قُلۡ مَن كَانَ عَدُوّٗا لِّـجِبۡرِيلَ فَإِنَّهُۥ نَزَّلَهُۥ عَلَىٰ قَلۡبِكَ بِإِذۡنِ ٱللَّهِ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَهُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ ٩٧
Qul man kāna 'aduwwal lijibrīla fa innahū nazzalahū 'alā qalbika bi idhnillāhi musaddiqal limā bayna yadayhi wahudan wabushrā lil-mu'minīn
Ka ce: Wanda ya1 kasance maƙiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a kan zũciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatãwa ga abin da yake gaba gare shi, kuma da shiriya da bishãra ga mũminai.
Bayanan ƙasa
1 Mai ƙin gaskiya kullum yanã neman dalĩlin da zai kãma ya zama wani uzuri a gare shi wajen ƙin aiki da gaskiyar. Yahũdu sunã cewa bã su son Jibirila dõmin shi ne ake aikõwa da azãba, yã halakar da Ãdãwa da Samũdãwa da mutãnen Luɗu, sunã nufin su ƙi abin da ya kãwo wa Annabi na Alƙur'ãni.