أَوَلَمَّآ أَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةٞ قَدۡ أَصَبۡتُم مِّثۡلَيۡهَا قُلۡتُمۡ أَنَّىٰ هَٰذَاۖ قُلۡ هُوَ مِنۡ عِندِ أَنفُسِكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ ١٦٥
Awalammā asābatkum musībatun qad asabtum mithlayhā qultum annā hādhā qul huwa min 'indi anfusikum innallāha 'alā kulli shay'in qadīr
Shin kuma a lõkacin1 da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: "Daga ina wannan yake?" Ka ce: "Daga wurin rãyukanku2 yake." Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne.
Bayanan ƙasa
1 Duk masĩfar da ta sãme ku, tõ, ku ne kuka jãwo wa kanku ita da wani laifi na sãɓãwa umurnin Allah. Kuma kãmin masĩfa guda ta sãme ku, to, alheri biyu sun sãme ku.
2 Kowace irin masĩfa ta sãmi mutum, to, shĩ ne ya yi sababinta a kansa. Kuma yã kamata ya yi bincike ya gãne sababin, a inda ya jãhilce shi. Kuma duk da haka kãmin masĩfa guda ta sãme shi, ya sãmi ni'ima biyu kõ fiye da haka.