Surat Al-'Adiyat العاديات

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلۡعَٰدِيَٰتِ ضَبۡحٗا ١

Wal-'ādiyāti dabhā

Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.

فَٱلۡمُورِيَٰتِ قَدۡحٗا ٢

Fal-mūriyāti qadhā

Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.

فَٱلۡمُغِيرَٰتِ صُبۡحٗا ٣

Fal-mughīrāti subhā

Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.

فَأَثَرۡنَ بِهِۦ نَقۡعٗا ٤

Fa atharna bihī naq'ā

Sai su motsar da ƙũra game da shi.

فَوَسَطۡنَ بِهِۦ جَمۡعًا ٥

Fawasatna bihī jam'ā

Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.

إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٞ ٦

Innal-insāna lirabbihī lakanūd

Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٞ ٧

Wa innahū 'alā dhālika lashahīd

Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka.

وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلۡخَيۡرِ لَشَدِيدٌ ٨

Wa innahū lihubbil-khayri lashadīd

Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.

۞ أَفَلَا يَعۡلَمُ إِذَا بُعۡثِرَ مَا فِي ٱلۡقُبُورِ ٩

Afalā ya'lamu idhā bu'thira mā fil-qubūr

Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.

وَحُصِّلَ مَا فِي ٱلصُّدُورِ ١٠

Wahussila mā fis-sudūr

Aka bayyana abin da ke cikin zukata.

إِنَّ رَبَّهُم بِهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّخَبِيرُۢ ١١

Inna rabbahum bihim yawma'idhil lakhabīr

Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Tambayoyi

Ayoyi nawa ne a Surat Al-'Adiyat?

Surat Al-'Adiyat tana da ayoyi 11. Ita ce sura ta 100 a cikin Alƙur'ani.

Shin Surat Al-'Adiyat Makkiya ce ko Madaniya?

Surat Al-'Adiyat sura Makkiya ce.

A wane juz'i Surat Al-'Adiyat take?

Surat Al-'Adiyat tana cikin juz'i 30.

Zan iya sauraron Surat Al-'Adiyat?

Eh. Danna Kunna a saman wannan shafi, ko ka fara daga kowace aya. Manhajar Qabas kuma tana ba ka damar sauke ta don sauraro ba tare da intanet ba.