Tambayoyin da mutane ke yi

Darasi 5 cikin 11

Waɗanne hakkoki mata suke da su a Musulunci?

Amsa a taƙaice

A Musulunci, maza da mata sun fito daga rai ɗaya kuma daidai suke a wurin Allah: duk namiji ko mace da ya yi imani kuma ya aikata alheri za a ba shi rayuwa mai daɗi da cikakken lada. Musulunci ya bai wa mata hakkin mallakar dukiya, neman kuɗi, gado, karɓar sadaki (mahr) da kuma neman yardarsu kafin aure, kuma ya umarci maza su kyautata wa mata. Annabi bai taɓa dukan mace ba.

Qabas ne ya rubuta ta, kuma an duba ta da Al-Mukhtasar fi Tafsir al-Qur'an al-Karim, Tafsirin Ibn Kathir da bayanan HadeethEnc.com.

Daga Alƙur'ani

يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ وَخَلَقَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا وَبَثَّ مِنۡهُمَا رِجَالٗا كَثِيرٗا وَنِسَآءٗۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِي تَسَآءَلُونَ بِهِۦ وَٱلۡأَرۡحَامَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَيۡكُمۡ رَقِيبٗا ﴿١﴾

Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi, da kuma zumunta. Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.

An-Nisa 4:1Karanta a cikin Alƙur'ani

مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ ﴿٩٧﴾

Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.

An-Nahl 16:97Karanta a cikin Alƙur'ani

إِنَّ ٱلۡمُسۡلِمِينَ وَٱلۡمُسۡلِمَٰتِ وَٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ وَٱلۡقَٰنِتِينَ وَٱلۡقَٰنِتَٰتِ وَٱلصَّٰدِقِينَ وَٱلصَّٰدِقَٰتِ وَٱلصَّٰبِرِينَ وَٱلصَّٰبِرَٰتِ وَٱلۡخَٰشِعِينَ وَٱلۡخَٰشِعَٰتِ وَٱلۡمُتَصَدِّقِينَ وَٱلۡمُتَصَدِّقَٰتِ وَٱلصَّٰٓئِمِينَ وَٱلصَّٰٓئِمَٰتِ وَٱلۡحَٰفِظِينَ فُرُوجَهُمۡ وَٱلۡحَٰفِظَٰتِ وَٱلذَّٰكِرِينَ ٱللَّهَ كَثِيرٗا وَٱلذَّٰكِرَٰتِ أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمٗا ﴿٣٥﴾

Lalle, Musulmi maza da Musulmi mãtã da muminai maza da muminai mãtã, da mãsu tawãli'u maza da mãsu tawãlĩu mãtãda mãsu gaskiya maza da mãsu gaskiya mãtã, da mãsu haƙuri maza da mãsu haƙuri mãtã, da mãsu tsõron Allah maza da mãsu tsõron Allah mãtã, da mãsu sadaka maza da mãsu sadaka mãtã, da mãsu azumi maza da mãsu azumi mãtã da mãsu tsare farjõjinsu maza da mãsu tsare farjõjinsu mãtã, da mãsu ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin wata gãfara da wani sakamako mai girma.

Al-Ahzab 33:35Karanta a cikin Alƙur'ani

لِّلرِّجَالِ نَصِيبٞ مِّمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَ وَلِلنِّسَآءِ نَصِيبٞ مِّمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَ مِمَّا قَلَّ مِنۡهُ أَوۡ كَثُرَۚ نَصِيبٗا مَّفۡرُوضٗا ﴿٧﴾

Maza suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mãtã suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya ƙaranta daga gare shi kõ kuwa ya yi yawa, rabo yankakke.

An-Nisa 4:7Karanta a cikin Alƙur'ani

وَءَاتُواْ ٱلنِّسَآءَ صَدُقَٰتِهِنَّ نِحۡلَةٗۚ فَإِن طِبۡنَ لَكُمۡ عَن شَيۡءٖ مِّنۡهُ نَفۡسٗا فَكُلُوهُ هَنِيٓـٔٗا مَّرِيٓـٔٗا ﴿٤﴾

Kuma ku bai wa mãtã sadãkõkĩnsu da sauƙin bãyarwa. Sa'an nan idan suka yãfe muku wani abu daga gare shi, da dãɗin rai, to, ku ci shi da jin dãɗi da sauƙin haɗiya.

An-Nisa 4:4Karanta a cikin Alƙur'ani

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَحِلُّ لَكُمۡ أَن تَرِثُواْ ٱلنِّسَآءَ كَرۡهٗاۖ وَلَا تَعۡضُلُوهُنَّ لِتَذۡهَبُواْ بِبَعۡضِ مَآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَعَاشِرُوهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ فَإِن كَرِهۡتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰٓ أَن تَكۡرَهُواْ شَيۡـٔٗا وَيَجۡعَلَ ٱللَّهُ فِيهِ خَيۡرٗا كَثِيرٗا ﴿١٩﴾

Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka zo da wata alfãsha bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi wani abu alhãli kuwa Allah Ya sanya wani alhẽri mai yawaa cikinsa.

An-Nisa 4:19Karanta a cikin Alƙur'ani

Daga Sunna

Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta ce: Wata mata ta zo a tare da ita akwai 'ya'yanta biyu mata, bata samu komai awurina ba banda wani dabino ɗaya, sai na bata shi sai ta raba shi tsakanin 'ya'yan nata mata biyu, sannan ta tashi sai ta fita, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo sai ta zantar da shi, sai ya ce: «‌Wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗannan 'ya'ya matan, sai ya kyautata musu, zasu zama kariya gare shi daga wuta».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Ingantacce ne HadeethEnc.com
Bayani

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa wata mata ta zo mata a tare da ita akwai 'ya'yanta biyu mata tana tambayarta ta bata abinda zata ci, Nana A'isha bata samu komai a wurinta ba banda dabino ɗaya, sai ta bata shi sai matar ta raba dabinon tsakanin 'ya'yan nata mata biyu ba ta ci komai daga gare shi ba, sannan ta tashi sai ta fita, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga (gida) sai Nana A'isha ta zantar da shi, sai ya ce: Duk wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗanan 'ya'ya matan, sai ya kyauata musu ya tarbiyantar da su ya ciyar da su ya shayar da su ya tufatar da su kuma ya yi haƙuri akan haka, zasu zama sutura da kariya gare shi daga wuta.

An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- zuwa ga Annabi: "Annabi SAW bai taba dukan wani abu ba da Hannunsa, ko Wata Mata Ko Baron gida, sai fagen Jahadin daukaka Addinin Allah, sai dai in an keta Hurumin Allah, Sai yayi Hukunci sabida Allah Madaukaki."

Muslim ne ya rawaito shi Ingantacce ne HadeethEnc.com

Duk darussa