Addu'ar biyan bashi

Addu'o'in samun sauƙi daga bashi da samun arziki na halal.

1 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلاَلِكَ عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكَ عَمَّنْ سِوَاكَ

Ma'ana da tushe

Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - cewa wani wanda aka ɗorawa fansa ya zo masa, sai ya ce: Haƙiƙa ni na kasa biyan fansa ta to ka taimakeni, ya ce: Shin bana sanar da kai wasu kalmomi ba waɗanda mazon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da ni su, da a ce kana da bashi a kanka kwatankwacin dutsen Seer Allah Zai biya maka, ya ce: "Ka ce : Ya Allah Ka wadatar da ni da halalinKa daga barin haram ɗinKa, kuma Ka wadatani da falalarKa daga wanda ba Kai ba".

Tirmizi ne ya ruwaito shi Daraja: Hasan ne

Sharhi

Wani bawa wanda mai shi ya ɗorawa fansa kuma ya yi ittifaƙi tare da shi akan ya sayi kansa ya 'yantata dan ya zama ɗa, kuma ba shi da dukiya, ya zo wurin sarkin muminai Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: Haƙiƙa ni na gajiya (na kasa) daga biyan abinda ke kaina to ka taimakeni akan biyansa da dukiya, ko da koyarwa da shiryarwa, sai sarkin muminai ya ce masa; Shin bana sanar da kai wasu kalmomi ba waɗanda manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani su, da a ce a kanka akwai bashi kwatankwacin wani dutse mai suna Seer na ƙabilar Ɗayyu ne da Allah Ya biya maka shi zuwa ga mai shi, kuma Ya tsamoka daga ƙasƙancinsa, Ya ce: Ka ce: (Ya Allah Ka isar mini) Ka juyar mini Ka nisantar da ni (da halal ɗinKa) ina mai wadatuwa da ita, (daga) faɗawa a (haram ɗinKa), (Kuma Ka wadatar da ni) Ka isar mini (da falalarKa) samuwarKa (daga wanda ba Kai ba) cikin halitta.

Fa'idodi

  • Neman shawara da neman ra'ayin ma'abota ilimi da Addini.
  • Ya wajaba akan ma'abota ilimi da masu Da'awa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - nunawa waɗanda ake kira da shiryar dasu zuwa abinda zai taimakesu akan abinda yake bijiro musu na matsaloli.
  • Kwaɗaitarwa akan taimakon wanda aka ɗorawa fansa.
  • Kwaɗaitarwa akan neman sanin wannan addu'ar, da roƙon Allah da ita.
  • Arziƙi na halal koda ya kadan ne shi ne mafi alheri daga dukiyar haram koda ta kasance mai yawa ce.
  • Neman wadatuwa da Allah maimakon halittarsa.
  • Kwaɗaitarwa akan amsawa mai tambaya amsawa mai kyau idan baka da abinda zaka ba shi.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ غَلَبَةِ الدَّيْنِ، وَغَلَبَةِ الْعَدُوِّ، وَشَمَاتَةِ الْأَعْدَاءِ

Ma'ana da tushe

Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana Addu’a da waɗannan kalomin: "Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya".

Nasa'i ne ya ruwaito shi da Ahmad Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga wasu al'amra:

Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsari) ina fakewa ina dogara (da Kai) bada wanin Ka ba, (daga rinjayar bashi) da rinjayarsa da baƙin cikinsa da takaicin sa, ina roƙonKa taimako akan biyansa da warware shi.

Na biyu: (Rinjayar maƙiyi) da rinjayansa da ɗora shi akaina, ina roƙon Ka kame cutarsa, da nasararsa a kansa.

Na uku: (Dariyar maƙiya) da farin cikin makiya akan abinda yake samun musulmai na bala'i da musiba.

Fa'idodi

  • Kwaɗaitarwa akan neman tsari daga dukkasn abinda yake shagaltarwa daga ɗa'a kuma yake jawo baƙƙan ciki kamar bashi.
  • Cin bashi kai tsaye babu laifi a cikinsa, kawai damuwa ga wanda ba shi da da abinda zai biya bashin, wannan shi ne bashi mai rinjaye.
  • Mutum ya wajaba akansa ya nisanci al'amuran da za yi masa dariya da su kuma a aibata shi a kansu.
  • Bayanin ƙiyayyar kafirai ga muminai da dariyar ƙetarsu garesu a lokacin aukawar masifu.
  • Maƙiya su bayyanar da farin cikinsu ga musifar mutum yana tsananta bala'in akan mutum.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'ar bashi: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.