Surat Al-Infitar الإنفطار

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتۡ ١

Idhas-samā'unfatarat

Idan sama ta tsãge.

وَإِذَا ٱلۡكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتۡ ٢

Wa idhal-kawākibuntatharat

Kuma idan taurãri suka wãtse.

وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ فُجِّرَتۡ ٣

Wa idhal-bihāru fujjirat

Kuma idan tẽkuna aka facce su.

وَإِذَا ٱلۡقُبُورُ بُعۡثِرَتۡ ٤

Wa idhal-qubūru bu'thirat

Kuma idan kaburbura aka tõne su.

عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّا قَدَّمَتۡ وَأَخَّرَتۡ ٥

'Alimat nafsum mā qaddamat wa akkharat

Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.

يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡإِنسَٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلۡكَرِيمِ ٦

Yā'ayyuhal-insānu mā gharraka birabbikal-karīm

Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci.

ٱلَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ ٧

Alladhī khalaqaka fasawwāka fa'adalak

Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.

فِيٓ أَيِّ صُورَةٖ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ ٨

Fī ayyi sūratim mā shā'a rakkabak

A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.

كَلَّا بَلۡ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ ٩

Kallā bal tukaddhibūna bid-dīn

A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!

وَإِنَّ عَلَيۡكُمۡ لَحَٰفِظِينَ ١٠

Wa inna 'alaykum lahāfizīn

Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.

كِرَامٗا كَٰتِبِينَ ١١

Kirāman kātibīn

Mãsu daraja, marubũta.

يَعۡلَمُونَ مَا تَفۡعَلُونَ ١٢

Ya'lamūna mā taf'alūn

Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.

إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٖ ١٣

Innal-abrāra lafī na'īm

Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.

وَإِنَّ ٱلۡفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٖ ١٤

Wa innal-fujjāra lafī jahīm

Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.

يَصۡلَوۡنَهَا يَوۡمَ ٱلدِّينِ ١٥

Yaslawnahā yawmad-dīn

Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.

وَمَا هُمۡ عَنۡهَا بِغَآئِبِينَ ١٦

Wamā hum 'anhā bighā'ibīn

Bã zã su faku daga gare ta ba.

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ ١٧

Wamā adrāka mā yawmud-dīn

Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako?

ثُمَّ مَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ ١٨

Thumma mā adrāka mā yawmud-dīn

Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?

يَوۡمَ لَا تَمۡلِكُ نَفۡسٞ لِّنَفۡسٖ شَيۡـٔٗاۖ وَٱلۡأَمۡرُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ ١٩

Yawma lā tamliku nafsul linafsin shay'an wal-amru yawma'idhi lillāh

Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Tambayoyi

Ayoyi nawa ne a Surat Al-Infitar?

Surat Al-Infitar tana da ayoyi 19. Ita ce sura ta 82 a cikin Alƙur'ani.

Shin Surat Al-Infitar Makkiya ce ko Madaniya?

Surat Al-Infitar sura Makkiya ce.

A wane juz'i Surat Al-Infitar take?

Surat Al-Infitar tana cikin juz'i 30.

Zan iya sauraron Surat Al-Infitar?

Eh. Danna Kunna a saman wannan shafi, ko ka fara daga kowace aya. Manhajar Qabas kuma tana ba ka damar sauke ta don sauraro ba tare da intanet ba.