Surat Al-Ma'idah, aya ta 103

5:103

مَا جَعَلَ ٱللَّهُ مِنۢ بَحِيرَةٖ وَلَا سَآئِبَةٖ وَلَا وَصِيلَةٖ وَلَا حَامٖ وَلَٰكِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۖ وَأَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ ١٠٣

Mā ja'alallāhu mim bahīratin walā sā'ibatin walā wasīlatin walā hāmin walākinnal-ladhīna kafarū yaftarūna 'alallāhil-kadhiba wa aktharuhum lā ya'qilūn

Kuma Allah bai sanya wata bahĩra ba, kuma haka sã'iba, kuma haka wasĩla, kuma haka hãmi1, amma waɗanda suka kãfirta, su suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma mafi yawansu bã su hankalta.

Bayanan ƙasa

1 Bahĩra da sã'iba da hãmi sunãyen dabbõbi ne waɗanda ake bari dõmin tsãfi Bukhãri yã ruwaito daga Sa'ĩd ɗan Musayyab Ya ce: "Bahĩra ita ce rãƙumar da ake hana nõnõnta dõmin aljannu, bãbu mai tãtsar ta daga mutãne. Sã'iba kuma sunã 'yanta ta dõmin gumãka, ba a ɗaukar kõme a kanta. Kuma wasĩla ita ce rãƙuma budurwa wadda ta fãra haifuwar mace, a ciki na farko, sa'an nan kuma na biyu haka mace. Suna barin ta ga gumãka idan ta sãdar da rãƙuma mata biyu bãbu namiji a tsakãninsu. Hãmi kuwa shĩ ne ƙaton rãƙumi wanda ya yi barbara shekaru sanannu a wurinsu. Idan ya ƙãre sai su bar shi ga gumãka, bã a aza kõme a kansa. Kuma waɗannan dabbõbin duka, mãsu hidimar gumãkan, su ne suke cin su.".