وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَقَفَّيۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِۦ بِٱلرُّسُلِۖ وَءَاتَيۡنَا عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَيَّدۡنَٰهُ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِۗ أَفَكُلَّمَا جَآءَكُمۡ رَسُولُۢ بِمَا لَا تَهۡوَىٰٓ أَنفُسُكُمُ ٱسۡتَكۡبَرۡتُمۡ فَفَرِيقٗا كَذَّبۡتُمۡ وَفَرِيقٗا تَقۡتُلُونَ ٨٧
Walaqad ātaynā mūsal-kitāba waqaffaynā mim ba'dihī bir-rusuli wa ātaynā 'īsabna maryamal-bayyināti wa ayyadnāhu birūhil-qudusi afakullamā jā'akum rasūlu bimā lā tahwā anfusukumustakbartum fafarīqan kaddhabtum wafarīqan taqtulūn
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Munbai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun biyar daga bãyansa da wasu Manzanni, kuma Muka bai wa Ĩsã ɗan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafa shi da Rũhi mai tsarki1. Shinfa, kõ da yaushe wani manzo ya je muku tãre da abin da rãyukanku bã su so, sai ku kangara, wani ɓangare kun ƙaryata, kuma wani ɓangare kuna kashẽwa?
Bayanan ƙasa
1 Rũhul Kuds; watau ran tsarki kõ rai mai tsarki, shi ne Jibirilu, amincin Allah ya tabbata a gare Shi. Ya zauna tãre da Ĩsã inda duk yake sunã tãre. Ãyõyin da aka bai wa Ĩsã sũ ne rãyar da matattu da warkar da kutãre da makãfi da marasa lãfiya. Wannan ya sanya cewa mãsu da'awar bin sa suka fito da aikin maristan, watau asibiti.