Tambayoyin da mutane ke yi

Darasi 2 cikin 11

Me Musulunci ke cewa game da Maryamu, mahaifiyar Annabi Isa?

Amsa a taƙaice

Maryamu, mahaifiyar Annabi Isa, tana ɗaya daga cikin mata mafi daraja a Musulunci. Alƙur'ani ya ce Allah ya zaɓe ta, ya tsarkake ta, kuma ya zaɓe ta a kan matan talikai, wanda malamai da yawa suka bayyana da matan zamaninta, kuma akwai sura cikakkiya ta Alƙur'ani da aka sanya wa sunanta. Ta haifi Annabi Isa tana budurwa, ta hanyar mu'ujiza daga Allah. Annabi ya ambace ta cikin 'yan mata kaɗan da suka kai ga kamala.

Qabas ne ya rubuta ta, kuma an duba ta da Al-Mukhtasar fi Tafsir al-Qur'an al-Karim, Tafsirin Ibn Kathir da bayanan HadeethEnc.com.

Daga Alƙur'ani

وَإِذۡ قَالَتِ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يَٰمَرۡيَمُ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰكِ وَطَهَّرَكِ وَٱصۡطَفَىٰكِ عَلَىٰ نِسَآءِ ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴿٤٢﴾ يَٰمَرۡيَمُ ٱقۡنُتِي لِرَبِّكِ وَٱسۡجُدِي وَٱرۡكَعِي مَعَ ٱلرَّٰكِعِينَ ﴿٤٣﴾

Kuma a lõkacin da malã'iku suka ce: "Ya Maryamu! Lalle ne, Allah Ya zãɓe ki, kuma Ya tsarkake ki, kuma Ya zaɓe ki a kan mãtan tãlikai." "Yã Maryamu! Ki yi ƙanƙan da kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujada, kuma ki yi rukũ'i tãre da mãsu rukũ'i."

Al-Imran 3:42-43Karanta a cikin Alƙur'ani

وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَرۡيَمَ إِذِ ٱنتَبَذَتۡ مِنۡ أَهۡلِهَا مَكَانٗا شَرۡقِيّٗا ﴿١٦﴾ فَٱتَّخَذَتۡ مِن دُونِهِمۡ حِجَابٗا فَأَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَرٗا سَوِيّٗا ﴿١٧﴾ قَالَتۡ إِنِّيٓ أَعُوذُ بِٱلرَّحۡمَٰنِ مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيّٗا ﴿١٨﴾ قَالَ إِنَّمَآ أَنَا۠ رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَٰمٗا زَكِيّٗا ﴿١٩﴾ قَالَتۡ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞ وَلَمۡ أَكُ بَغِيّٗا ﴿٢٠﴾ قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞۖ وَلِنَجۡعَلَهُۥٓ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِ وَرَحۡمَةٗ مِّنَّاۚ وَكَانَ أَمۡرٗا مَّقۡضِيّٗا ﴿٢١﴾

Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas. Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci. Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!" Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki." Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?" Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce."

Maryam 19:16-21Karanta a cikin Alƙur'ani

وَمَرۡيَمَ ٱبۡنَتَ عِمۡرَٰنَ ٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهِ مِن رُّوحِنَا وَصَدَّقَتۡ بِكَلِمَٰتِ رَبِّهَا وَكُتُبِهِۦ وَكَانَتۡ مِنَ ٱلۡقَٰنِتِينَ ﴿١٢﴾

Da Maryama ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da Littattafan Sa alhãli kuwa ta kasance daga mãsu tawãli'u.

At-Tahrim 66:12Karanta a cikin Alƙur'ani

Daga Sunna

An karvo daga Abu Musa -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Mutane da yawa su cika Mutane, amma daga cikin Mata babu waxanda suka cika sai Asiya Matar fir'auna, da Maryam Bint Imran, kuma lallai cewa Falalar Aisha akan sauran Mata kamar Falalar Al-tharid kan sauran abinci"

Bukhari da Muslim suka Rawaito shi Ingantacce ne HadeethEnc.com
Bayani

Lallai waxanda suka kai Matsayin cika a cikin Falalar Addini da Halayya daga cikin Maza akwai da yawa daga cikinsu akwai wanda yakai Matakin cika ta Al-ada Kamar Malamai da Mutanen kirki da Waliyyai, akwai daga cikin su akwai wanda ya wuce matakin cika kamar Annabwa, amma Matan da suka cika su ne kaxan kwarai kuma waxanda suke gaba Asiya Matar Fir'auna ita Asiya Bint Muzahim wacce Allah ya buga Misali da ita a cikin cikar Imani, sai ya ce: "Kuma Allah ya buga Misali ga waxanda sukai Imani Matar fir'auna" Saboda tayi Imani da Annabi Musa lokacin da yai Nasara kan Masu Sihirin fir'auna, kuma yayin da fir'auna ya san ta yi Imani sai yayi mata Azaba Mai tsanani har zuwa lokacin da ta Mutu tana riqe da Imaninta, amma ta biyu ita ce Maryam Bint Imran wacce Allah ya buga Misali wajen kare kanta, da kuma cikar Ibadarta, sannan SAW ya ce: "Kuma falalar Aisha kan sauran Mata kamar fifikon Tharid kan sauran Abinci" Tharid shi ne mafi daxin abincin Larabawa kuma anayinsa ne da gurasa da kuma nama, to Aisha a Fifikon ta kan Mata kamar Fifikon wancan Tharid xin wanda shi ne mafi daxin abinci kan Sauran Abinci

An kavo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce naji Manzon Allah SAW yana cewa: "Babu wani da za'a haifa a cikin "yan Adam face sai Shaioxan ya shafeshi lokacin da za'a haife shi, sai ya faxo yana kuka daga shafar shaixan sai Maryam kawai da Xanta"

Bukhari da Muslim suka Rawaito shi Ingantacce ne HadeethEnc.com
Bayani

Kowane Jariri ana haifar sa sai Shaixan zai sokeshi a kuivinsa, sai ya kwalla kuka yayi Ihu bayan haihuwarsa kaxan saboda wannan zungurin na Shaxan, sai Maryam da Xanta Isa -Amincin Allah a garesu- saboda Allah ya kare su a lokacin haihuwarsu saboda Addu'ar Mahaifiyar Maryam lokacin da ta ce: "Kuma ni ina ne mata tsari da Zuriyarta daga Shaixan tsinanne" sai Allah ya amsa Addu'ar Mahaifiyar Maryam, sai ya kare Maryam da Xanta Isa daga zungurar Shaixan korarre ga barin rahamar Allah, Kuma babu wata Zariya ga Maryam in ba Isa -Amincin Allah a gare shi- kuma wannan Shafar ko sukar daga shaxan na haqiqa ne, kuma ba wai Ma'anarsa Kwaxayin Shaixan ba ne na vatar Xan Adam ba Kamar yadda Mu'atazilawa suke faxa, kuma ya wajaba ayi imani da hakan kan Haqiqaninsa, kamar yadda haka yake a Aqidar Ahlussunnah da jama'a

Duk darussa