Surat Al-Baqarah, aya ta 235

2:235

وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا عَرَّضۡتُم بِهِۦ مِنۡ خِطۡبَةِ ٱلنِّسَآءِ أَوۡ أَكۡنَنتُمۡ فِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمۡ سَتَذۡكُرُونَهُنَّ وَلَٰكِن لَّا تُوَاعِدُوهُنَّ سِرًّا إِلَّآ أَن تَقُولُواْ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗاۚ وَلَا تَعۡزِمُواْ عُقۡدَةَ ٱلنِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ ٱلۡكِتَٰبُ أَجَلَهُۥۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ ٢٣٥

Walā junāha 'alaykum fīmā 'arradtum bihī min khitbatin-nisā'i aw aknantum fī anfusikum 'alimallāhu annakum satadhkurūnahunna walākil lā tuwā'idūhunna sirran illā an taqūlū qawlam ma'rūfan walā ta'zimū 'uqdatan-nikāhi hattā yablughal-kitābu ajalahū wa'lamū annallāha ya'lamu mā fī anfusikum fahdharūhu wa'lamū annallāha ghafūrun halīm

Kuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta1 da shi daga nẽman auren mãtãko kuwa kuka ɓõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cẽwa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shia ɓõye, fãce dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.

Bayanan ƙasa

1 Bayãnin hukuncin neman auren mace a cikin iddarta. An hana sai dai da bananci kamar ya ce mata, "Ina zan sãmi kamarki?".