Inna fi khalqis-samawati

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

إِنَّ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ ١٩٠

Inna fī khalqis-samāwāti wal-ardi wakhtilāfil-layli wan-nahāri la'āyātil li ulil-albāb

Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali.

ٱلَّذِينَ يَذۡكُرُونَ ٱللَّهَ قِيَٰمٗا وَقُعُودٗا وَعَلَىٰ جُنُوبِهِمۡ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ رَبَّنَا مَا خَلَقۡتَ هَٰذَا بَٰطِلٗا سُبۡحَٰنَكَ فَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ ١٩١

Alladhīna yadhkurūnallāha qiyāman waqu'ūdan wa'alā junūbihim wayatafakkarūna fī khalqis-samāwāti wal-ardi rabbanā mā khalaqta hādhā bātilan subhānaka faqinā 'adhāban-nār

Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. TsarkinKa! Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta.

رَبَّنَآ إِنَّكَ مَن تُدۡخِلِ ٱلنَّارَ فَقَدۡ أَخۡزَيۡتَهُۥۖ وَمَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٖ ١٩٢

Rabbanā innaka man tudkhilin-nāra faqad akhzaytahū wamā liz-zālimīna min ansār

"Ya Ubangijinmu! Lalle ne Kai, wanda Ka shigar a cikin wuta to, haƙĩƙa, Ka tozarta shi kuma bãbu wasu mataimaka ga Azzãlumai.

رَّبَّنَآ إِنَّنَا سَمِعۡنَا مُنَادِيٗا يُنَادِي لِلۡإِيمَٰنِ أَنۡ ءَامِنُواْ بِرَبِّكُمۡ فَـَٔامَنَّاۚ رَبَّنَا فَٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرۡ عَنَّا سَيِّـَٔاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ ٱلۡأَبۡرَارِ ١٩٣

Rrabbanā innanā sami'nā munādiyan yunādī lil-īmāni an āminū birabbikum fa'āmannā rabbanā faghfir lanā dhunūbanā wakaffir 'annā sayyi'ātinā watawaffanā ma'al-abrār

"Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Sabõda haka Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rãyukanmu tãre da mutãnen kirki.

رَبَّنَا وَءَاتِنَا مَا وَعَدتَّنَا عَلَىٰ رُسُلِكَ وَلَا تُخۡزِنَا يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ إِنَّكَ لَا تُخۡلِفُ ٱلۡمِيعَادَ ١٩٤

Rabbanā wa ātinā mā wa'attanā 'alā rusulika walā tukhzinā yawmal-qiyāmati innaka lā tukhliful-mī'ād

"Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta mu a Rãnar ¡iyãma. Lalle ne Kai, bã Ka sãɓãwar Alkawari."

فَٱسۡتَجَابَ لَهُمۡ رَبُّهُمۡ أَنِّي لَآ أُضِيعُ عَمَلَ عَٰمِلٖ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰۖ بَعۡضُكُم مِّنۢ بَعۡضٖۖ فَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ وَأُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَأُوذُواْ فِي سَبِيلِي وَقَٰتَلُواْ وَقُتِلُواْ لَأُكَفِّرَنَّ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَأُدۡخِلَنَّهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ ثَوَابٗا مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلثَّوَابِ ١٩٥

Fastajāba lahum rabbuhum annī lā udī'u 'amala 'āmilim minkum min dhakarin aw unthā ba'dukum mim ba'din falladhīna hājarū wa ukhrijū min diyārihim wa ūdhū fī sabīlī waqātalū waqutilū la ukaffiranna 'anhum sayyi'ātihim wala'udkhilannahum jannātin tajrī min tahtihal-anhāru thawābam min 'indillāhi wallāhu 'indahū husnuth-thawāb

Sabõda haka Ubangijinsu Ya karɓa musu cẽwa, "Lallene Nĩ bã zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sãshenku daga sãshe. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidãjensu, kuma aka cũtar da su a cikin hanyaTa, kuma suka yi yãƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musumiyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙoramu ke gudãna daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako.

لَا يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ ١٩٦

Lā yaghurrannaka taqallubul-ladhīna kafarū fil-bilād

Kada jujjuyawar waɗanda suka kãfirta a cikin garũruwa ta rũɗe ka.

مَتَٰعٞ قَلِيلٞ ثُمَّ مَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ ١٩٧

Matā'un qalīlun thumma ma'wāhum jahannamu wabi'sal-mihād

Jin dãɗi ne kaɗan sa'an nan makõmarsu Jahannama ce, kuma tir da shimfiɗa ita!

لَٰكِنِ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ رَبَّهُمۡ لَهُمۡ جَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا نُزُلٗا مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۗ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّلۡأَبۡرَارِ ١٩٨

Lākinil-ladhīnat-taqaw rabbahum lahum jannātun tajrī min tahtihal-anhāru khālidīna fīhā nuzulam min 'indillāhi wamā 'indallāhi khayrul lil-abrār

Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa sunã da Gidãjen Aljanna (waɗabda) ƙoramu ke gudãna a ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu, a kan, liyãfa daga wurin Allah, kuma abin da ke wurin Allah ne mafi alhẽri ga barrantattu.

وَإِنَّ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَمَن يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُمۡ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِمۡ خَٰشِعِينَ لِلَّهِ لَا يَشۡتَرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ ثَمَنٗا قَلِيلًاۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ ١٩٩

Wa inna min ahlil-kitābi laman yu'minu billāhi wamā unzila ilaykum wamā unzila ilayhim khāshi'īna lillāhi lā yashtarūna bi'āyātillāhi thamanan qalīlan ulā'ika lahum ajruhum 'inda rabbihim innallāha sarī'ul-hisāb

Kuma lalle ne daga Mutãnen Littãfi1 haƙĩƙa akwai wanda yake yin ĩmãnĩ da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, sunã mãsu tawãlu'i ga Allah, bã su sayen tamani kaɗan da ãyõyin Allah. Waɗannan suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu. Lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako da yawa ne.

Bayanan ƙasa

1 A cikin Mutãnen Littãfi akwai mutãnen ƙwarai na kirki waɗanda hãsada ba ta hana su bin gaskiya ba. Sun sifantu da sifõfin kamãla; watau ba dukkansu ne miyagu ba. Akwai na ƙwarai a cikinsu kamar yadda hãli yake a kõwane tãron mutãne.

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱصۡبِرُواْ وَصَابِرُواْ وَرَابِطُواْ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ ٢٠٠

Yā'ayyuhal-ladhīna āmanusbirū wasābirū warābitū wattaqullāha la'allakum tuflihūn

Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku yi haƙuri kuma ku yi dauriya, kuma ku yi zaman dãko, kuma ku yi taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara.1

Bayanan ƙasa

1 Haƙuri a kan ibãda da ɗaukar wahalõlin sharĩ'a gabãɗaya gwargwadon ĩkon yi. Dauriya a kan abokan gaba; watau kada maƙiya su fi mũminai haƙuri wajen yãƙi daɗaukar wahalõlinsa. Zaman dãko ga taushewar hanyõyin abõkan gaba daga barin shiga ƙasar Musulmi. Bãbu bambanci ga maƙiyi bayyananne da maƙiyi ɓõyayye. Maƙiyi ɓõyayye ya fi aibi dõmin kasancewarsa, zai shiga wuta, amma kasancewarsa maƙiyi bayyananne, zai shiga Aljanna. Taƙawa ita ce bin umuruin Allah da kangewa daga barin haninSa kamar yadda Ya faɗa. Wannan shĩ ne kan ibãda duka bãyan ĩmãni, dõmin haka ya ce kõ zã ku ci nasara, idan kun riƙe waɗannan abũbuwa da kyãwo.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Karanta Surat Al-Imran gaba ɗaya

Tambayoyi

Ina Inna fi khalqis-samawati take a cikin Alƙur'ani?

Inna fi khalqis-samawati tana cikin Surat Al-Imran, 3:190-200.