Fa idha 'azamta fatawakkal 'alallah

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

فَبِمَا رَحۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ لِنتَ لَهُمۡۖ وَلَوۡ كُنتَ فَظًّا غَلِيظَ ٱلۡقَلۡبِ لَٱنفَضُّواْ مِنۡ حَوۡلِكَۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ وَشَاوِرۡهُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِۖ فَإِذَا عَزَمۡتَ فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَوَكِّلِينَ ١٥٩

Fabimā rahmatim minallāhi linta lahum walaw kunta fazzan ghalīzal-qalbi lanfaddū min hawlika fa'fu 'anhum wastaghfir lahum washāwirhum fil-amri fa idhā 'azamta fatawakkal 'alallāhi innallāha yuhibbul-mutawakkilīn

Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara1 da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali.

Bayanan ƙasa

1 Annabi shi ne makomar al'amurra ga dukkan kome, amma Allah Ya lizimta masa sauƙin hali zuwa ga sahabbansa, da yin ma'ãmala da su, ma'ãmala mai kyau, da yi musu addu'a a kõwane hãli, kuma a wurin yãƙi kõ abin da ya shãfi yãƙi, Yã lizimta masa ya yi shãwara da su, kuma Ya bã shi damar yin ijtihãdi a nan, sa'an nan Ya umurce shi daya dõgara ga Allah wajen zartaswa, a kan ra'ayin da ya gani daga gare su.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Karanta Surat Al-Imran gaba ɗaya

Tambayoyi

Ina Fa idha 'azamta fatawakkal 'alallah take a cikin Alƙur'ani?

Fa idha 'azamta fatawakkal 'alallah tana cikin Surat Al-Imran, 3:159.