Last ten ayahs of Al-Kahf

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

ٱلَّذِينَ كَانَتۡ أَعۡيُنُهُمۡ فِي غِطَآءٍ عَن ذِكۡرِي وَكَانُواْ لَا يَسۡتَطِيعُونَ سَمۡعًا ١٠١

Alladhīna kānat a'yunuhum fī ghitā'in 'an dhikrī wakānū lā yastatī'ūna sam'ā

Waɗanda idãnunsu suka kasance a cikin rufi daga tunã1 Ni, kuma sun kasance bã su iya saurãrãwa.

Bayanan ƙasa

1 Zikr- tunãwa- shi ne Alƙur'ãni da abin da ya tãra na ibãda da sauran ma'ãmalõli, dukansu ibãda ne, matuƙar an bi abin da Allah Ya ajiye a cikinsu na hukunce-hukunce.

أَفَحَسِبَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَن يَتَّخِذُواْ عِبَادِي مِن دُونِيٓ أَوۡلِيَآءَۚ إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا جَهَنَّمَ لِلۡكَٰفِرِينَ نُزُلٗا ١٠٢

Afahasibal-ladhīna kafarū an yattakhidhū 'ibādī min dūnī awliyā'a innā a'tadnā jahannama lil-kāfirīna nuzulā

Shin fa, waɗanda suka kãfirta sun yi zaton (daidai ne) su riƙi waɗansu bãyĩNa1, majiɓinta baic iNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai.

Bayanan ƙasa

1 Waɗanda suka riƙi wasu bãyin Allah, sunã bauta musu, kamar Yahũdu mãsu bauta wa Uzairu da Nasãra mãsu bautawa Ĩsã da wasu Musulmi mãsu bauta wa wasu sãlihai sun zama kãfirai. Ma'anar bautawar shi ne su ƙirƙira wasu hukunce-hakunce kõ wasu sifõfi waɗanda suka sãɓa wa maganar Alƙur'ãni da Hadĩsi, sa'an nan su jingina su zuwa ga waɗannan bãyin Allah, su bi su da su.

قُلۡ هَلۡ نُنَبِّئُكُم بِٱلۡأَخۡسَرِينَ أَعۡمَٰلًا ١٠٣

Qul hal nunabbi'ukum bil-akhsarīna a'mālā

Ka ce: "Kõ mu gaya muku game da mafĩfita hasãra ga ayyuka?"

ٱلَّذِينَ ضَلَّ سَعۡيُهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُمۡ يَحۡسَبُونَ أَنَّهُمۡ يُحۡسِنُونَ صُنۡعًا ١٠٤

Alladhīna dalla sa'yuhum fil-hayawātid-dunyā wahum yahsabūna annahum yuhsinūna sun'ā

"Waɗanda aikinsu ya ɓace a cikin rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sunã zaton lalle ne sũ, sunã kyautata, (abin da suke gani) aikin ƙwarai?"

أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ وَلِقَآئِهِۦ فَحَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فَلَا نُقِيمُ لَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَزۡنٗا ١٠٥

Ulā'ikal-ladhīna kafarū bi'āyāti rabbihim waliqā'ihī fahabitat a'māluhum falā nuqīmu lahum yawmal-qiyāmati waznā

Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Ubangijinsu, da kuma haɗuwa da Shi, sai ayyukansu suka ɓãci. Sabõda haka bã zã Mu tsayar musu da awo1 ba a Rãnar ¡iyãma.

Bayanan ƙasa

1 Watau ko aunawa bã zã a yi ba balle a daidaita ma'auni.

ذَٰلِكَ جَزَآؤُهُمۡ جَهَنَّمُ بِمَا كَفَرُواْ وَٱتَّخَذُوٓاْ ءَايَٰتِي وَرُسُلِي هُزُوًا ١٠٦

Dhālika jazā'uhum jahannamu bimā kafarū wattakhadhū āyātī warusulī huzuwā

Wancan ne sakamakonsu shĩ ne Jahannama, sabõda kãfircinsu, kuma suka riƙi ãyõyi Na da Manzanni Na abin izgili.

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ كَانَتۡ لَهُمۡ جَنَّٰتُ ٱلۡفِرۡدَوۡسِ نُزُلًا ١٠٧

Innal-ladhīna āmanū wa'amilus-sālihāti kānat lahum jannātul-firdawsi nuzulā

Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Aljannar Firdausi ta kasance ita ce liyãfa a gare su.

خَٰلِدِينَ فِيهَا لَا يَبۡغُونَ عَنۡهَا حِوَلٗا ١٠٨

Khālidīna fīhā lā yabghūna 'anhā hiwalā

Suna madawwama a cikinta, bã su nẽman makarkata daga barinta.

قُل لَّوۡ كَانَ ٱلۡبَحۡرُ مِدَادٗا لِّكَلِمَٰتِ رَبِّي لَنَفِدَ ٱلۡبَحۡرُ قَبۡلَ أَن تَنفَدَ كَلِمَٰتُ رَبِّي وَلَوۡ جِئۡنَا بِمِثۡلِهِۦ مَدَدٗا ١٠٩

Qul law kānal-bahru midādal likalimāti rabbī lanafidal-bahru qabla an tanfada kalimātu rabbī walaw ji'nā bimithlihī madadā

Ka ce: "Dã tẽku1 ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari."

Bayanan ƙasa

1 Ma'anar ãyar nan ita ce Allah ne Mafi sani. llmin Allah bã shi da iyãka, kõ kalmõmin da suka ɗauki ma'anõninsa, bã zã a iya rubuta su ba, balle ma'anõnin da ke cikinsu. Sabõda haka abin da ke hankali a mutum, shĩ ne ya yi aiki da ɗan ilmin da Allah Ya umurce shi da aiki dashi. Idan ya nemi ya wuce nan, to, ya halakar da kansa dõmin bai san inda zai fãɗa ba. Wannan ilmin shi ne sharĩ'a da aiki da ita.

قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَمَن كَانَ يَرۡجُواْ لِقَآءَ رَبِّهِۦ فَلۡيَعۡمَلۡ عَمَلٗا صَٰلِحٗا وَلَا يُشۡرِكۡ بِعِبَادَةِ رَبِّهِۦٓ أَحَدَۢا ١١٠

Qul innamā ana basharum mithlukum yūhā ilayya annamā ilāhukum ilāhun wāhidun faman kāna yarjū liqā'a rabbihī falya'mal 'amalan sālihan walā yushrik bi'ibādati rabbihī ahadā

Ka ce: "Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa."1

Bayanan ƙasa

1 Wannan ãya, a dunƙule, ta tãra dukan abin da ke cikin sũrar. Allah Ya shiryar da mu, ga kaɗaita shi ga ibãda, da yin ibadar, kuma yadda Allah Ya ce a yĩ ta, ga mai tsammãnin rabo a Lãhira. Wanda ba ya tsammãnin rabon Lãhira, ya tsaya ga dũniya mai gushħwa da sauri, to, shĩ bã a shiga batunsa ba.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Karanta Surat Al-Kahf gaba ɗaya

Tambayoyi

Ina Last ten ayahs of Al-Kahf take a cikin Alƙur'ani?

Last ten ayahs of Al-Kahf tana cikin Surat Al-Kahf, 18:101-110.