Surat Al-Ma'idah, aya ta 27

5:27

۞ وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ ٱبۡنَيۡ ءَادَمَ بِٱلۡحَقِّ إِذۡ قَرَّبَا قُرۡبَانٗا فَتُقُبِّلَ مِنۡ أَحَدِهِمَا وَلَمۡ يُتَقَبَّلۡ مِنَ ٱلۡأٓخَرِ قَالَ لَأَقۡتُلَنَّكَۖ قَالَ إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلۡمُتَّقِينَ ٢٧

Watlu 'alayhim naba'abnay ādama bil-haqqi idh qarrabā qurbānan fatuqubbila min ahadihimā walam yutaqabbal minal-ākhari qāla la aqtulannaka qāla innamā yataqabbalullāhu minal-muttaqīn

Kuma karantã musu1 lãbãrin ɗiya biyu2 na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne."

Bayanan ƙasa

1 Ƙuraishawa ko kuwa al'ummarka.

2 Ɗiyan Ãdamu, biyu, Ƙãbĩla da Hãbĩla. Asalin maganar kamar yadda aka ruwaito, mãtar Ãdamu, Hauwa'u, tana haifuwar namiji da mace a kowane ciki, wajen aure sai a shirɓata dõmin bãbu wasu mutãne sai su. Sai Ƙabĩla ya ƙi yarda a bai wa Hãbĩla 'yar'uwarsa, har Ãdam ya sanya su yin baiko da abin sana'arsu. Ƙãbĩla manõmi ne, ya bãyar da munãna daga kãyan nõmansa, shi kuma Hãbĩla ya bãyar da rãgo mai kyau dõmin sana'arsa kiwo ne. Sai wuta ta sauko ta ɗauki rãgon Hãbĩla, alãmar karɓa. Wannan kuwa ya ɗauki Ƙãbĩla ga tunãnin kashe shi. Laifi guda yana sabbaba wasu laifuka mãsu yawa.