Surat At-Tawbah, aya ta 36

9:36

إِنَّ عِدَّةَ ٱلشُّهُورِ عِندَ ٱللَّهِ ٱثۡنَا عَشَرَ شَهۡرٗا فِي كِتَٰبِ ٱللَّهِ يَوۡمَ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ مِنۡهَآ أَرۡبَعَةٌ حُرُمٞۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلۡقَيِّمُۚ فَلَا تَظۡلِمُواْ فِيهِنَّ أَنفُسَكُمۡۚ وَقَٰتِلُواْ ٱلۡمُشۡرِكِينَ كَآفَّةٗ كَمَا يُقَٰتِلُونَكُمۡ كَآفَّةٗۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلۡمُتَّقِينَ ٣٦

Inna 'iddatash-shuhūri 'indallāhithnā 'ashara shahran fī kitābillāhi yawma khalaqas-samāwāti wal-arda minhā arba'atun hurumun dhālikad-dīnul-qayyimu falā tazlimū fīhinna anfusakum waqātilul-mushrikīna kāffatan kamā yuqātilūnakum kāffatan wa'lamū annallāha ma'al-muttaqīn

Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin Littãfin1 Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya. Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.

Bayanan ƙasa

1 Kõ dã, a cikin waɗannan watanni akwai mãsu alfarma, kõ da yake sũ kãfirai ba sa kiyaye alfarmarsu ba, sun shigar da wani wãyonsu a ciki wanda suke cewa Nasĩ'u (watau jinkiri); Idan sunã son su yi yãƙi a cikin ɗayan watannin, sai su halattar da shi, sa'an nan su haramta wani watã a matsayinsa, su ƙãra kãfirci a kan kafircinsu, da yin haka. Sabõda haka Allah Ya halattar da yãƙi a cikin kõwanne watã dõmin kada a mãmayi Musulmi. Kuma yin jihãdi Yanã cikin ayyukan ibãda wadda Allah Yake riɓanya lãdarta a cikin watannin, mãsu alfarma.