Darasi 10 cikin 11
Me ya sa Allah yake barin wahala da musibu?
Amsa a taƙaice
Wannan rayuwa jarrabawa ce. Allah yana jarrabtar mutane da wahala da sauƙi domin ya bayyana wanda ya yi haƙuri da wanda ya kyautata aiki. Ga mumini babu wani ciwo da ke tafiya a banza: ko sukar ƙaya tana shafe wasu daga cikin zunubansa, kuma Allah ya yi alƙawarin babban lada da rahama ga waɗanda suka yi haƙuri suka koma gare shi. Alƙur'ani kuma ya yi alƙawarin cewa tare da tsanani akwai sauƙi, kuma cikakken adalci yana jira a rayuwa ta gaba.
Qabas ne ya rubuta ta, kuma an duba ta da Al-Mukhtasar fi Tafsir al-Qur'an al-Karim, Tafsirin Ibn Kathir da bayanan HadeethEnc.com.
Daga Alƙur'ani
وَلَنَبۡلُوَنَّكُم بِشَيۡءٖ مِّنَ ٱلۡخَوۡفِ وَٱلۡجُوعِ وَنَقۡصٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَنفُسِ وَٱلثَّمَرَٰتِۗ وَبَشِّرِ ٱلصَّٰبِرِينَ ﴿١٥٥﴾ ٱلَّذِينَ إِذَآ أَصَٰبَتۡهُم مُّصِيبَةٞ قَالُوٓاْ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيۡهِ رَٰجِعُونَ ﴿١٥٦﴾ أُوْلَٰٓئِكَ عَلَيۡهِمۡ صَلَوَٰتٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَرَحۡمَةٞۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُهۡتَدُونَ ﴿١٥٧﴾
Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙasa daga dũkiya da rãyuka da 'ya'yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri. Waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmãwa." Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan sũ ne shiryayyu.
أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتۡرَكُوٓاْ أَن يَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا وَهُمۡ لَا يُفۡتَنُونَ ﴿٢﴾ وَلَقَدۡ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡكَٰذِبِينَ ﴿٣﴾
Ashe, mutãne sun yi zaton a bar su su ce: "Mun yi ĩmãni," alhãli kuwa bã zã a Jarrabe su ba?" Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabãninsu, dõmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata.
فَإِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرًا ﴿٥﴾ إِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرٗا ﴿٦﴾
To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
Daga Sunna
Daga Abu Sa'id Alkhudri da Abu Hurarira - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba abinda yake samun musulmi na wahala ko rashin lafiya ko bakin ciki ko takaici ko cuta ko bakin ciki har kayar da zai taka, sai Allah ya kankare masa kurakuransa da su".
Bayani
Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa abinda musulmi yake samu na cutuka da bakin cki da takaici da masibu da tsanani da tsoro da yunwa - kai koda akwai kayar da za ta taba shi ta sashi radadi -, hakan zai zama kaffara ga zunubansa da kuma kankare kurakuransa.