Sallar jana'iza: yadda ake yin ta

Sallar jana'iza mataki bayan mataki, tare da addu'o'inta da hadisan da ta zo daga gare su.

Yadda ake yin ta

  1. Tsaya ka fuskanci Alƙibla, a bayan gawa, da niyyar sallar jana'iza. Yi kabbara ta farko (Allahu akbar) ka karanta Fatiha.
  2. Yi kabbara ta biyu, sannan ka yi salati ga Annabi ﷺ kamar yadda ake yi a tahiya.
  3. Yi kabbara ta uku, sannan ka yi addu'a ga mamacin.
  4. Yi kabbara ta huɗu, ka ɗan dakata, sannan ka kammala sallar da sallama.

Babu ruku'u, babu sujada, babu kiran sallah kuma babu iƙama. A mazhabar Hanafiyya ana faɗar yabon buɗe sallah (thana) bayan kabbara ta farko maimakon Fatiha.

Hadisai

1 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Annabi mai tsira da aminchi su kara tabbata a gareshi ya bada labarin rasuwar Najjashi a cikin ranar da ya rasu, sai ya fito da su zuwa wurin sallah, sai ya yi sahu da su, ya yi kabbarori guda hudu

Bukhari da Muslim suka Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annajjashi sarkin Habasha yana da babbar gudunmawa akan wadanda sukayi hijira zuwa kasarsa daga cikin sahabbai, a lokacin da quraishwa suka takura musu a garin makkah,kafin musuluntar mutanen madina sai ya girmama su, sa`annan kyakkyawar niyyar sa da bin gaskiyar sa, da kuma korewa kansa girman kai, suka kaishi ga shiga addinin musulunchi, sai ya rasu a kasar sa, alhalin bai hadu da Annabi ba saboda kyautatawarsa ga musulmai, da girman matsayin sa da kasancewar sa yana wata kasa da ba`ayi masa sallaha cikinta ba, sai manzon Allah mai tsira da aminchi su kara tabbata a gareshi ya baiwa sahabban sa labarin rasuwar Najjashi a ranar da ya rasu a cikinta, sai ya fita da su zuwa wurin yin sallah saboda kambama sha`anin Najjashi don kuma ya bayyanawa sahabban sa cewa ya musulunta da sanar musu da falalar sa da kuma yi masa sakayya gameda abinda ya yiwa masu masu Hijira, da neman yawaitar masu yi masa sallah, sai Annabi ya yi musu sahu sahu ya yi masa sallar gaa`ibi ya yi kabbarori guda hudu a cikin wannan sallar, don neman ceto a gareshi a wajen Allah madaukakin sarki

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abdullah bn Abi, yardar Allah ta tabbata a gare su, ya ce: "Lallai cewa Abdullahi bn Abi Aufa yayi Kabarbaru Hudu a jana'izar 'ya mace, don haka sai ya tashi bayan ta hudu abunda yake tsakanin Kabbarorin biyu yana neman gafararta sai ya yi addu'a, sannan ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare sh - ya kasance yana yin hakan": Kuma a wata ruwaya: Ya yi kabbara sau Hudu , sai ya zauna wani lokaci har sai da nayi zaton zai yi kabbara ta biyar ne, sannan ya yi sallama a damansa da hagu. Lokacin da ya tafi, sai muka ce masa: Menene wannan? Ya ce: Ba zan kara muku ba a kan abin da na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aikata, ko kuma: Wannan shi ne yadda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi

Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Hakim Ya Rawaito shi Daraja: Hasan ne

Sharhi

Abdullahi bn Abi Aufa - Allah ya yarda da shi - ya ba da labarin cewa ya yi Sallar jana’izar ‘yarsa, don haka sai ya yi Mata Kabbara hudu, kuma bayan ta hudan yayi Mata Addu'a Kuma ya nema mata gafara da dalla-dalla game kan hakan. shine ya yi kabbara ta shiga salla, sannan ya karanta fatiha, sannan ya ce a ta biyun kuma, sai ya yi salati ga Annabi mai tsira da amincin Allah, sannan ya yi kabbara ta uku, sannan yayi wa mamacin Addu'a, sannan ya Kabbara ta Hudu. Kuma Abdullahi bn Abi Aufa - Allah ya yarda da shi - ya ce bayan ya yi sallama ga wadanda suka yi salla tare da shi: Haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi. Wato yayi Kabbara Hudu kuma yayi Addu'a ga Mamaci bayan ta huɗu. Kuma a cikin wata ruwaya: Ya cewa shi yayi Kabarbari hudu, sa’an nan ya yi Masa Addua kuma ya nemi gafara bayan ta huɗun, har sai ya tabbatar da cewa a bayansa za a ce ta biyar kuma, sannan ya gabatar da Sallama biyu: ta farko a gefen dama, kuma ta biyu a na hagu, kamar sallah .Kuma bayan cikar Sallar wani da yake bayansa ya tambayeshi Dangane da dalilin jinkirinsa bayan kabbarar ta huxu, kuma bai Sallama daga ia ba nan ba, sai ya ce: Abin da kuka yi ba shi da wani abu da ya wuce abin da Manzon Allah - SAW. An ruwaito ijma'i a kan haka, kamar yadda yake a cikin Al-Mughni na Ibnu Qudamah, kuma wannan hadisin ya kasance hadisi Hasan ne a wajen Al-Albani, amma akwai Sabani a tsakanin malamai dangane da ingancin sa. Domin a cikin isnadinsa akwai Ibrahim Al-Hijri, wanda yake mai rauni ne, kuma akwai Hadisin marfoo'i da ya zo a cikin Sallama daya, kuma a cikinsa akwai Irsali.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

اللهم إن فلان ابن فلان في ذمتك وحبل جِوَارِكَ، فَقِهِ فِتْنَةَ القبر، وعذاب النار، وأنت أهل الوفاء والحمد؛ اللهم فاغفر له وارحمه، إنك أنت الغفور الرحيم

Ma'ana da tushe

Daga Wahathah bn Al-Asqa - yardar Allah ta tabbata a gare shi - tare da isnadi: "Manzon Allah - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mana addu'a a kan wani mutum Musulmi, kuma na ji yana cewa:" Ya Allah, dan-haka dan haka-yana cikin kariyarka da taron makwabtaka, don haka ka sanya shi fitinar kabari, kuma azabar ka ce wutar, Aminci da yabo; Ya Allah ka gafarta masa ka yi masa rahama, lallai kai mai gafara ne, mai jinqai. ”

Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi, Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi sallar jana'iza ga wani mutum Musulmi, sannan ya ce abin da ake nufi: Ya Allah, da-da-da-bin-haka-da-lafiya yana cikin aminci da kariya, kuma yana neman gafarar ka Don haka ka tabbatar da shi yayin neman jarabawa a cikin kabari, kuma ka tsare shi daga azabar wuta, domin ba ka rasa lokacin da aka kayyade, kuma ku mutanen gaskiya ne, don haka Allah ya gafarta masa ya yi masa rahama, kai babban dillalin gafara ne ga zunubai, da kuma yawan rahama ta hanyar karbar biyayya da ninka ayyukan alheri.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Samurata Dan Jundub Allah ya yarda da shi yace: "Na yi salla ga wata mata data rasu a dalilin nifasinta a bayan Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi- sai ya tsaya a tsakkiyarta".

Bukhari da Muslim suka Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Sallatar mamaci hakki ne na wajibi ga ko wane mamaci cikin musulmi: namiji ko mace, karami ko babba, shi ne Samurata ke bamu labari cewa yayi salla a bayan Annabi lokacin da yake salla ga wata mata ta rasu a sanadiyar jinin haihuwa, sai Annabi tsira da aminci ya tsaya a saitin tsakkiyarta.

Karanta a HadeethEnc.com

5 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

an karbo daga Abi Huraira Allah ya yarda dashi an daga hadisin zuwa ga Annabi: "wanda ya halarci Gawa har akai mata salla yana da kiradi guda.wanda kuma ya halarce ta har aka binneta yana da kiradi biyu.sai aka ce: menene kiradi biyu? sai yace: kwatankwacin manyan dutsuna biyu" a wata ruwayar kuma: "mafi kankantarsu kwatankwacin dutsen Uhudu"

Bukhari da Muslim suka Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Allah mai madaukakin suna da albarka mai tausasawa ne ga bayinsa, sa`annan yana nufin da ya shimfida musu dalilan yin gafara a garesu, musamman ma lokacin da zasu bar duniya, wadda ta ke ita ce gidan aiki, izuwa gidan da za`a ninke takardun ayyukan su a cikin ta. don hakanan ne ya kwadaitar bisa yin sallar jana`iza da halartar ta, saboda ita sallar neman ceto ne ga mamaci kuma tana kasancewa dalilin samun rahamar Allah. sai ya sanya ladan qiradi ga wanda ya sallace ta, ya kuma sanya wani ladan qiradin ga wanda ya halarci binne ta. wannan wani gwargwado ne daga lada mai girma kuma matsayinsa sananne ne wurin Allah madaukakin saki. yayin da gwargwadon girman wannan lada ya buya ga sahabbai Allah ya kara yarda a gare su- sai Annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kusanto da shi ga kwakwalen su, ta yadda kowane qiradi ya kai girman babban dutse; saboda abinda ke ciki na girma tsayawa akan hakkin dan uwansa musulmi tare da yin addu`ah a gareshi da tunatarwa dangane da makoma da debewa mutanen gidan kewar mamacin su da wanin haka da maslahohi.

Karanta a HadeethEnc.com

6 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku yi gaggawa da jana'iza, idan ta gari ce to alheri kuke kaita gare shi, idan kuma koma bayan haka ne, to sharri ne kuke sauke shi daga wuyayenku".

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yin gaggawa da shirya jana'iza da yi mata sallah da kuma binneta; idan jana'izar ta kasance ta garice to alheri ne, kuke gabatarwa gare shi na ni'imar ƙabari, idan kuma ta kasance koma bayan haka ne to sharri ne kuke saukewa daga wuyayenku.

Fa'idodi

  • Ibnu Hajar ya ce: An so yin gaggawa, sai dai ta inda abinda ake jin tsoron faruwar ɓarna ga mamaci, ko wahala akan mai ɗaukar ko mai rakiyar ya tsanananta matuƙa.
  • An ƙayyade gaggawar da idan mutuwar bata zama fuj'a ba wacce ake jin tsoron ta zama suma ce, to yana kamata kada a binneta har sai an tabbatar da mutuwarsa, ko ya zama akwai wata maslaha a cikin jinkirta shi, na yawaitar masallata, ko halartar 'yan uwansa, kuma ba'a jin tsoron ta ɓaci.
  • Kwaɗaitarwa akan yin gaggawa da jana'iza dan maslahar mamaci idan ya kasance ɗan aljanna ne, ko dan maslahar 'yan rakiya idan ya kasance ɗan wuta ne.
  • Nawawi ya ce: Ana ɗauka daga gare shi (wannan Hadisin) barin abokantakar da mutanen banza waɗanda ba mutanen kirki ba.

Karanta a HadeethEnc.com

7 Sau ɗaya

لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku laƙƙanawa matattunku: Laa ilaha illallah»

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitarwa kan mu faɗi kuma mu maimaita kalamr Tauhidi "La'ilaha illallahu" a wurin wanda fizgar mutuwa ta zo masa har sai ya faɗeta, dan ta zama ƙarshen maganarsa.

Fa'idodi

  • An so yi wa wanda mutuwa ta halarto masa talƙini.
  • An karhanta yawaita yin talƙini ga wanda mutuwa ta halarto masa, da kuma nacewa a kansa idan ya karɓi talƙinin, ko an fahimci hakan daga gare shi; dan kada ya takura masa sai ya furta abin da bai dace ba.
  • Nawawi ya ce: Idan ya faɗeta sau ɗaya to kada ya maimaita masa saidai idan ya yi wata maganar daban a bayansa, sai asake bijiro masa da ita dan ta zama ita ce ƙarshen zancensa.
  • Hadisin ya ƙunshi halartar wurin da wanda mutuwa ta halarto masa dan tinatar da shi da kuma yi debe masa kewa da rintse idanuwansa da kuma tsayuwa da haƙƙoƙinsa.
  • Rashin halaccin yin talƙini bayan mutuwa da wurin ƙabari bayan an binne; saboda rashin aikata hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Karanta a HadeethEnc.com

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Sallar jana'iza: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.