Surat At-Tawbah, aya ta 118

9:118

وَعَلَى ٱلثَّلَٰثَةِ ٱلَّذِينَ خُلِّفُواْ حَتَّىٰٓ إِذَا ضَاقَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَرۡضُ بِمَا رَحُبَتۡ وَضَاقَتۡ عَلَيۡهِمۡ أَنفُسُهُمۡ وَظَنُّوٓاْ أَن لَّا مَلۡجَأَ مِنَ ٱللَّهِ إِلَّآ إِلَيۡهِ ثُمَّ تَابَ عَلَيۡهِمۡ لِيَتُوبُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ ١١٨

Wa'alath-thalāthatil-ladhīna khullifū hattā idhā dāqat 'alayhimul-ardu bimā rahubat wadāqat 'alayhim anfusuhum wazannū al lā malja'a minallāhi illā ilayhi thumma tāba 'alayhim liyatūbū innallāha huwat-tawwābur-rahīm

Kuma (Allah) Yã karɓi tũba a kan ukun1 nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rãyukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton bãbu wata mafakã daga Allah fãce (kõmãwa) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tũbarsu, dõmin su tabbata a kan tũba. Lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.

Bayanan ƙasa

1 Sũ mutãne uku waɗan da aka jinkintar da al'amarinsu, a ãyã ta l06, sũ ne Ka'abu bn Mãliki da Marãratu bn Rabĩ'a el Umary, da Hilãlu bn Umaiya el Wãƙify. Sun ƙi fita, bã da wani uzuri ba, kuma a lõkacin da Annabi ya kõmo daga Tabũka, waɗanda ba su fita ba suka tafi suka faɗi uzurõrinsu na rashin fitã. Annabi ya karɓa musu Kuma ya nema musu gãfara. Amma su ukun, suka faɗi gaskiya cewa sun zauna ne bã dõmin munãfunci ba, sai dai abin yã kasance haka kawai bã da wani uzuri ba. To, Annabi ya ce su dãkata, sai abin da Allah Ya ce a kansu. Aka hana kõwa ya yi musu magana a cikin Madĩna, har mãtansu na aure. Suka yi kwãna hamsin a cikin matsuwa, sa'an nan Allah Ya sauko da tũbarsu.