Sanin Musulunci

Darasi 5 cikin 8

Wanene Annabi Muhammad?

Daga Alƙur'ani

مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَآ أَحَدٖ مِّن رِّجَالِكُمۡ وَلَٰكِن رَّسُولَ ٱللَّهِ وَخَاتَمَ ٱلنَّبِيِّـۧنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا ﴿٤٠﴾

Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kõme.

Al-Ahzab 33:40Karanta a cikin Alƙur'ani

وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا رَحۡمَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ ﴿١٠٧﴾

Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai.

Al-Anbiya 21:107Karanta a cikin Alƙur'ani

وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا كَآفَّةٗ لِّلنَّاسِ بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ ﴿٢٨﴾

Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.

Saba 34:28Karanta a cikin Alƙur'ani

وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٖ ﴿٤﴾

Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.

Al-Qalam 68:4Karanta a cikin Alƙur'ani

Daga Sunna

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kaɗai an aikoni ne dan in cika manyan ɗabi'u».

Bukhari a cikin Al-Adab Al-Mufrad da Ahmad da Baihaki suka ruwaito shi Hasan ne HadeethEnc.com
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agate shi - ya bada labarin cewa kaɗai shi Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya aikoshi ne dan ya cika kyawawan ɗabi'u; inda aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan cika abinda ya gabace shi na manzanni, kuma mai cika kyawawan ɗabi'un larabawa, sun kasance suna son alheri kuma suna ƙin sharri, masu mutunci ne da karamci da gabata; sai aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan cike abubuwan da suka gaza da ke cikin ɗabi'unsu, kamar alfaharinsu da nasabobi, da girman kai, da wulaƙanta talaka da wanin hakan.

Daga Umar Ibnu Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce: Bawan Allah kuma ManzonSa".

Bukhari ne ya rawaito shi Ingantacce ne HadeethEnc.com
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana hani daga wuce gona da iri da kuma ketare iyakar shari'a a yabonsa da kuma siffanta shi da siffofin Allah - Madaukakin sarki - da kuma ayyukansa wadanda suka kebanta da shi, ko cewa shi yana sanin gaibu, ko a kira shi tare da Allah, kamar yadda Nasara suka aikata tare da Isa Dan Maryam - amincin Allah ya tabbata a gare shi -. Sannan ya bayyana cewa shi bawa ne daga bayin Allah, ya kuma yi umarni da mu fada game da shi: Bawan Allah kuma ManzonSa.

Duk darussa