Ruqya daga Sunna: addu'o'in ciwo da waraka

Kalmomin waraka da Annabi ﷺ ya yi amfani da su kuma ya koyar.

1 Sau ɗaya

بِاسْمِ اللهِ (٣)
أَعُوذُ بِاللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ (٧)

Ma'ana da tushe

Daga Usman ɗan Abul Aas al-Saƙafi - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya kai kukan wani ciwo da yake jinsa a cikin jikinsa wajen Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tunda ya musulunta, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: "Ka sanya hannunka akan wurin da kake jin raɗaɗin daga jikinka, ka ce: Da sunan Allah sau uku, kuma ka ce sau bakwai “Ina nema tsarin Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro".

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Wani ciwo ya kama Uman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya kusa ya halakar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo l ya duba shi, kuma ya sanar da shi wata addu'ar da Allah zai ɗauke masa abinda ya saukar masa na rashin lafiyar; shi ne ya ɗora hannunsa akan wurin da yake jin ciwon, kuma sai ya ce: Bismillah, (Da sunan Allah) sau uku, sannan ya ce sau bakwai: (Ina neman tsari) ina fakewa kuma ina katanguwa (Da Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji)na raɗaɗi a wannan lokacin (kuma nake tsoro) nake jin tsoron faruwarsa a nan gaba na baƙin ciki da tsoro, ko ya wannan cutar ta ci gaba kuma radadinta ya yadu a jiki.

Fa'idodi

  • An so mutum ya yi wa kansa tawaida kamar ydda ya zo a cikin hadisin.
  • Kai kuka - ba tare da kurari ba ko bijirewa - ba ya kore dogaro (ga Allah) da kuma haƙuri.
  • Addu'a tana daga jumlar aikata sabubba, saboda haka yana kamata a takaitu da lafazzukanta da kuma adadinta.
  • Wannan addu'ar tana kasancewa ne ga dukkan wani raɗaɗi na gaɓa.
  • Ɗora hannu akan wurin raɗaɗi a lokacin yin tawaida da wannan addu'ar.

Karanta a HadeethEnc.com

2 Sau ɗaya

بِاسْمِ اللهِ أَرْقِيكَ، مِنْ كُلِّ شَيْءٍ يُؤْذِيكَ، مِنْ شَرِّ كُلِّ نَفْسٍ أَوْ عَيْنِ حَاسِدٍ، اللهُ يَشْفِيكَ بِاسْمِ اللهِ أَرْقِيكَ

Ma'ana da tushe

Daga Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi -: Cewa (Mala’ika) Jibril ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Muhammad baka da lafiya ne? sai ya ce: «‌Eh» ya ce: «‌Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan abinda zai cutar da kai, daga sharrin kowane rai ko maitar mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya».

Muslim ne ya rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Sharhi

Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya tambaye shi: Ya Muhammad kana fama da rashin lafiya ne? Sai ya ce: Eh. Sai Mala’ika Jibril ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa ruƙya da faɗinsa: «‌Da sunan Allah» ina mai neman taimakonSa «‌Nake maka ruƙya» nake nema maka tsari. «‌Daga dukkan abinda yake cutar da kai» ƙarami ne ko babba. «‌Daga kowace rai» mummuna. «‌Ko maitar mai hassada» da ya kai gareka, Allah «‌Ya warkar da kai» kuma ya kareka daga dukkanin cutuka. «‌Da sunan Allah nake maka ruƙya» ya maimaita shi ne dan kai matuƙa, kuma ya fara da shi kuma ya rufe da shi dan nuni zuwa ga cewa babu wani mai amfanarwa sai Shi - tsarki ya tabbatar maSa -.

Fa'idodi

  • Halaccin labarta rashin lafiya dan bayanin waƙi'in hali ba dan babin rashin haƙuri da kai kuka ba.
  • Ruƙya tana halatta da sharuɗɗan nan masu zuwa: 1- Ta zama da Alƙur'ani ne ko da ambatan sunan Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma addu'o'in da aka shara'anta. 2- Ta zama da harshen larabci, ko da abinda ake sanin ma'anarsa daga wasu harsunan daban. 3- Ya ƙudirce cewa ruƙya ita akan kanta bata tasiri; kawai ita sababi ce daga cikin sabubban da basa tasiri sai da izinin Allah - Mai girma da ɗaukaka -. 4- Ta kaɗaita daga shirka, ko abinda aka haramta, ko bidi'a, ko abinda zai kai zuwa ga hakan.
  • Tabbatar da cutar lambing baka ( ko maita), kuma cewa ita gaskiya ce, to yana kamata a nemi yin ruƙya daga gareta.
  • An so yin ruƙya da abinda ya zo a cikin hadisi.
  • Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar waninsa ne daga mutane, duk abinda yake samun waninsa na rashin lafiya zai iya samunsa.
  • Kulawar Allah ga AnnabinSa- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kiyayeShi, da wakilta mala'ikunSa da hakan.

Karanta a HadeethEnc.com

3 Sau ɗaya

Ma'ana da tushe

An rawaito daga Abu Sa'id Al-khudri -Allah ya yarda da shi- ya ce:Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi-ya Kasance yana neman tsari daga Aljani da kuma Kanbun baka" har Falaki da Nasi suka sauka, yayin da suka sauka, sai ya dauke su yabar wasunsu"

Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi Daraja: Ingantacce ne

Tambayoyi

Me ke cikin wannan shafi?

Ruqya daga Sunna: kowanne da Larabci, tare da ma'anarsa, hadisin da ya zo daga gare shi, darajarsa da sharhi.

Daga ina fassarorin suke?

Daga HadeethEnc.com, Kundin Fassarar Hadisan Annabi. Ana nuna kowane hadisi daidai yadda suka wallafa shi, tare da tushensa da darajarsa, da hanyar haɗi zuwa asalin.

Zan iya samun tunatarwa ta kullum?

Eh. Manhajar Qabas ta Android kyauta tana tunatar da kai zikirin safe da yamma kowace rana, kuma tana da irin wannan na'urar ƙirga.