلَبَةِ الدَّيْنِ، وَغَلَبَةِ الْعَدُوِّ، وَشَمَاتَةِ الْأَعْدَاءِ

Ma'ana da tushe

Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana Addu’a da waɗannan kalomin: "Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya".

Nasa'i ne ya ruwaito shi da Ahmad Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga wasu al'amra:

Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsari) ina fakewa ina dogara (da Kai) bada wanin Ka ba, (daga rinjayar bashi) da rinjayarsa da baƙin cikinsa da takaicin sa, ina roƙonKa taimako akan biyansa da warware shi.

Na biyu: (Rinjayar maƙiyi) da rinjayansa da ɗora shi akaina, ina roƙon Ka kame cutarsa, da nasararsa a kansa.

Na uku: (Dariyar maƙiya) da farin cikin makiya akan abinda yake samun musulmai na bala'i da musiba.

Fa'idodi

  • Kwaɗaitarwa akan neman tsari daga dukkasn abinda yake shagaltarwa daga ɗa'a kuma yake jawo baƙƙan ciki kamar bashi.
  • Cin bashi kai tsaye babu laifi a cikinsa, kawai damuwa ga wanda ba shi da da abinda zai biya bashin, wannan shi ne bashi mai rinjaye.
  • Mutum ya wajaba akansa ya nisanci al'amuran da za yi masa dariya da su kuma a aibata shi a kansu.
  • Bayanin ƙiyayyar kafirai ga muminai da dariyar ƙetarsu garesu a lokacin aukawar masifu.
  • Maƙiya su bayyanar da farin cikinsu ga musifar mutum yana tsananta bala'in akan mutum.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Da Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ka nemi tsari da Allah daga Wahalar Bala'i, da Fadawa tabewa, da Mummunan Rabo, da Kuma Dariyar Makiya" kuma cikin wata Riwayar Sufyan Al-Sauri ya ce: Ina kokwanton ni na kara daya daga cikin su.

Bukhari da Muslim suka Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

5 Sau ɗaya

اللهم أنت عَضُدِي ونَصِيرِي، بِكَ أَحُول، وبِكَ أَصُول، وبك أقاتل

Ma'ana da tushe

Daga Anas bin Malik, yardar Allah ta tabbata a gare shi, wanda ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zai yi mamayewa, sai ya ce: "Ya Allah, kai ne hannu na kuma mai taimako na, kai ne ƙarfina, adalcin ka, kuma za ka yi yaƙi".

Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'ar damuwa da baƙin ciki: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.