Surat Al-An'am, aya ta 52

6:52

وَلَا تَطۡرُدِ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ رَبَّهُم بِٱلۡغَدَوٰةِ وَٱلۡعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجۡهَهُۥۖ مَا عَلَيۡكَ مِنۡ حِسَابِهِم مِّن شَيۡءٖ وَمَا مِنۡ حِسَابِكَ عَلَيۡهِم مِّن شَيۡءٖ فَتَطۡرُدَهُمۡ فَتَكُونَ مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ ٥٢

Walā tatrudil-ladhīna yad'ūna rabbahum bil-ghadawāti wal-'ashiyyi yurīdūna wajhahū mā 'alayka min hisābihim min shay'in wamā min hisābika 'alayhim min shay'in fatatrudahum fatakūna minaz-zālimīn

Kuma kada ka kõri waɗanda1 suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai.

Bayanan ƙasa

1 Musulunci addinin Allah ne, wanda yake faƙĩrin dũkiya da mawãdãcinta, duka ɗaya suke a gare shi. Sabõda haka wanda duka ya rigayi wani a cikinsu, to, bã za a kõre shi ba dõmin ɗayan ya shiga. Allah ĩmãni Yake so, kõ daga wãne irin mutum yake, bã Ya bukãtar dũkiya.