Surat Al-Baqarah, aya ta 234

2:234

وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوۡنَ مِنكُمۡ وَيَذَرُونَ أَزۡوَٰجٗا يَتَرَبَّصۡنَ بِأَنفُسِهِنَّ أَرۡبَعَةَ أَشۡهُرٖ وَعَشۡرٗاۖ فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا فَعَلۡنَ فِيٓ أَنفُسِهِنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ ٢٣٤

Walladhīna yutawaffawna minkum wayadharūna azwājan yatarabbasna bi anfusihinna arba'ata ashhurin wa'ashran fa idhā balaghna ajalahunna falā junāha 'alaykum fīmā fa'alna fī anfusihinna bil-ma'rūfi wallāhu bimā ta'malūna khabīr

Kuma waɗanda suke mutuwa1 daga gare ku suna barin mãtan aure, mãtan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwãna goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ãda. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.

Bayanan ƙasa

1 Bayãnin iddar mutuwar maza; mace ɗiya za ta zauna wata huɗu da kwana gõma. Baiwa mãtar aure tanã a kan rabi. Wadda ke shakkar ciki sai ta zauna sai shakka tã ɗebe. Ana takaba watau mai iddar mutuwa ta nisanci ƙawa kõwace iri ce, sai tã ƙãre idda.