Rabbana afrigh 'alayna sabra

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

وَلَمَّا بَرَزُواْ لِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦ قَالُواْ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَثَبِّتۡ أَقۡدَامَنَا وَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ ٢٥٠

Walammā barazū lijālūta wajunūdihī qālū rabbanā afrigh 'alaynā sabran wathabbit aqdāmanā wansurnā 'alal-qawmil-kāfirīn

Kuma a lõkacin da suka1 bayyana ga Jãlũta da rundunoninsa, suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu kuma Ka tabbatar da sãwayenmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."

Bayanan ƙasa

1 Dãwũdu ɗan Ãisha ya gãji annabcin Shamwĩlu da mulkin Ɗãlũta, shĩ ne ya fãra haɗã su a cikin Bani lsrã'ila bãyansa sai ɗansa Sulaimãn ya gãje shi haka nan. Yawan mutãnen Ɗãlũta da suka yi yãƙi kamar adadin mutãnen Badar ne waɗanda suka yi yãƙi tãre da Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Karanta Surat Al-Baqarah gaba ɗaya

Tambayoyi

Ina Rabbana afrigh 'alayna sabra take a cikin Alƙur'ani?

Rabbana afrigh 'alayna sabra tana cikin Surat Al-Baqarah, 2:250.