Darasi 7 cikin 8
Me ke faruwa bayan mutuwa?
Daga Alƙur'ani
كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَإِنَّمَا تُوَفَّوۡنَ أُجُورَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ فَمَن زُحۡزِحَ عَنِ ٱلنَّارِ وَأُدۡخِلَ ٱلۡجَنَّةَ فَقَدۡ فَازَۗ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ ﴿١٨٥﴾
Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijãrõrinku kawai ne a Rãnar ¡iyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne yã tsĩra. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce jin dãɗin rũɗi.
يَوۡمَئِذٖ يَصۡدُرُ ٱلنَّاسُ أَشۡتَاتٗا لِّيُرَوۡاْ أَعۡمَٰلَهُمۡ ﴿٦﴾ فَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٍ خَيۡرٗا يَرَهُۥ ﴿٧﴾ وَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ شَرّٗا يَرَهُۥ ﴿٨﴾
A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu. To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.
وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا تُرۡجَعُونَ فِيهِ إِلَى ٱللَّهِۖ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ ﴿٢٨١﴾
Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã'anta, kuma sũ bã a zãluntar su.
Daga Sunna
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, wadanne abu biyu ne masu wajabtawa? Sai ya ce: "Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna, wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta"
Bayani
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da dabi'u biyu: Wacce take wajabta shiga Aljanna, da wacce take wajabta shiga wuta? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa: Cewa dabi'ar da take wajabta Aljanna ita ce mutum ya mutu alhali yana bautawa Allah Shi kadai ba ya taranya wani abu da shi, Kuma cewa dabi'ar da take wajabta wuta ita ce mutum ya mutu alhali shi yana taranya wani abu da Allah, sai ya sanya kishiya ga Allah da tamka a cikin AllantakarSa ko a kasancewar shi ne Mahalicci ko sunayenSa da siffofinSa.