Addu'a ga mara lafiya da ziyarar mara lafiya

Abin da ake faɗa lokacin ziyartar wanda ba shi da lafiya.

1 Sau ɗaya

لا بأس؛ طَهُور إن شاء الله

Ma'ana da tushe

An Rawai to daga Abdullahi Bn Abbas -Allah ya yarda da su- Cewa Annabi ya shiga wajen wani Balaraben Kauye ya duba shi, "Ya ku Jama'ar Muhajirai da Mutanen Madina, Lallai cewa daga cikin ku akwai wasu Mutane basu da Dukiya, ko Dangi, saboda haka wani daga cikinku ya hadu da Biyu ko Uku"

Buhari ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

2 sau 7

أَسْأَلُ اللَّهَ الْعَظِيمَ رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيَكَ

Ma'ana da tushe

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya duba mara lafiya (wanda) ajalinsa bai yi ba, sai ya ce a wurinsa sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya, sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar".

Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani musulmin da zai ziyarci wani musulmi a cikin rashin lafiyarsa wanda lokacin mutuwarsa bai yi ba, sannan mai ziyarar ya yi wa mara lafiya addu'a da faɗinsa: (Ina roƙon Allah Mai girma) a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, (Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya), kuma ya maimaitata hakan sau bakwai sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar.

Fa'idodi

  • An so addu'a ga mara lafiya da wannan addu'ar, da kuma maimaitata sau bakwai.
  • Tabbatar da waraka ga wanda aka faɗi wannan addu'ar a wurinsa da izinin Allah - Maɗaukakin sarki -, in ta bijiro da gaskiya da kuma salaha.
  • Zai faɗi wannan addu'ar ne a ɓoye da bayyane, dukkan hakan ya halatta, sai dai idan ya jiyar da mara lafiyar to shi ya fi; domin a cikinsa akwai shigar da farin ciki gare shi.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

أَذْهِبِ الْبَاسَ، رَبَّ النَّاسِ، وَاشْفِ أَنْتَ الشَّافِي، لَا شِفَاءَ إِلَّا شِفَاؤُكَ، شِفَاءً لَا يُغَادِرُ سَقَمًا

Ma'ana da tushe

Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wajan mara lafiya yana yi masa addu'a zai ce : «Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu wata waraka sai warakarKa, warakar da bata barin wata masassara».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ziyarci wani mara lafiya zai yi masa addu'a sai ya ce: Ya Allah (Ka tafiyar) Ka gusar da (tsanani) da tsananin rashin lafiya, (ya Ubangijin mutane) kuma Mahaliccinsu kuma Mai renansu, (Ka warkar da) wannan mara lafiyar (Kai ne) tsarki ya tabbatar maKa (Mai warkarwa) ina kamun ƙafa zuwa gareKa da sunanKa Mai warkarwa, (babu wata waraka) mai tabbata ga mara lafiya (sai warakarKa) da kuma lafiyarKa, (waraka) kai tsaye (wacce bata bari) ta wanzar ta kuma bar (wata masassara) da wani rashin lafiyar daban.

Fa'idodi

  • Mai warkarwa Shi ne Allah - Mai girma da ɗaukaka -, amma likita da magani to su biyun sabubba ne basa anfanarwa kuma ba sa cutarwa sai da izinin Allah.
  • Gaida mara lafiya yana daga haƙƙoƙi tsakanin musulmai, hakan cancanta ga iyalai.
  • Kwaɗaitarwa ga wanda ya ziyarci mara lafiya ya yi masa wannan addu'ar mai albarka waccea aka ruwaito.
  • Daga shiryrwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yin magani da ruƙya ta shari'a da Alƙur'ani da kuma addu'o'i masu tsarki, saboda haka tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana yi wa kansa ruƙya idan ya yi rashin lafiya, haka nan yana yi wa wanda ya yi rashin lafiya daga iyalansa da wasunsu ruƙiyya.
  • Ibnu Hajar ya ce: Haƙiƙa yi wa mara lafiya addu'ar waraka tare da abinda ke cikin rashin lafiya na kankare zunubai da lada kamar yadda hadisai suka zo da hakan ya rikitar, to amsa ita ce: Lallai addu'a ibada ce, kuma bata kore lada da kuma kaffara; domin cewa su suna samuwane a farkon rashin lafiyar da kuma haƙuri a kanta, mai addu'a yana tsakanin kyawawa biyu: Kodai abin nufinsa ya samu, ko kuma a canja masa da jawo wani anfanin ko tunkuɗe cuta, kowanne daga cikinsu daga falalar Allah ne.

Karanta a HadeethEnc.com

4 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ رَبَّ النَّاسِ، مُذْهِبَ البَأسِ، اشْفِ أنْتَ الشَّافِي، لاَ شَافِيَ إِلاَّ أنْتَ، شِفَاءً لاَ يُغَادِرُ سَقماً

Ma'ana da tushe

An rawaito daga Anas -Allah yayarda da shi- cewa shi ya ce da Sabit -Allah ya yi masa rahama: bana yo maka Rukya ba da rukyar Manzon Allah -Amincin Allah a gareshi-? ya ce E , yace: "Ya Ubangiji Mai renon Mutane, mai tafiyar da cuta, ka warkar kaine mai warkawa, babu mai warakarwa sai kai, warakarwar da bata barin cuta"

Buhari ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Lallai cewa Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya kirawo Sabit Al-Bunani kuma ya ce da shi bana yi maka Ruqya ba da Ruqyar Manzon Allah SAW ya kasance yana roqon Ubagijinsa ga Mara lafiya kan ya yayewa mara lafiyar tsananinsa da raxaxinsa kuma ya sanya shi waraka da babu wata Waraka bayanta, kuma Malamai sun haxu kan halacin Ruqya idan ta haxa abubuwa uku: 1- ta kasance da zancen Allah aka yi ta ko sunayensa ko Siffofinsa, 2-kuma ta kasance da Yaren Larabci ko kuma da abunda za'a iya gane Ma'anarsa, kuma anso ta Kasance da Lafazan da suka zo a cikin Hadisisai 3-kuma mai yin Ruqya xin ya qudurce cewa Ruqyarsa ba ba zatayi tasiri ba ita kaxai sai da qudurar Allah SWT

Karanta a HadeethEnc.com

5 Sau ɗaya

اللَّهُمَّ اشْفِ سَعْداً، اللَّهُمَّ اشْفِ سَعْداً، اللَّهُمَّ اشْفِ سَعْداً

Ma'ana da tushe

Daga Saad bin Abi Waqas - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: Manzon Allah - SAW- ya tursasa ni ya ce: "Ya Allah, ka warkar da farin ciki, ya Allah, ka warkar da farin ciki, ya Allah, ka warkar da Sa'adi".

Bukhari da Muslim Suka Rawaito shi amma lafazin na Muslim ne Daraja: Ingantacce ne

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Addu'a ga mara lafiya: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Yaya na'urar ƙirga take aiki?

Taɓa na'urar ƙirga da ke ƙarƙashin zikiri, za ta ƙirga baya har zuwa sifili. Tana wannan shafi ne kawai kuma ba a adana komai.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.