Surat An-Nisa, aya ta 100

4:100

۞ وَمَن يُهَاجِرۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ يَجِدۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُرَٰغَمٗا كَثِيرٗا وَسَعَةٗۚ وَمَن يَخۡرُجۡ مِنۢ بَيۡتِهِۦ مُهَاجِرًا إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ يُدۡرِكۡهُ ٱلۡمَوۡتُ فَقَدۡ وَقَعَ أَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا ١٠٠

Waman yuhājir fī sabīlillāhi yajid fil-ardi murāghaman kathīran wasa'atan waman yakhruj mim baytihī muhājiran ilallāhi warasūlihī thumma yudrikhul-mawtu faqad waqa'a ajruhū 'alallāhi wakānallāhu ghafūrar rahīmā

Kuma wanda ya yi hijira a cikin hanyar1 Allah, zai sãmu, a cikin ƙasa, wurãren jũyãwa mãsu yawa da yalwa. Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, lãdarsa tã auku ga Allah, Kuma Allah Yã kasance, a gare ku, Mai gãfara, Mai jin ƙai.

Bayanan ƙasa

1 Allah Yana kwaɗaitar da mũminai ga yin hijira zuwa wurin neman yardarsa. Hukuncin hijira yana nan a ko da yaushe hãli ya hukunta da a yi ta.