Surat Az-Zalzalah الزلزلة

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِذَا زُلۡزِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ زِلۡزَالَهَا ١

Idhā zulzilatil-ardu zilzālahā

Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.

وَأَخۡرَجَتِ ٱلۡأَرۡضُ أَثۡقَالَهَا ٢

Wa akhrajatil-ardu athqālahā

Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.

وَقَالَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا لَهَا ٣

Waqālal-insānu mā lahā

Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?"

يَوۡمَئِذٖ تُحَدِّثُ أَخۡبَارَهَا ٤

Yawma'idhin tuhaddithu akhbārahā

A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.

بِأَنَّ رَبَّكَ أَوۡحَىٰ لَهَا ٥

Bi anna rabbaka awhā lahā

cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.

يَوۡمَئِذٖ يَصۡدُرُ ٱلنَّاسُ أَشۡتَاتٗا لِّيُرَوۡاْ أَعۡمَٰلَهُمۡ ٦

Yawma'idhin yasdurun-nāsu ashtātal liyuraw a'mālahum

A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.

فَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٍ خَيۡرٗا يَرَهُۥ ٧

Faman ya'mal mithqāla dharratin khayran yarah

To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.

وَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ شَرّٗا يَرَهُۥ ٨

Waman ya'mal mithqāla dharratin sharran yarah

Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Tambayoyi

Ayoyi nawa ne a Surat Az-Zalzalah?

Surat Az-Zalzalah tana da ayoyi 8. Ita ce sura ta 99 a cikin Alƙur'ani.

Shin Surat Az-Zalzalah Makkiya ce ko Madaniya?

Surat Az-Zalzalah sura Madaniya ce.

A wane juz'i Surat Az-Zalzalah take?

Surat Az-Zalzalah tana cikin juz'i 30.

Zan iya sauraron Surat Az-Zalzalah?

Eh. Danna Kunna a saman wannan shafi, ko ka fara daga kowace aya. Manhajar Qabas kuma tana ba ka damar sauke ta don sauraro ba tare da intanet ba.