Zama Musulmi

Darasi 1 cikin 3

Ta yaya zan zama Musulmi?

Daga Alƙur'ani

فَٱعۡلَمۡ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لِذَنۢبِكَ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مُتَقَلَّبَكُمۡ وَمَثۡوَىٰكُمۡ ﴿١٩﴾

Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka, (kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku.

Muhammad 47:19Karanta a cikin Alƙur'ani

مُّحَمَّدٞ رَّسُولُ ٱللَّهِۚ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ أَشِدَّآءُ عَلَى ٱلۡكُفَّارِ رُحَمَآءُ بَيۡنَهُمۡۖ تَرَىٰهُمۡ رُكَّعٗا سُجَّدٗا يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗاۖ سِيمَاهُمۡ فِي وُجُوهِهِم مِّنۡ أَثَرِ ٱلسُّجُودِۚ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِۚ وَمَثَلُهُمۡ فِي ٱلۡإِنجِيلِ كَزَرۡعٍ أَخۡرَجَ شَطۡـَٔهُۥ فَـَٔازَرَهُۥ فَٱسۡتَغۡلَظَ فَٱسۡتَوَىٰ عَلَىٰ سُوقِهِۦ يُعۡجِبُ ٱلزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ ٱلۡكُفَّارَۗ وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ مِنۡهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمَۢا ﴿٢٩﴾

Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma waɗannan da ke tãre da shi mãsu tsanani ne a kan kãfirai, mãsu rahama ne a tsakãninsu, kanã ganin su sunã mãsu rukũ'i mãsu sujada, sunã nẽman falala daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alãmarsu tanã a cikin fuskõkinsu, daga kufan sujuda. Wannan shĩ ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu, a cikin Injĩla ita ce kamar tsiron shũka wanda ya fitar da rẽshensa, sa'an nan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa'an nan ya daidaita a kan ƙafãfunsa, yanã bãyar da sha'awa ga mãsu shũkar' dõmin (Allah) Ya fusãtar da kãfirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gãfara da ijãra mai girma.

Al-Fath 48:29Karanta a cikin Alƙur'ani

شَهِدَ ٱللَّهُ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَأُوْلُواْ ٱلۡعِلۡمِ قَآئِمَۢا بِٱلۡقِسۡطِۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ ﴿١٨﴾

Allah Ya shaida cẽwa: Lalle ne bãbu abin bautãwa fãce Shi kuma malãiku da ma'abũta ilmi sun shaida, yana tsaye da ãdalci, bãbu abin bautãwa face Shi, Mabuwãyi, Mai hikima.

Al-Imran 3:18Karanta a cikin Alƙur'ani

Daga Sunna

Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Mu’azu yana bayan shi a kan jaki, Ya ce: Ya Mu’azu Ɗan Jabal!!)). Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa, Ya ce; Ya "Mu’azu" Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa sau uku [ya faɗa], ya ce: Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne da gaske daga zuciayarsa sai wuta ta haramta a gareshi)). Ya ce: Ya Ma’aikin Allah shin ba na ba mutane labarin nan ba domin su yi murna? Ya ce: Za su saki jiki. Sai Mu’azu ya ba da labarin bayan rasuwar Ma’aikin Allah gudun kada ya ɓoye ilimi.

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Ingantacce ne HadeethEnc.com
Bayani

Mu’azu Ɗan Jabal Allah Ya yadda da shi, ya kasance yana bayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan abin hawa na dabbarsa, sai ya kira shi Ya Mu’azu, ya maimaita kiran na sa har sau uku, domin ƙarfafawa da Kuma muhimmancin abin zai faɗa masa.

A duka kiran Mu’azu Allah Ya yarda da shi yana amsa masa da cewa; Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da da farincin hakan bayan farinciki, Wato na amsa maka Ya Ma’aikin Allah bayan amsawa, kuma na nemi farinciki da wannan amsawa.

Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba shi bayanin babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Ma’aikin Allah ne da gaske daga zuciyarsa ba ƙarya ba, idan har ya mutu a wannan hali, to, Allah Ya haramta masa wuta.

Sai Mu’azu Allah Ya yarda da shi ya tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan ya baiwa mutane labari domin su yi farin ciki su yi wa juna bushara ta alheri?

Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji tsoron kada su saki jiki da hakan, su ƙaranta ayyuka.

Mu’azu bai ba da wannan bayanin ba sai dab da rasuwarsa, don tsoron kada ya faɗa cikin masu ɓoye ilimi.

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya. Kunya wani tsagi ce na imani.

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Ingantacce ne HadeethEnc.com
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewar imani rassa ne, kuma halaye ne masu yawa, sun kunshi ayyuka da ƙudurce-ƙudurcen zuciya da maganganu.

Kuma mafi girman ɗabi’un imani da falala shi ne faɗin: "Babu abin bautawa da cancanta sai Allah". Tare da sanin ma’anarta, da kuma aiki da abin da take nunawa na cewa Allah Shi ne abin bauta guda ɗaya, wanda Ya cancanci a bauta masa Shi kaɗai ban da wani ba shi ba.

Kuma mafi ƙarancin ayyukan imani shi ne kawar da duk abin da zai cutar da mutane a kan hanyoyi.

Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin cewa kunya tana cikin ɗabi’u na imani, kuma ɗabi’a ce da take zaburarwa a kan yin abu mai kyau da kuma barin mummuna.

Duk darussa